1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

October 10, 2003
https://p.dw.com/p/BvqU

A wannan makon jaridun na Jamus sun bayar da la'akari da halin da ake ciki a Liberiya da Kongo da Zimbabwe da kuma fafutukar da kamfanonin Jamus ke yi na samun kasuwar tashoshin samar da makamashi daga zafin hasken rana a kasashen Afurka. Amma da farko zamu fara duba wa'adin da dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD suka kayyade wa sassan da basa ga maciji da juna a kasar Liberiya domin su tsagaita bude wuta a yayinda ita kuma kungiyar lauyoyin Afurka ta ke nema da a taso keyar Charles Taylor domin fuskantar shari'a. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:
"A kokarinsu na tabbatar da zaman lafiyar Liberiya askarawan kiyaye zaman lafiya na MDD sun gabatar da kira ga sassan da rikicin kasar ya shafa da su janye makamansu kwata-kwata daga Monrovia, fadar mulkin kasar, kuma tun abin da ya kama daga jiya alhamis askarawan kiyaye zaman lafiyar suka fara binciken motocin dake shige-da-fice a birnin. A dai ranar sha hudu ga wannan wata ne aka shirya tsofon jami'in gwamnatin Charles Taylor Moses Blah zai danka ragamar mulki ga hannun shugaban rikon kwaryar da aka nada Gyude Bryant. Dangane da hambararren shugaba Charles Taylor kuwa kungiyar lauyoyin Afurka dake da mazauninta a birnin Lagos ta lashi takobin yin bakin kokarinta wajen ganin lalle sai an mika shi ga hannun kotun MDD dake shari'ar miyagun laifuka na yaki a can Saliyo saboda ya amsa laifukan ta'asar yakin da ake zarginsa da aikatawa."
A can kasar Zimbabwe ana fama da koma bayan yawan jama'a sakamakon guje-gujen hijira na al'umar kasar, musamman kwararrun masana da ma'aikata daga cikinsu, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito, inda ta kara da cewar:
"A yayinda a zamanin bayan aka kiyasce yawan al'umar Zimbabwe zai kama mutane miliyan 14, amma sakamakon kididdigar da aka gudanar a kasar shekarar da ta wuce ya kayyade yawansu akan mutane miliyan goma da dubu dari shida. A baya ga cutar nan ta Aids da tayi sanadiyyar rayukan wasu dubban daruruwan al'umar kasar, wasu miliyoyin kuma sun tsere domin zaman hijira a ketare. Bayanai da aka samu a humumance sun ce kimanin kwararrun masana da ma'aikata na kasar dubu dari hudu da saba'in da tara da dari uku da arba'in da takwas suka juya wa kasar tasu baya. Dubu dari da saba'in da shida a Birtaniya, wasu dubu talatin da uku a Amurka, sai wasu dubu goma sha shida a Kanada, sannan ita kuma makobciyar kasa ta Botswana tana karbar bakuncin wasu dubu dari da sittin da biyar kana dubu ashirin da biyu kuma a Afurka ta Kudu. A halin yanzu haka akasarin likitocin dake aiki a gidajen asibitin Zimbabwe sun fito ne daga kasashen Cuba da janhuriyar Demokradiyyar Kongo, sannan nes-nes kuma daga Tanzaniya. Kuma ko da shi ke hijirar tana da nasaba da matsaloli na tattalin arziki dake addabar kasar ta Zimbabwe, amma fa muhimmin abu shi ne a shawo kan matsalar siyasar kasar, wadda ita ce tushen dukkan matsalolin da take fama da su yanzu haka."
A janhuriyar Demokradiyyar Kongo askarawan kiyaye zaman lafiya na MDD sun gano gawawwakin mutane kimanin 50, kamar yadda jaridar Frankfurter Rundschau ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:
"Murna ta koma ciki dangane da ikirarin da aka rika yi na cewar dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Turai sun samu nasarar ayyukansu da suka gudanar a kasar Kongo bayan da a ranar litinin da ta wuce sojojin MDD suka gano gawawwakin mutane 55, akasarinsu yara kanana, da aka yi musu kisan kiyashi a kauyen Kachele mai tazarar kilomita 60 daga arewa-maso-gabacin Bunia. Kawo yanzun dai ba a san masu laifin wannan ta'asa ba, amma majiyoyi masu nasaba da MDD sun tabbatar da cewar za a dauki dukkan matakin da ya dace wajen cafke masu wannan laifi da kuma hana wanzuwar wani sabo makamancinsa.
A