1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

September 19, 2003
https://p.dw.com/p/BvqX

Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon shi ne halin da ake ciki a kasar Guinea-Bissau ta yammacin Afurka, wacce ta fuskanci juyin mulkin soja a farkon wannan makon ba tare da zub da jini ba. Jaridar Die Tageszeitung ta saka ayar tambaya a game da ko shin kasar ta Guinea Bissau zata zama wani sabon dandalin rikici ne a Afurka ta Yamma. Amma fa sojojin, a bisa ikirarin da suka yi, manufarsu game da wannan juyin mulki shi ne kawo karshen ainifin rikicin da ake fama da shi, amma ba kirkiro wani sabo ba. Domin kuwa hambararren shugaban, wanda aka nada shi sakamakon zabe na demokradiyya an dauke shi tamkar hatsabibin mutum ne dake neman tayar da zaune tsaye.
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:
"Bisa ga dukkan alamu al'umar kasar Guinea-Bissau su miliyan daya da dubu metan sun dade suna alla-alla su ga karshen mulkin shugaba Kumba Yala. Domin kuwa sa'o'i 24 kacal, bayan juyin mulkin da ya wanzu a cikin ruwan sanyi, hada-hadar rayuwa ta koma kamar yadda aka saba gani yau da kullum, tamkar ba abin da ya faru a kasar ta yammacin Afurka. Hambararren shugaban, wanda ya lashe zaben da ya kawo karshen tashe-tashen hankulan da kasar ta sha fama da shi a misalin shekaru ukun da suka wuce, ya zama babban misali a game da ire-iren shuagabannin nan na Afurka dake ikirarin goyan-bayan mulkin demokradiyya, amma daga bisani bayan sun samu nasarar zabe sai su koma mulkin kama karya. Wani abin lura ma a nan shi ne, ko da shi ke kasar Portugal da ta taba yi wa Guinea-Bissau mulkin mallaka da MDD da kuma Kungiyar Tarayyar Afurka sun yi Allah Waddai da juyin mulkin, amma babu daya daga cikinsu dake neman ganin an sake mayar da Kumba Yala kan karagar mulki. Duka-duka kira da suka yi shi ne na sake dora kasar kan tsarinta na demokradiyya."
Daga Guinea-Bissau zamu koma Liberia, inda ake fatan ba wa rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da za a tura zuwa kasar ta yammacin Afurka cikakken ikon zartaswa a fafutukar kyautata makomarta. A karkashin wata shawarar da fadar mulkin Amurka ta gabatarwa da kwamitin sulhu na MDD a farkon wannan makon, kamata yayi rundunar ta kiyaye zaman lafiya ta kunshi dakaru dubu 15 wadanda za a ba su cikakken ikon zartaswa, kamar yadda jaridar Frankfurter Rundschau ta rawaito, inda ta ci gaba da cewar:
"Sojojin kiyaye zaman lafiyar na MDD, wadanda ake da niyyar tura su zuwa Liberiya domin su maye gurbin dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen yammacin Afurka a cikin watan oktoba mai zuwa, a baya ga aikin kiyaye zaman lafiya, kazalika za a dora musu alhakin sa ido a fafutukar kyautata makomar wannan kasa da sake dora ta akan wani sahihin tsari na demokradiyya. A karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin shugaba Charles Taylor da aka kakkabe daga karagar mulki da 'yan tawaye za'a kafa wata gwamnati ta hadin gambiza, wacce zata shirya sabon zabe a kasar a shekara ta 2005."
A wannan makon kungiyar alkalai ta Jamus ta ba wa madam Mariama Cisse lamabar yabo ta fafutukar kare hakkin dan-Adam. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:
"Bayan kammala karatunta na alkalanci a birnin Paris, madam Mariama Cisse bata yi wata-wata ba wajen tsoma hannu a fafutukar kirkiro wata kungiya ta alkalai a kasar Nijer a shekara ta 1989. Manufar wannan kungiya kuwa ita ce wayar da kan jama'a game da al'amuran doka ta la'akari da guguwar demokradiyya da ta fara kadawa a wancan lokaci. Kungiyar ta taka rawar gani, inda kasar Nijer ta shiga inuwar kudurin MDD akan girmama hakkin dan-Adam a shekara ta 1999."