Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.02.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A wannan makon mai karewa jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran Afurka. Misali jaridar nan ta Die Tageszeitung ta leka Nijeriya tana mai bitar kai ruwa-ranar da ake famar yi dangane da lambar riga kafin shan inna, lamarin da take gani tamkar barazana ce ga matakin da kungiyar lafiya ta duniya WHO ta gabatar tun daga litinin da ta wuce na yi wa yara lambar ta riga kafin shan inna a duk fadin duniya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Wasu jihohi hudu na arewacin Nijeriya sun bijire wa matakin na lambar riga kafin shan inna da kungiyar lafiya ta duniya WHO da asusun taimakon yara na MDD Unicef suka gabatar, saboda imanin da suka yi na cewar maganin riga kafin na kunshe da wasu sinadarai masu hana haifuwa. Ita dai kungiyar ta WHO, kamar yadda ta nunar tana fatan gusar da wannan cuta ne kwata-kwata daga doron kasa nan da karshen shekara ta 2004 ta la'akari da nasarar da ta samu wajen kayyade yawan masu kamuwa da cutar daga yara dubu 350 a 1988 zuwa yara 677 a shekarar da ta gabata. Kuma kasashen da har yau suke fama da barazanar cutar ta shan inna sun hada da Nijeriya da Indiya da Pakistan da Masar da Nijer da kuma Afghanistan. Amma fa ita kanta gwamnatin Nijeriya tana da rabonta na alhakin wadannan gardandami da ake famar yi. Domin kuwa a maimakon ta ba da umarnin aiwatar da lambar ta riga kafi, sai ta amince da a gudanar da bincike akan wadannan magunguna a kimiyyance. Kuma ko da yake an gudanar da binciken a can ATK, amma gwamnati ta ki ta fito da sakamakon binciken a fili. A nasu bangaren masana kimiyya a Kanon Dabo sun ba da kwangilar binciken magunguna a kasar indiya inda aka gano cewar a hakika suna kunshe da wasu sinadarai masu hana haifuwa dake kuma haddasa cutar sankarau, wato kansa."

A halin da ake ciki yanzu haka ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemari Wieczorek-Zeul na ziyarar janhuriyar Benin mai makobtaka da Nijeriya. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi amfani da wannan dama domin janyo hankali zuwa ga rikicin da ake fama da shi tsakanin kasashen yammacin Afurka da KTT dangane da noman auduga. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Kasashen Benin da Mali da Nijer da Burkina Faso, masu fafutukar neman ganin an kamanta adalci a cinikin auduga, sun zama kyakkyawan misali ga adawar da kasashen yammacin Afurka suke yi da babakeren kasashe masu ci gaban masana'antu a harkokin ciniki na duniya. Wadannan kasashe guda hudu, a lokacin taron ciniki na duniya a Cancun ta kasar Mexiko, ba tare da wata rufa-rufa ba, suka fito fili suna masu sukan lamirin kasashen Turai da Amurka dangane da manufofinsu na karya farashin auduga da manomansu ke samarwa. Tun da farkon fari kasashen guda hudu na yammacin Afurka suka samu goyan baya daga Heidemari Wieczorek-Zeul, lamarin da ya bata wa sauran kasashen KTT rai matuka ainun. Amma a yanzu, ta la'akari da canjin salon tunanin da ake samu tsakanin kasashen KTT, ana iya ya ba wa ministar taimakon raya kasashe masu tasowan ta Jamus a game da rawar da ta taka a rikicin cinikin auduga tsakanin kasa da kasa." A ranar 10 ga watan maris mai kamawa ne za a gurfanar da fursinoni goma daga cikin fursinonin da ake zarginsu da miyagun laifuka na yaki a kasar Saliyo. A lokacin da take gabatar da rahoto game da wannan kotu ta musamman, jaridar Die Zeit mai fita mako-mako ta ce wannan kotu ka iya zama abin koyi ga sauran kasashe. Jaridar dai ta ci gaba da cewar: "Abin da ya banbanta kotun ta Saliyo da sauran kafofin dake cin shari'ar ta'asar yakin da ta samu misali a kasashen Ruwanda da Yugoslabiya, shi ne kasancewar an kafata ne a cikin gida kuma kotun koli ta Saliyo tana farautar ainifin masu munanan laifuka ne na keta haddin dan-Adam tun daga shekara ta 1996, daidai da yadda yarjejeniyar Geneva ta tanada. Bugu da kari kuma a karo na farko za a yanke hukunci akan masu laifukan tilasta aikin soja akan yaran da suka gaza shekaru 15 na haifuwa."