Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.11.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Da farko zamu fara ne da rahoton jaridar Neues Deutschland a game da sakamakon zaben kasar Mauritaniya da aka gudanar makon da ya wuce, inda ta ce:
"Wani abin mamaki a game da zaben kasar Mauritaniya ranar juma'ar da ta shige shi ne kasancewar tun kafin a rufe rumfunan zabe ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ba da sanarwar cewa shugaba mai ci Maouia Ould Taya shi ne ya lashe zaben tare da kashi 67% na jumullar kuri'un da aka kada kuma a sakamakon haka ba lalle sai an kai wani zagaye na biyu na zaben shugaban kasa ba. Ma'aikatar ta cikin gida tayi fatali da dukkan zargi na magudi da aka yi, amma fa tun da farko gwamnati ta ki amincewa da jami'an sa ido daga kasashen ketare, kuma sau biyu shugaba Ould Taya yana ba da umarnin cafke babban abokin takararsa Muhammed Khouna Ould Haidallah bisa zarginsa da yunkurin kwace madafun mulki da karfin hatsi. A yanzu sai dai kawai a zura ido a ga yadda ma'amallar shugaban zata kasance a game da 'yan hamayyarsa."
A yammacin kasar Sudan ana fama da dubban daruruwan 'yan gudun hijira sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin, wanda kuma duniya bata mayar da hankali kansa ba, a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung , wacce ta kara da cewar:
"Ita dai gwamnati a fadar mulki ta Khartoum tana sako-sako da matsalar inda take batu a game da rikici na 'yan ta-kife. Amma fa a hakikanin gaskiya akwai abubuwa da dama dake shaidar cewar tashe-tashen hankulan a Darfur sun fara daukar wani salo na rikicin siyasa, inda ake zargin gwamnati ta rufa wa dakarun sa kai laraba dake cikin cikakkiyar damarar makamai a fadan da suke fafatawa da manoma a yankin. Kuma ko da shi ke a 'yan watannin da suka wuce ne fadan yayi tsamari amma alkaluma na MDD sun yi nuni da cewar kimanin 'yan gudun hijira dubu 600 ne suka tsere daga wannan yanki."
A ATK wasu farar fata dake da mummunar akidar wariyar jinsi sun shirya wani matakin juyin mulki da kuma daukar matakai na gallazawa domin fatattakar bakar fata daga kasar baki daya. A lokacin da take ba da wannan rahoto mujallar Focus karawa tayi da cewa:
"Kafin a cafke farar fatar 'yan ta'adda a ATK sai da suka gwada matakin nasu da suka yi niyyar gabatarwa karkashin taken Operation Popeye bisa manufar sake maido da kasar karkashin mulkin farar fata da kuma farautar bakake. Wani dan leken asirin da aka shigar da shi tsakaninsu shi ne ya fallasa wannan makarkashiya. Tuni suka fara tara kudi da makamai da harsasai da kuma nada kwamandojinsu domin wanzar da wannan ta'asa. Sai dai kuma wadannan wani gungu ne na tsiraru, amma akasarin farar fatan ATKn ba su da wata nasaba da matakan ta'adda."
A cikin wani sharhi da tayi ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemari Wieczorek-Zeul tayi gargadi a game da watsi da matakan yaki da talauci a kokarin da ake yi na tallafa wa kasashen Afurka wajen kirkiro wata tsayayyar runduna ta kiyaye zaman lafiya a nahiyar. A lokacin da take gabatar da wannan sharhi jaridar Frankfurter Rundschau ta ci gaba ne da cewar:
"Dalilin wannan gargadi shi ne gaskiyar cewa talauci shi ne musabbabin matsalolin da ake fama da su a sassan duniya dabam-dabam yanzu haka. Ba zata yiwu ba kasashen Turai su zauna su harde kafafuwansu suna masu more rayuwa a yayinda jama'a a nahiyar Afurka ke fama da kaka-nika-yi. Tuni duniyar ta zama tamkar rufa daya ta yadda duk wata matsalar da ta billa Ya-Allah ta kewayen dan-Adam ce ko cuta, a cikin kiftawa da Bisimillah sai ta zama ruwan dare ta yadu zuwa sauran sassa."