1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

October 24, 2003
https://p.dw.com/p/BvqS

Rahotannin jaridun na Jamus zao fara ne da ya da zango a kasar Sudan, inda ake samun kyakkyawan ci gaba a fafutukar neman zaman lafiyar kasar da kawo karshen yakin da ya ki ci ya ki cinyewa tun misalin shekaru ashirin da suka wuce. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi: "Wani abin lura a game da wannan sabon ci gaba da aka samu shi ne yadda takanas ta Kano sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya zarce zuwa Nairobin Kenya domin halartar taron sulhun da ake gudanarwa a karamin garin Naivasha mai tazarar kilomita 100 daga arewacin Nairobi a tsakanin mataimakin shugaban kasar Sudan Ali Osman Taha da madugun 'yan tawayen kudancin Sudan John Garang. Colin Powell dai ya bayyana kwarin guiwarsa a game da cewar kwalliya zata mayar da kudin sabulu saboda dukkan sassan biyu sun tabbatar masa da cewar zasu cimma daidaituwa akan wata yarjejeniya ta zaman lafiya nan da karshen shekara. Tuni kuwa gwamnatin Amurka tayi wa gwamnatin shugaba El-Bashir alkawarin taimakon abin da ya kai dala miliyan 500 da zaran an cimma irin wannan daidaituwa tsakanin sassan biyu."
Amma fa bisa ga ra'ayin jaridar ta Süddeutsche Zeitung wannan fafutuka da Amurka ke yi, ba tsakani da Allah ba ne. Jaridar sai ta kara da cewar:
"Ainifin musabbabin wannan ci gaba shi ne arzikin man fetur da aka gano a kasar ta Sudan, wanda kuma kawo yanzu kamfanonin kasashen Malasiya da China ne ke cin gajiyarsa, ita kuma Amurka ba ta kaunar ganin ta zama 'yar rakiya, hakan kuwa ba zata yiwu ba matsawar da kasar ta ci gaba da kakaba wa Sudan takunkumin karya tattalin arziki. Bugu da kari kuma shi kansa shugaban Bush zai amfana daga wata yarjejeniya ta sulhu a matsayin mai sasantawa tsakanin Musulmi da Kiristoci."
A can kasar Zimbabwe al'amura sun tsaya cik kuma rikicin kasar ya dauki wani sabon fasali kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma kara da cewar:
"A halin yanzu haka kasar Zimbabwe baki dayanta tana fama da rashin man fetir kuma in har an ci gaba akan wannan mawuyacin hali to kuwa tattalin arzikin kasar dake fama da tafiyar hawaniya zai tabarbare kwata-kwata ya kuma taimaka a yi awon gaba da gwamnatin shugaba Robert Mugabe. Dalilin haka shi ne karancin kudaden musaya na ketare da gwamnati ke fama da shi sakamakon matakin da ta dauka na mamayar akasarin gonakin dake samarwa da kasar kudaden shiga. An dai dade gwamnati na ikirarin cewar ana fama da karancin man fetir ne saboda fifikon da ake ba wa manoma, amma a hakikanin gaskiya duka-duka abin da aka bawa manoman bai zarce lita dubu 280 daga cikin lita miliyan 150 na man diezel da aka tanada ba. Wannan na mai yin nuni ne da wata sabuwar masifa dake tafe, wacce kuma zata kara jefa al'umar kasar cikin mawuyacin hali na yunwa."