1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridun Jamus

April 9, 2004

Halin da ake ciki a kasar Ruwanda, shekaru goma bayan kisan kiyashin da ya wakana a kasar ta kuryar nahiyar Afurka, shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/Bvq3
Ta'asar Kisan Kiyashin kasar ruwanda a 1994
Ta'asar Kisan Kiyashin kasar ruwanda a 1994Hoto: AP

Afurka a Jaridun Jamus

A dai wannan makon mai karewa juyayin zagayowar shekaru goma da wanzuwar ta’asar kisan kiyashin da aka fuskanta a kasar Ruwanda ita ce tafi daukar hankalin jaridun Jamus baki dayansu, ko da yake wasu daga cikin jaridun sun yi bitar halin da ake ciki a wasu sassan na nahiyar Afurka. A cikin wani rahoton da ta bayar dangane da rawar da kasar Faransa ta taka a kisan kiyashin na kasar Ruwanda jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Kasar Faransa ta taka muhimmiyar rawa wajen shirya makarkashiyar kisan kiyashin da ya wanzu a kasar Ruwanda fiye da yadda ake zato. Domin kuwa, kamar yadda rahotanni daga wadanda suka gane wa idanuwansu abin da ya wakana suka nunar, a kan idon sojojin Faransa ake tace ‘yan kabilar Tutsi a kuma mika su ga dakarun sa kai na Hutu domin su yi musu yankar rago. A hakika ma dai ita Faransar ce ummal’aba’isin zayyana wannan makarkashiya, lokacin da babban mashawarcin kasar a al’amuran soja da aka tura zuwa Ruwanda laftana-kanar Gilbert Canovas ya ba da shawarar kafa dakarun sa kai da za a yi musu riga irin ta manoma a yankunan karkara. A tsakanin 1991 da 1992 wannan shiri ya kammalu tare da barbazuwar ‘yan sa kan a yankunan karkara na fadin kasar Ruwanda. Manufar kasar ta Faransa dai shi ne hana Ruwanda mai amfani da harshen Faransanci fadawa hannun ‘yan tawayen Tutsi dake tuttudowa daga kasar Uganda dake amfani da Turanci. A takaice wannan matakin na da nasaba da yada angizon mulkin mallaka."

Ita ma jaridar Der Tagesspiegel ta gabatar da irin wannan sharhin tare da tabo maganar rawar da kasashen Faransa da Belgium suka taka da kuma ikirarin cewar akwai cikakkun bayanan dake nuna yadda sojojin Faransa suka shiga ana fafatawa dasu kafada-da-kafada da sojojin kasar Ruwanda domin murkushe mayaka ‘yan Tutsi da kuma kisan kiyashin da ya biyo baya. Jaridar ta ambaci sakatare-janar na MDD Kofi Annan yana mai bayanin cewar:

"Muddin ana fatan kauce wa irin wannan ta’asa nan gaba to kuwa wajibi ne a dauki nagartattun matakai na yaki da kiyayya da gaba da wariyar jinsi da kabilanci da kuma danyyen mulki na kama karya. A dai wancan lokaci sojojin MDD da aka tsugunar a sun gaza wajen kare makomar yara da mata da tsofaffi da sauran mutane kimanin dubu 800 da aka kashe a kasar Ruwandan a shekarar 1994."

Daga can kuryar tsakiyar nahiyar Afurka zamu juya zuwa kudancin nahiyar tare da ya da zango a Afurka ta Kudu, wacce jaridar Rheinischer Merkur ta ce manyan matsalolin da take fuskanta, yau shekaru goma bayan murkushe mulkin wariya, sun hada da rashin aikin yi ga jama’a da kuma yaduwar cutar Aids. Kuma wannan ka iya zama kalubala ga gwamnatin ANC a zaben kasar da za a gudanar mako mai zuwa. Jaridar sai ta kara da cewar:

"A hakika, ko da yake kasar ATK ta cimma gagarumar nasara wajen murkushe mulkin danniya na farar fata da kuma shimfida kyakkyawar turba ta demokradiyya hade da kamanta adalci ga kowa da kowa a gaban shari’a. Kuma kasar na samun bunkasar tattalin arziki iya gwargwado da hauhawar darajar takardun kudinta na Rand tare da karuwar baki masu yawon bude ido. Amma fa har yau da sauran rina a kaba. Domin kuwa tsiraru farar fata ne ke mallakar kashi 80/ na filin noma kuma sune ke rike da muhimman mukamai a masana’antu da kamfanonin kasar. A baya ga haka ana dada samun bunkasar miyagun lafuka, inda aka kiyasce cewar a kan aiwatar da kisan kai a kasar ta ATK a bayan kowadanne mintuna 25. A daura da haka cutar nan ta Aids sai dada yaduwa take yi tsakanin al’umar wannan kasa ta yadda ala-tilas gwamnati ta canza salon tunaninta ta kuma fara daukar nagartattun matakai don tinkarar cutar tun kafin ta zame mata gagara badau."

A karshen makon da ya wuce ne MDD ta gabatar da matakinta na kiyaye zaman lafiya a kasar Cote d’Ivoire, inda take da niyyar tsugunar da sojoji dubu shida. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Da yawa daga al’umar kasar Cote d’Ivoire tuni suka fid da kauna a game da cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarsu nan ba da dadewa ba. Domin kuwa su kansu sojojin Faransa su 4000 da kuma na kasashen yammacin Afurka su 1000 da aka dirke ba abin da suka tabuka domin dakatar da takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar ta yammacin Afurka. Kuma duk wanda ya lura da kisan ba gaira da aka yi wa masu zanga-zangar neman zaman lafiyar kasar makon da ya gabata tilas ne murnarsa ta koma ciki akan manufa."