Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.11.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A wannan makon mai karewa jaridu 'yan kalilan ne a nan kasar suka gabatar da rahotanni akan al'amuran nahiyar Afurka. Daga cikinsu kuwa har da jaridar Die Tageszeitung , wacce da farko ta ba da rahoto a game da ziyarar da shuagabannin kasashen Kongo da Uganda suka kai kasar Amurka a wannan makon. Jaridar ta ce:
"Ko da shi ke ziyarar tasu bata da dangantaka da juna, amma an shirya saduwa tsakanin shuagabannin biyu, saboda samun kusantar juna a tsakaninsu abu ne dake da muhimmanci ga manufofin Amurka dangane da kasashen Afurka. Kasar ta Amurka tana ba da kakkarfan taimako ga kasashen biyu kuma ta shimfida wa Uganda sharadin janye sojojinta daga harabar Kongo kafin ta bata wani sabon taimako na soji. Ita dai Amurka tana bukatar ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu a kasashen Afurka, saboda a ganinta kasashen nahiyar dake fama da rikici ka iya zama wata muhimmiyar mafaka ga 'yan ta'adda da sauran kungiyoyi na 'yan ta kife dake aikata miyagun laifuka tsakanin kasa da kasa." A halin yanzu an gurfanar da wasu mutane 121 a gaban kotu a kasar Namibiya bisa tuhumarsu da kasancewa 'ya'yan wata kungiya ta 'yan aware da ta shirya wani yunkuri na juyin mulki a kasar misalin shekaru hudun da suka wuce. A lokacin da take gabatar da rahoto jaridar Neues Deutschland cewa tayi:
"Babu wanda ya san tahakikanin dalilin wannan jinkiri da aka yi wajen gabatar da shari'ar domin kuwa ita kungiyar 'yan awaren mai suna Caprivi tun da dadewa aka murkushe ta shi kuma madugun 'yan tawayen ya nemi mafakar siyasa a kasar Denemark. Kaszalika gwamnatin Namibiya tayi afuwa ga wasu 'yan siyasa na lardin Caprivi su 15 da ake zarginsu da hannu a yunkurin da bai ci nasara ba. Wadannan fursinoni 121 da ake shari'rsu a yanzun 'yan rakiya ne kawai. Ga alamu dai sassaucin da gwamnatin Namibiya ke yi ga ainifin gaggan masu alhakin yunkurin yana da nasaba da adawar da har yau take fuskanta a lardin kuma bata sha'awar ganin lamarin ya dada yin tsamari." A farkon wannan makon an samu ci gaba matuka ainun akan hanyar cimma zaman lafiyar kasar Burundi sakamakon rattaba hannu da wakilan gwamnati da na 'yan tawayen kasar suka yi akan wata takardar yarjejeniyar dake cike gibin yarjejeniyar zaman lafiyarsu ta farko da suka cimma a watan oktoban da ya wuce. Jaridar Die Tageszeitung tayi bitar wannan ci gaba inda take cewar:
"Bayan daidaituwar da aka cimma a game da ba wa 'yan tawaye kashi 40% na mukamin kwamanda a sojan Burundi a watan oktoban da ya wuce, a wannan karon an dace akan ba wa 'yan tawayen mukamin mukaddashin hafsan-hafsoshin sojan kasar dake kuryar tsakiyar Afurka. Kazalika sassan biyu zasu sake gudanar da wani taron koli a tsakiyar wannan wata a kasar Tanzaniya domin cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya ta bai daya. Yakin basasar kasar da ake gwabzawa tsakanin sojan gwamnati dake da rinjaye 'yan Tutsi da dakarun 'yan tawayen Hutu yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu 300 a cikin shekaru goman da suka wuce." A wani matakin taimako da ta dauka Jamus ta bude wani karamin asibiti a wani yanki na karkara a kasar Tanzaniya domin bincike da kuma jiyyar masu kwayoyin cutar nan ta AIDS dake karya garkuwar jikin dan-Adam. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ba da rahoto akan haka tana mai cewar:
"Ko da shi ke likitocin da Jamus ta tura domin aiki a asibitin ba su da ikon gusar da kwayoyin cutar HIV, amma akalla ana mahrabin da ayyukan da suke gudanarwa, inda mutane basa fargabar tinkararsu domin neman cikakkun bayanai akan manufa, musamman ma karerayin da ake yayatawa na cewar kamfanonin harhada magunguna na kasashe masu ci gaban masana'antu na raba robobin nan na kondam, wadanda aka gurbata su da kwayoyin cutar saboda yada ta tsakanin al'umar Afurka."