Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A wannan makon halin da ake ciki a Darfur na kasar Sudan shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

'Yan gudun hijirar Sudan dake kwarara zuwa Chadi

'Yan gudun hijirar Sudan dake kwarara zuwa Chadi

A wannan makon ko da yake jaridun na Jamus sun sake mayar da hankali ga Afurka ta Kudu dangane da bikin rantsar da shugaba Thabo Mbeki da aka yi domin wani sabon wa’adi na mulki tsawon shekaru biyar masu zuwa, amma babban abin da ya fi ci wa masharhantan tuwo a kwarya shi ne halin da ake ciki a kasar Sudan, dangane da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a Darfur. Ita dai jaridar DER TAGESSPIEGEL tana tattare ne da ra’ayin cewar rikicin yankin Darfur na da nasaba da wani mataki na farautar bayi, saboda bakar fatar yankin Musulmi ne dake fuskantar hare-hare da kashe-kashe na gilla daga ‘yan uwansu Musulmi Laqrabawa jajayen fatu dake ganin fifikon kansu akan bakar fata. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Ita dai Sudan kasa ce da ba ta rabuwa da rikici kuma tun misalin shekaru 21 da suka wuce take fama da yakin basasa a kokarin murkushe ‘yan aware na kudancin kasar. To sai dai kuma a yayinda aka fara hangen sararawar al’amura a wannan yanki sai ga wata sabuwa ta konno kai a yammaci inda Musulmi ke yakar Musulmi. Makiyaya Larabawa jajayen fatu dake samun goyan baya daga fadar mulki ta Khartoum ke kai farmaki kan bakar fata ‘yan kabilun Zagawa da Fur da kuma Masalit. Kimanin mutane dubu 10 suka yi asarar rayukansu a tsakanin shekara daya kacal, a yayinda wasu sama da miliyan daya kuma suka yi hijira."

Ita kuwa jaridar DIE ZEIT a lokacin da take gabatar da nata rahoton ta fara ne da korafi a game da yadda kafofin yada labarai kan yi sako-sako da al’amuran Afurka har sai idan an fara fuskantar barazanar yunwa ko yake-yake dake sanadiyyar mutuwar dubban daruruwan mutane, sannan ne su kan mayar da hankalinsu ga wannan nahiya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Da kyar ne kasashen Afurka kan shiga kanun labarai sai fa idan dubban dauruwan al’umar nahiyar sun fara fuskantar barazanar mutuwa, kamar yadda lamarin ya kasance dangane da kasar Ruwanda ko kuma Sudan a yanzun. Wani rahoto na MDD shi ne ya fito da ainfin halin da ake ciki a Darfur, lardin yammacin kasar Sudan. Tun da jimawa tsofon ministan cikin gida na Jamus mai kula da al’amuran Sudan karkashin tutar MDD ya gabatar da gargadi a game da wata masifa ta ta’asar kisan kiyashin da ake barazanar fuskanta a kasar ta Sudan ba tare da an dauki matakai domin kandagarkinsa ba. Abin mamaki da takaici shi ne kasancewar ba wanda ya fito fili ya ja kunnen gwamnatin Sudan dake ba wa Larabawa jajayen fatu goyan baya wajen keta haddin ‘yan uwansu Musulmi bakar fata, walau ita kanta MDD ko kuma hukumarta dake kula da hakkin dan-Adam a birnin Geneva."

Ganin yadda al’amura ke dada yin tsamari a gabacin kasar Kongo wasu wakilan majalisar dokokin Jamus suka gabatar da kiran daukar tsauraran matakai daga bangaren askarawan MDD domin lafar da kurar rikicin. A lokacin da take rawaito rahotonta game da haka jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

"Akwai bayanai dake nuna cewar dakarun sojan Ruwanda sun sake kutsa kai a lardin Kivu na gabacin Kongo. Kuma ko da yake gwamnati a Kigali ta musunta wannan zargi, amma daga baya-bayan nan shi kansa shugaba Paul Kagame ya fito fili ya bayyana cewar yana nan akan bakansa kuma ba ya tsoron askarawan kiyaye zaman lafiya na MDD. Wakilan majalisar dokokin Jamus guda biyar da suka kai ziyarar gani da ido a Bukavu sun bayyana kaduwa da irin abubuwan da suka shaidar kuma a sakamakon haka suke ganin wajibi ne MDD ta tashi tsaye domin dakatar da ta’asar dake wanzuwa a yankin."

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG ta yi bitar wannan zargi da ake wa kasar Ruwanda a game da sake tura sojojinta zuwa Kongo, bayan janyesu da tayi a hukumance, a shekara ta 2002. Jaridar sai ta kara da cewar:

"A hakika dai da wuya a tantance gaskiyar korafin da ake yi na wanzuwar sojan Ruwanda a gabacin Kongo. Domin kuwa da yawa daga dakarun sojan Ruwandar ‘yan usulin Kongo ne, wadanda aka fatattakesu daga kasar a cikin shekarun 1990. Wasu daga cikinsu sun ci gaba da zama a kasar tasu ta asali bayan janyewar Ruwandar a shekara ta 2002. Ita kuwa Ruwanda a nata bangaren ko da yake ta musunta zargin tana mai kalubalantar askarawan kiyaye zaman lafiya na MDD a game da rashin tabuka kome wajen karya alkadarin ‘yan tawayen Hutu su kimanin dubu takwas da suka barbazu a kasar ta Kongo, amma a daya hannun ta hakikance da kutsawar sojojinta zuwa Burundi domin farautar ‘yan tawayen Hutu.