Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 20.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A wannan makon ma kamar yadda aka saba jaridun na Jamus ba su yi sako-sako da al'amuran nahiyar Afurka ba duk kuwa da mayar da hankali da suka yi ga rikicin da ake fama da shi a tsuburin Haiti. Daga cikin muhimman batutuwan da jaridun na Jamus suka ba da rahotanni kansu a game da nahiyar ta Afurka har da halin da ake ciki a kasar Sudan inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung take cewar: "Duk da rahotannin nasarorin da ake samu daga majiyoyi na gwamnatin Sudan akan dakarun 'yan tawaye a Darfour, amma fa har yau ana ci gaba da dauki ba dadi a wannan yanki kuma tuni aka mayar da fagen yakin zuwa harabar kasar Chadi. An samu rahotanni a game da wasu dakarun sa kai dake farautar mayaka na 'yan tawayen Darfour a wasu kauyuka na kasar Chadi suna masu halaka farar fula da kuma awon gaba da dabbobi sama da dari shida. To sai dai kuma ita kanta gwamnatin kasar ta Chadi ta ki ta ce uffan a game da wannan batu. A kuma halin da ake ciki shugaba Al-Bashir na kasar Sudan ya ba da sanarwa a game da kafa wata hukumar zaman lafiya da zata kunshi har da wakilan 'yan tawayen, wacce kuma zata bi bahasi domin neman cikakken haske a game da bukatun al'umar Darfour." Ita ma jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Sudan tana mai ya da zango a kudancin kasar domin nazarin shirye-shiryen da ake yi na rungumar zaman lafiya a yankin. Jaridar sai ta kara da cewar: "Kungiyar tawaye ta SPLA ta tashi haikan a shirye-shiryenta na rungumar abin da zai biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da gwamnati a birnin Khartoum. Domin kuwa a karkashin zanen yarjejeniyar da aka tanadar, nan da shekaru shida, bayan rattaba hannu kanta, al'umar yankin zasu samu wata kafa ta kada kuri'ar raba gardama a game da makomarsu, kuma ba shakka akasarinsu zasu ba da goyan baya ne ga ikon cin gashin kan yankinsu. Amma kuma hakan zai zama tamkar an gudu ne ba a tsira ba, saboda 'yan arewacin Sudan ba zasu taba amincewa da hakan ba, lamarin dake ma'anar sake komawa fagen fama tsakanin sassan biyu." A halin da ake ciki yanzu haka kasar ATK ta fi kowace kasa a doron duniyar nan tamu fama da radadin cutar nan ta Aids mai karya garkuwar jiki, inda da yawa daga cikin bakar fatar kasar kan yi tsumulmular kudi saboda daukar nauyin jana'izarsu, a cewar jaridar Frankfurter Rundschau , wacce ta tura wakilinta zuwa ATK domin bitar halin da ake ciki. Jaridar sai ta ci gaba da cewar: "A halin yanzu haka ana dada fama da karancin filaye a makabartun ATK, inda a kowace rana ta Allah mutane kusan dari shida ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar nan ta Aids mai karya garkuwar jikin dan-Adam. Alkaluma a hukumance sun nuna cewar kimanin 'yan ATK miliyan biyar ne ke dauke da kwayoyin cutar, wanda ya sanyata akan gaba a tsakanin sauran kasashen dake doron duniyar nan tamu. A yayinda a zamanin baya yawa-yawancin al'umar ATK kan cimma shekaru sittin na haifuwa, a yanzu an wayi gari akasarinsu ba sa zarce shekaru 42 a duniya." A wani sabon ci gaba kuma jaridar Die Tageszeitung ta gano cewar bayan kawo karshen rawar da haulakan yaki ke takawa a gabacin kasar Kongo a yanzun Jamusawa da 'yan kasar Austriya ne ke gwagwarmayar dora hannu akan wasu rijiyoyin ma'adinai a kasar ta kuryar tsakiyar Afurka. Jaridar sai ta ci gaba da cewar: "Wani Bajamushe mai suna Karl-Heinz Albers dake da mazauninsa a Goma da kuma wani dan kasar Austriya da ake kira Michael Krall suna nan suna gwagwarmaya da juna a kokarinsu na dora hannu akan wata rijiya mai dimbim arzikin ma'adinai."