Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 21.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da halin da ake ciki a Malawi sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar alhamis

A wannan makon mai dai kamar sauran makonni ukun da suka gabata, halin da ake ciki a yammacin kasar Sudan shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, amma duk da haka ba su yi watsi da sauran sassa na nahiyar Afurka ba. Misali jaridar Neues Deutschland ta sake lekawa yammacin Sahara domin bitar abin da ta kira matakan kasar Moroko domin hana ruwa gudu ga ikon cin gashin kan yammacin Sahara. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Har yau yankin yammacin Sahara da ya taba wanzuwa karkashin mulkin mallakar kasar Spain na ci gaba da kasancewa karkashin mamayen kasar Moroko. Mazauna yankin na ci gaba da gwagwarmayar neman ikon cin gashin kansu, a yayinda ita kuma MDD ta gaza wajen samun bakin zaren warware wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung tayi bitar shawarar da kwamitin sulhu na MDD ya tsayar ne a game da binciken dukkan matakai na keta haddin dan-Adam da aka dauka a kasar Cote d’Ivoire tun abin da ya kama daga shekara ta 2002, amma kuma ta kara da korafin cewar majalisar ta ki ta fito fili ta kalubalanci shugaba Gbgbo. Jaridar sai ta ce:

"A zaman da yayi domin tattauna rikicin Cote d’Ivoire, kwamitin sulhu na MDD ya ki ya fito fili yayi Allah Waddai da masu alhakin kisan kiyashin da aka yi wa masu adawa da gwamnati a birnin Abidjan a cikin watan maris da ya wuce. To sai dai kuma ko da yake kafofin yada labaran kasar ta Cote d’Ivoire dake goyan bayan shugaba Gbagbo sun shiga doki da murna a game da suke ganin tamkar wata nasara ce ga shugaba, amma kwamitin sulhun na MDD a daya bangaren ya ci alwashin binciken dukkan matakan keta hakkin dan-Adam da aka fuskanta a wannan kasa tun bayan barkewar yakin basasarta a shekara ta 2002."

A can kasar Malawi ana fuskantar barazanar tayar da zaune tsaye sakamakon zargin magudi a zaben kasar da aka gudanar a jiya alhamis. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

"Kungiyoyi masu zaman kansu da mujami’un kasar Malawi na tababa a game da yiwuwar caba magudi a zaben kasar da aka gudanar a jiya alhamis ko da yake babu wata alamar dake nunar da hakan a rumfunan zaben, wadanda wasu daga cikinsu ba a bude su akan kari ba. Dalilin haka dai shi ne takardun zabe sama da miliyan shida da aka buga a yayinda ita kanta kasar gaba daya mazaunanta ba su kai yawan mutane miliyan shida ba."

Bayan watanni masu yawa da aka yi ana famar kai ruwa rana tsakanin jam’iyyun dake mulkin hadin gambiza a Janhuriyar Demokradiyyar Kongo a yanzu dukkan sassan da lamarin ya shafa sun cimma daidaituwa akan raba madafun iko tsakaninsu. A lokacin da take gabatar da sharhi game da haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Shuagabannin mulkin hadin gambiza a kasar Kongo sun sa kafa suka yi fatali da wata kyakkyawar dama da ta samu a garesu domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hadin kan wannan kasa. Bayan shekaru gwammai da tayi tana fama da danniya da kama karya tare da yakin basasar da ya biyo baya, wanda yayi kaca-kaca da dukkan hanyoyin sadarwarta, kasar Kongo ta samu ‘yar sararawa a hukumance ta yadda zata iya yin wani sabon yunkuri domin sake gina makomarta. Abin da zai taimaka game da haka kuwa shi ne shigar da illahirin al’umarta su kimanin miliyan shida domin a dama da su a matakan da za a dauka na hana amfani da iko da hanyar da ba ta dace ba ko kuma billar wani sabon rikici. Amma a maimakon haka shuagabannin dake mulkin hadin gambiza sai suka gwammace su raba madafun mulkin tsakaninsu ba tare da tsoma bakin talakawan kasa ba."