Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A wannan makon ma kamar dai a makon jiya jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama a game da al'amuran nahiyar Afurka, inda misali jaridar General-Anzeiger ta nan birnin Bonn tayi amfani da ziyarar da ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul ta kai kasar Benin domin bitar matsalolin da kasar ke fama dfa shi wajen cinikin audugar dake samar mata da kudaden shiga. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Kasar Benin dake makobtaka da nijeriya a yammacin Afurka ta dogara ne kacokam akan auduga don samun kudaden musaya na ketare. Amma fa farashin audugan ya fadi da misalin kashi 40% a cikin shekaru ukun da suka wuce. Babban dalilin haka kuwa shi ne matakan karya farashin auduga da kasashe masu ci gaban masana'antu ke dauka. Misali kasar Amurka ta kashe abin da ya kai dala miliyan dubu uku da dari bakwai domin karya farashin audugar da manyan manomanta su kimanin dubu 25 ke nomawa ta haka suka samu saukin shigar da audugar tasu akan farashi mai rahusa a kasuwannin duniya. Ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul tayi suka da kakkausan harshe akan wannan manufa, wacce take taimakawa wajen kara kassara tattalin arzikin kasashe matalauta dake tasowa."

Wata gobarar da ta rutsa da ofishin magajin garin Nairobin Kenya tayi kaca-kaca da ginin sannan tayi awon gaba da wasu muhimman takardun da suka shafi wata tabargaza ta cin hanci a kasar ta gabacin Afurka. A lokacin da take rawaito wannan labari jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

"Da yawa daga wadanda suka shaidar da lamari da idanuwansu sun hakikance cewar da gangan ne aka cinna wannan wuta a daidai sashen hukumar kula da al'amuran gine-gine, inda aka dirke kudayen da suka jibanci kwangilar gine-ginen a Nairobi. An shigar da wata tawaga ta musamman a tsakanin jami'an hukumar, wacce aka dora mata alhakin gusar da wadannan kundaye, wadanda suka shafi kwangilar da aka rika rarrabawa ga mukarraban tsofon shugaban kasar Kenya Daniel arap Moi, wanda kuma sabuwar gwamnati ta shugaba Mwai Kibaki take ganin abu ne da ya saba da tsarin dokar ba da kwangila a kasar ta gabacin Afurka."

A cikin wata sabuwa kuma wata kungiya mai zaman kanta a arewa-maso-gabacin kasar Kongo ta zargi dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD da laifin kisan gilla akan wasu farar fula su 12. A lokacin da take bitar matsalar jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Wata kungiyar al'adu ta 'yan kabilar Hema a arewa-maso gabacin kasar Kongo ta zargi sojojin kiyaye zaman lafiya da laifin bude wuta da kuma kisan farar fula 12 lokacin wata jana'iza a Buniya, shelkwatar lardin Ituri. Amma bisa ta bakin kakakin rundunar ta MDD Leo Salmeron farar fula biyu ne tsautsayi ya rutsa da su lokacin wata musayar wuta tsakanin sojojin majalisar da wani gungun mutane dake cikin damarar makamai.. A daura da haka a wasu sassa na kasar ta Kongo sojojin kiyaye zaman lafiyar na MDD ba fuskantar matsin kaimi. Misali a Bukavu, a farkon watan fabarairu aka shiga bata kashi tsakanin sassan da basa ga maciji da juna, sannan wasu sojan sa kai dake kewayen yankin sun lashi takobin sake daura damarar makamai."

Rahotanni daga kasar namibiya sun ce gwamnati na shirin kwace filayen noma daga hannun farar fata domin sake raba su tsakanin bakar fata dake da rinjaye a kasar ta Kudu-Maso-Yammacin Afurka. A lokacin da take sharhi game da haka, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Ko da yake gwamnatin Namibiya na kan bakanta game da sayen filayen noma ala-tilas daga hannun manoma farar fata, amma ta ce ta fi kaunar cimma manufar a cikin ruwan sanyi domin kaucewa daga matsaloli irin shigen wadanda aka fuskanta a kasar Zimbabwe mai makobtaka da ita. A dai halin da ake ciki yanzu haka alkaluma sun nuna cewar kimanin kashi 50% na filin noma mai fadin eka miliyan 35 ke hannun manoma farar fata, wadanda duka-duka yawansu bai zarce kashi 6% na illahirin al'umar namibiya ba."