1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

December 19, 2003
https://p.dw.com/p/BvqI
A wannan makon dai jaridun na Jamuas, daidai da sauran kafofin yada labarai a sassa dabam-dabam na duniya, sun fi mayar da hankalinsu ne akan halin da ake ciki a kasar Iraki sakamakon kame tsofon shugaban kasar da aka yi, wanda kuma ake ta cece kuce a game da irin shari'a ko kuma hukuncin da za a yanke masa. To amma duk da haka wasu daga cikin jaridun ba su yi watsi da al'amuran na nahiyar Afurka ba. Misali jaridar Neues Deutschland, wacce tayi bitar halin da ake ciki a yankin Deltan Nijeriya tana mai dora alhakin tashe-tashen hankulan wannan yanki akan dimbim arzikin man fetur dake dirke a can. Bisa ga ra'ayin jaridar marubucin adabin nan na Nijeriya da aka zartar masa da hukuncin kisa Ken saro-Wiwa shi ne ya fito da ainifin matsalar dake akwai a wannan yanki na gwagwarmayar dora hannu akan albarkatun kasa. Jaridar sai ta kara da cewar:
"Ko da shi ke Nijeriya na tinkafo da arzikinta na mai ne dake dirke a yankin Delta, amma su kansu al'umar wannan yanki suna cikin hali ne na rabbana ka wadatamu. Daruruwan mutane suka rasa rayukansu sannan aka fatattaki wasu dubanni a shekarar da ta gabata a gwagwarmayar neman rabo na kudaden shiga da Nijeriya ke samu daga cinikin manta. Ainifin masu alhakin wadannan kashe-kashe da ta da zaune tsaye kuwa, ba kowa ba ne illa dakarun sa kai na kabilun yanki guda uku, wadanda ba sa ga maciji da juna. wadannan kabilun sun hada da Itsekiri da Urhobo da kuma Ijaw. Su ma jami'an tsaron Nijeriya suna da rabonsu na alhakin wadannan kashe-kashe, wadanda a bara suka taimaka aka rika rufe tashar jiragen ruwan Warri, wadda ta kanta ne Nijeriya ke fitar da kashi 40% na man da take cinikinsa a ketare. Daya matsalar kuma ita ce ta satar mai da ake yi, wanda ya kama kashi 10% na yawan mai da kasar ke samarwa a shekara kuma a bara tayi asarar abin da ya kai dala miliyan dubu daya da dari biyar sakamakon haka."
Shugaban kasar Afurka ta Kudu Thabo Mbeki yana kan bakansa na nuna hadin kai da zumunta ga shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe. A lokacin da take ba da rahoto a game da ziyarar aikin da shugaban Afurka ta Kudun ya kai ga Zimbabwe, jaridar Süddeutsche Zeitung ta ambaci Mbeki yana mai fadin cewar a zamanin baya dukkan al'ummomin Zimbabwe da ATK sun yi hadin kai wajen gwagwarmaya da mulkin danniya da kama karya kuma a saboda haka ya zama wajibi a yanzun su karfafa hadin kansu domin tinkarar sabbin matsalolin da suka taso. Jaridar sai ta kara da cewar:
"Bisa ga ra'ayin Zimbabwe kamata yayi a ci gaba da tuntubar juna da Mugabe a maimakon neman a mayar da shi saniyar ware domin hakan ba zai tsinana kome ba illa ya kara tsawwala mawuyacin halin da ake ciki."
Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar matsalar kasar ta Zimbabwe, ko da shi ke ta fi mayar da hankali ne akan goyan bayan da mataimakin kakakin 'yan Christian Union a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag yake ba wa 'yan hamayya a kasar ta kudancin Afurka. Jaridar ta ambaci jami'in siyasar na Jamus, wanda ya gana da wakiloan 'yan hamayyar ba tare da wata masaniya a game da halin da ake ciki a Zimbabwen ba yana mai fada wa 'yan jarida cewar martabar da tsofon shugaba Nelson Mandela ya samar wa ATK zata zube a idanun duniya, muddin kasar ta ci gaba da ba wa gwamnatin danniya da kama karya ta Robert Mugabe goyan baya.