1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a jaridun Jamus

Lawal, TijaniJanuary 23, 2008

Sharhunan labarai daga jaridun Jasmus akan nahiyar mu ta Afurka.

https://p.dw.com/p/Cwbr
Rikicin siyasa a KenyaHoto: AP

Niger/Kenya/Angola

Har yau dai rikicin ƙasar kenya shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a game da al'amuran Afurka, ko da yake ba watsi suke yi da sauran sassa na nahiyar ba.

Niger

Misali dai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta leka kasar Nijer domin nazarin halin da ake ciki dangane da wasu 'yan jaridar ƙasar Faransa su biyu da mahukunta suka tsaresu suke kuma fuskantar barazanar hukuncin kisa kamar yadda jaridar ta nunar ta kuma kara da cewar:


"Ana zargin 'yan jaridar guda biyu ne da laifin barazana ga al'amuran tsaron kan kasar Nijer. Amma fa duka-duka laifinsu shi ne kokarin gabatar da rahoto akan 'yan tawayen Tuareg a arewacin ƙasar ta Nijer. Tuni kuwa gamayyar 'yan jarida ta kasa-da-kasa da yi Allah waddai akan abin da ta kira matakin wata gwamnati mai bin manufofi na danniya da take hakkin 'yan jarida a kokarinta na hana tsage gaskiya ko ta halin kaka."

Kenya


Daga ƙasar Nijer zamu koma ƙasar Kenya a gabacin Afurka, wadda har yau rikicin ta ya ki ci ya ki cinyewa. A cikin sharhin da ta gabatar jaridar Die Tageszeitung nuni tayi da cewar:

"A hakikanin gaskiya ba kawai 'yan kabilar Kikuyu ne ake kai wa hari ba, hatta 'yan kabilar Kalenyin, wadanda suka bai wa Kibaki goyan baya an lallasa su aka fatattakesu daga gidajensu. Masu kai harin na da cikakkun bayanai a game da wadanda suka zabi Kibaki da kuma wanda ya jefa wa abokin adawarsa Odiga kuri'a. Kazalika su ma magoya bayan 'yan hamayyar sun yi asarar rayukansu a matakai na rama wa kura aniyarta. Akwai ma rahotannin dake cewar hatta su kansu mahukuntan kasar Kenya, kawunansu ya rarrabu daidai da sauran al'umar kasar."


A dai wannan makon mai karewa ne aka gabatar da zaman farko na majalisar dokokin ƙasar ta Kenya. Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi akan haka tana mai cewar:


"An gudanar da zaman farko na majalisar dokokin Kenya a cikin yamutsi, inda wakilan ke zargin junansu da maguɗin zaɓe, ko da yake a karshe an nada sabon kakakin majalisar daga bangaren 'yan hamayya."

Angola

Duk da zaman lafiya da tsarin mulki na demokradiyya a ƙasar Angola, amma har yau al'umar ƙasar na ci gaba da fama da tabon yakin basasar da aka yi tsawon shekaru da dama ana fuskanta a kasar. Wannan maganar kuwa musamman ta shafi nakiyoyi ne na karkashin ƙasa da aka bibinne a sassa dabam-dabam na Angola, in ji jaridar Rheinische Post, wadda ta kara da cewar:

"Kimanin kashi 90% na wadanda bala'in fashewar nakiyoyi na karkashin kasa a Angola farar hula ne da suka hada da manoma a gonakinsu da yara a filayen wasa ko kuma mata dake kan hanyarsu zuwa cefane a kasuwa."

Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi tsakanin kasashen ACP da na Kungiyar Tarayyar Turai akan wata yarjejeniyar ciniki ta wucin gadi, a yanzun da yawa daga kasashen sun ba da kai bori ya hau, inda suka saduda ga bukatun kasashen Turai. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"A yanzun ba abin da yayi shaura illa a sa ido a ga ko shin sauran kasashe masu adawa, su ma a nasu bangaren zasu mika wuya. Kungiyoyi masu zaman kansu dai suna ci gaba da kakkausan suka akan Kungiyar Tarayyar Turai a game da matsin lambar da take wa kasashe masu tasowa na ACP domin su bude kofofin kasuwanninsu ta yadda kasashen na Turai zasu samu damar shigar da kayayyakinsu a wadannan kasuwanni ba tare da kwasta ba."