1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

October 17, 2003
https://p.dw.com/p/BvqT

A wannan makon dai akasarin jaridun na Jamus sun mayar da hankalinsu ne akan kasar liberiya, wacce ta samu sabon shugaba na rikon kwarya, wanda aka saka dogon buri a kansa na cewar zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar ya kuma dora ta kan wani sahifin tsari na mulkin demokradiyya tsantsa a cikin shekaru biyu na mulkinsa. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar Die Welt cewa tayi:
"A wannan makon al'umar Liberiya sun samu wata 'yar sa'ida sakamakon danka al'amuran mulkin kasarsu ga hannun Gyude Bryant da aka yi. Hamshakin dan kasuwar, mai shekaru 54 da haifuwa, wanda zai jagoranci kasar domin share hanyar zabe a shekara ta 2005, wanda kuma akasarin al'umar Liberiya ba da wata masaniya game da shi, an zabe shi akan wannan mukami ne a matsayinsa na dan ba ruwana, lokacin taron sulhu watan agustan da ya wuce. Kuma dukkan 'yan tawaye da wakilan gwamnatin hambararren shugaba Charles Taylor suka amince da shi. To sai dai kuma abin tsoro shi ne ka da a sake fuskantar wasu sabbin hare-hare kafin a kammala tsugunar da sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD su dubu 15 a wannan kasa a cikin watan janairu mai zuwa. Musamman ganin yadda Charles Taylor ke bakin kokarinsa na yin tasiri a siyasar kasar sannan su kuma 'yan tawaye dake da mayaka dubu 45 suke ci gaba da mamayar kashi uku bisa hudu na fadin Liberiya."

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta ba da rahoto ne akan wata makarantar soja dake samun goyan baya daga Jamus, wadda kuma nan gaba zata zama wata cibiyar bayar da horo ga sojojin MDD da za a tsugunar da su domin aikin kiyaye zaman lafiya a wata kasa ta Afurka. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:
"A misalin shekaru biyu da suka wuce ne gwamnatin Jamus ta tsayar da shawarar rufa wa kasar Ghana baya wajen gina cibiyar ba da horo ta Kofi-Annan, domin ba da karin ilimi ga sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD. Bisa ga ra'ayin gwamnatin Jamus irin wannan cibiya tana da muhimmanci, musamman wajen ba da horo ga sojojin Afurka a kokarinsu na kiyaye zaman lafiya ko magance rikice-rikice na yanki kamar dai yadda aka gani a kasashen Liberiya da Saliyo."

A wannan makon gwamnatin Sudan ta saki shugaban jam'iyyar National Congress ta Musulmi Sheikh Hassan Atturabi ta kuma dage dokar harmata ayyukan jam'iyyar. Jaridar Frankfurter Rundschau ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:
"Ba zato ba tsammani a farkon wannan makon gwamnatin kasar Sudan tayi wa Hassan Atturabi da wasu mukarrabansa su bakwai dake tsare afuwa tare da soke dokar haramcin da aka kakaba wa jam'iyyarsa ta National Congress. Ga alamu dai wannan afuwa ta samu ne sakamakon matsin lamba daga ketare. To sai dai kuma manazarta sun bayyana cewar shugaba Al-Bashir na neman shigar da jam'iyyar ta masu zazzafan ra'ayi na addini a tattaunawar sulhu da ake yi ne domin ya samu wani kakkarfan matsayi bisa manufa. Domin kuwa tattaunawar ta yanzu ta shafi rabon mukamai ne da dora hannu akan albarkatun da Allah Ya fuwace wa Sudan da kuma matsayin kowane daga cikin addinai uku a wannan kasa."

Gwamnatin kasar Kenya ta fara samun nasara a matakanta na yaki da rashawa a cewar jaridar Frankfurter Rundschau a cikin wani rahoton da ta bayar, inda ta kara da cewar:
"Matsalar cin hanci da son kai ita ce ke addabar tattalin arzikin kasar Kenya, wacce kuma gwamnatin shugaba Mwai Kibaki ta lashin takobin yakarta ko ta halin kaka. Kuma a wannan makon ta samu ci gaba inda a cikin wani rahoton da ta bayar ta gabatar da sunayen wasu alkalai na kasar da aka same su da laifukan karbar hanci domin gabatar da shaidar zul. A sakamakon wannan tabargaza gwamnatin zata aiwatar da garambawul ga tsare-tsaren kotun kasar ta Kenya."