Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 21.11.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankalin jaridun Jamus a game da nahiyar Afurka a wannan makon har da halin da ake ciki a Zimbabwe, inda al'amura suka tsaya cik da kyar motoci ke zirga-zirga a titunan kasar sakamakon karancin manfetur da take fama da shi. A lokacin da take gabatar da rahotonta game da wannan matsala jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Mutane kan sha fama da wahala kafin su kai guraben ayyukansu a kasar Zimbabwe saboda tun watanni da dama da suka wuce kasar ke fama da karancin mai kuma a sakamakon haka ma'aikata kan yi sammako, inda suke tashi da jijjifi su kama hanyar zuwa guraben ayyukansu a tsakiyar Harare. A kuma halin da ake ciki yanzu haka babu wata alamar dake nuna cewar za a samu sauyin lamarin nan ba da dadewa ba. Domin kuwa ayyukan noman taba da kasar ta saba cinikinta a kasuwannin duniya sun ja da baya daga tan dubu 237 a shekara ta 2000 zuwa tan dubu 80 kacal a wannan shekarar. Kazalika cinikin dabbobi da take yi da kasashen KTT ya samu mummunan koma baya daga bisashe miliyan daya da dubu dari biyu zuwa dubu dari da hamsin kawai. An samu hauhawar farashin kayan masarufi na yau da kullum da misalin kashi 600% sakamakon karancinsu a duk fadin kasar ta Zimbabwe." Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta lura ne da yadda shugaba Mugabe ke neman jefa shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo cikin wani hali na kaka nika yi sakamakon matakai na kame-kame da ya gabatar kuma duniya gaba dayanta ke Allah Waddai da shi. Jaridar sai ta ci gaba da cewar: "Matakin kame-kame da shugaba Mugabe ya gabatar yana neman sake saka kafar wando daya ne da sauran kungiyoyi na kasa da kasa. Shugaban na Zimbabwe bai dadara ba yana mai bayyana niyyarsa ta halartar taron kolin kasashen Komonwelt a Nijeriya watan desamba mai zuwa. Wannan maganar ta jefa shugaba Olusegun Obasanjo cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Domin kuwa in har ya ki amincewa da halarcin Mugabe zuwa zauren taron mai yiwuwa wasu daga cikin kasashen Afurka su ki shiga taron. Kuma Nijeriya faufau ba zata yarda a yi mata tambarin 'yar amshin shatan Birtaniya ba, lamarin da zai jawo mata bakin jini tsakanin kawayenta a nahiyar Afurka."

Galibi an fi mayar da hankali wajen gabatar da taimako ne ga yankunan da ake yayata rikice-rikicensu ta akwatunan telebijin da jaridu a cewar Jaridar Frankfurter Runschau a cikin wani rahoton da ta bayar tana mai cewar: "Rikice-rikice kamar wadanda ake fama da su a kasashen Iraki da Afghanistan, wadanda ake yayata su ta akwatunan telebijin da jaridu a kullu-yaumin sune suka fi daukar hankalin jama'a wajen ba da taimako a maimakon rikice-rikice da aka yi fatali da su kamar a kasashen Burundi ko Kongo ko Liberiya". Jaridar ta ambaci sakatare-janar na MDD Kofi Annan yana mai bayanin cewar Afurka ce ke fama da 17 daga cikin munanan rikice-rikice kimanin 21 da ake fama da su a sassa dabam-dabam na duniya. Galibi kuwa yake-yake ne na basasa da kan haddasa guje-gujen hijira na dubban daruruwan jama'a. An gabatar da shirye-shirye na taimaka wa wadannan makaurata amma abin takaici ba a samu isasshen kudin wanzar da su ba." A wani sabon ci gaba kuma shugaban dakarun 'yan tawaye na Hutun Ruwanda dake da sansaninsu a Kongo ya mika wuya ga mahukuntan Ruwanda. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi: "Ko da shi ke Paul Rwarakabije na da hannu dumu-dumu a ta'asar kisan kiyashin da ta wanzu a Ruwanda a shekarar 1994, amma gwamnati a Kigali tayi marhabin da mika wuya da yayi wanda take gani tamkar wata nasara ce ga matakanta na mayar da manufofin kasar kan turbar demokradiyya. Shi kuma Rwarakabije da mukarrabansa suna iya fatan samun wasu muhimman mukamai a sojan kasar ta Ruwanda. Domin kuwa a maimakon a tsare su sai aka nema daga gare su su taimaka wajen shawo kan sauran takwarorinsu su bi sau."