1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin da jaridun Jamus suka bayar dangane da al'amuran nahiyarmu ta Afurka a wannan makon mai karewa har da halin da ake ciki a kasar saliyo sakamakon kotun kasa-da-kasa da aka bude a Freetown a wannan makon domin shari'ar masu ta'asar miyagun laifuka a yakin basasar kasar ta yammacin Afurka. A lokacin da take batu game da haka jaridar Die Tageszeitung ta ci gaba ne da cewar:
"Wani abin lura a nan shi ne kasancewar daga cikin mutane 13 da aka daukaka kara kansu a gaban kotun, tara ne kawai za a iya cin shari'arsu. Kuma wadannan fursinoni tara, a hakika ba su da wani muhimmanci. Shi kansa babban mai laifi, tsofon shugaban kasar Liberiya Charles Taylor ya samu mafaka a Nijeriya. An saka masa da wannan kariyar ce saboda amincewar da yayi da ya kakkabe hannunwansa daga mulkin kasar Liberiyar a cikin watan agustan da ya wuce."
Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau a lokacin da take ba da nata rahoton cewa tayi:
"Taylor, wanda ake zarginsa da laifin rura wutar rikicin Saliyo, shi ne kawai ya rage a tsakanin gaggan masu laifukan ta'asar da aka caba a yakin basasar wannan kasa, bayan mutuwar madugun kungiyar tawaye ta RUF Sankoh Foday da kuma Sam Bokarie. Tun kafin a bude kotun ta kasa da kasa aka nema daga Nijeriya da ta taso keyarsa domin ya fuskanci shari'a. Daga cikin masu neman ganin an gurfanar da Taylor gaban kotun har da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam na Amnesty da Human Rights Watch, wadanda suka ce wajibi ne kungiyoyi na kasa da kasa su dada yin matsin lamba kan gwamnatin Nijertiya domin ta danka tsofon shugaban na Liberiya ga kotun. Suka ce lokaci yayi da kasashen Afurka zasu ankara da gaskiyar cewa babu wani da ya fi karfin doka."
Ko da yake an kawar da mulkin wariyar jinsi a kasar Afurka ta Kudu, amma fa har yau farar fata ne ke mallakar filayen noma kuma a sakamakon haka a yanzu bakar fatar suka tashi tsaye wajen ganin an maida musu da filayensu da aka kwace. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Die Zeit ta saka ayar tambaya ne da cewar ko shin kaddarar da ta rutsa da Zimbabwe ita ce ke neman rutsawa da ATK a halin yanzu? Jaridar sai ta ci gaba da cewar:
"An samu wata kunyar dake dada bunkasa yanzu haka a ATK, kuma shuagabanninta basa wata rufa-rufa wajen yaba wa shugaba Mugabe na kasar zimbabwe suna masu yin kiran shiga wani sabon babi na gwagwarmayar neman 'yancin kai karo na biyu. Dalili kuwa shi ne kasancewar yau shekaru 10 bayan kifar da gwamnatin wariya, amma har yau tsiraru farar fata ne ke mallakar kashi 80% na kasar noma mai albarka a ATK. Tsofuwar gwamnatin wariya ta farar fata tafattaki bakar fata kimanin miliyan ili da dubu dari biyar daga yankunansu na asali tana mai kakkafa musu sabbin matsugunai ala-tilas. Kungiyar ta fito fili ta yi nuni da cewar sake kwaco wadannan filaye shi ne musabbabin gabatar da matakin neman 'yancin kai. Kuma tuni ta ta fada wa 'ya'yanta da su kaurace wa zaben kasar da za a gudanar watan afrilu mai zuwa, muddin gwamnatin ANC ba ta ba da la'akari da bukatunsu ba."
A wannan makon kasashen dake gabar kogin Nilu suka gabatar da taronsu a Uganda domin saka ayar tambaya a game da fifikon da 'yan mulikin mallaka suka ba wa kasashen Masar da Sudan wajen aiwatar da ruzwan kogin. A lokacin da take bayani game da haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:
"A shekarar 1929 kasashen Birtaniya da Masar suka cimma wata yarjejeniya akan aiwatar da ruwan kogin Nilu, kuma a matsayinta na 'yan mulkin mallaka Birtaniya ta shigar da kasashen Uganda da Kenya da Tanzaniya da kuma Sudan a wannan yarjejeniya, wacce a karkashinta aka haramta wa kasashen gudanar da wani aiki da zai tauye kwararar kogin zuwa Masar. An sabunta yarjejeniyar tare da kara karfafa matsayin kasashen Masar da Sudan a 1959. Bisa ga ra'ayin kasar Masar bai kamata a taba wannan alfarma da aka tanadar mata a yarjejeniyar ba, wacce tun a 1962 tsofon shugaban Tanzaniya Julius Nyerere ya ce haramtacciya ce. Akwai kasashe da dama suka goyi bayan wannan ra'ayi suke kuma bukatar samun damar cin gajiyar albarkar ruwan kogin na Nilu."