1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da hali na zaman dardar da ake fuskanta tsakanin kasar Kongo da makobciyarta Ruwanda

Shugaban Kagame na Ruwanda da takwaransa Joseph Kabila na Kongo na rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Shugaban Kagame na Ruwanda da takwaransa Joseph Kabila na Kongo na rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

A wannan makon dai babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus shi ne gasar kwallon kafa ta cin kofin kasashen Turai, inda aka fi da kungiyar kwallon kafa ta kasar tun a zagayen farko. To sai dai kuma duk da haka jaridun ba su yi watsi da al’amuran Afurka ba. Misali jaridar Frankfurter Rundschau ta lura da yadda ake dada fuskantar barazanar billar wani sabon yaki a kasar Kongo, inda a wannan makon gwamnati a birnin Kinshasa ta tura sojojin kasar zuwa yankin iyaka tsakaninta da Ruwanda. A lokacin da take bayani game da haka jaridar ta Frankfurter Rundschau cewa tayi:

"Kimanin sojoji dubu 10 gwamnati a fadar mulki ta kinshasa ta tura zuwa lardin Kudancin Kivu domin murkushe ‘yan tawaye dake samun daurin gindi daga makobciyar kasa ta Ruwanda, lamarin da ya sanya kasar Afurka ta Kudu take gargadi a game da yiwuwar billar yaki tsakanin kasashen biyu dake makobtaka da juna."

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi bitar gargadin da ATK tayi a game da barazanar billar yaki tsakanin makobtan kasashen Kongo da Ruwanda, inda Ruwandar ke zargin Kongo da yunkurin ta da zaune tsaye a wannan yanki jaridar sai ta kara da cewar:

"Halin zaman dardar sai dada yin tsamari yake yi tsakanin Ruwanda da Kongo, sakamakon dimbim sojoji da kasar Kongo ta dirke a iyaka tsakaninta da makobciyarta Ruwanda a fafutukar karya alkadarin ‘yan tawayen dake amfani da garuruwan Beni da Kindu da kuma Kalemie wajen shirya hare-harensu. Amma ita Ruwanda, a ganinta, wannan mataki wani yunkuri ne na kai mata farmaki kuma ta ce ba zata zauna ta harde kafafuwanta ba. Kimanin mutane dubu 30 suka kaurace wa yankin gabacin Kongo sakamakon bata-kashin baya-bayan nan da aka fuskanta tare da ‘yan tawayen."

Rahotanni masu nasaba da MDD sun ce al’amura na dada yin tsamari a yankin kudancin Afurka sakamakon yaduwar cutar Aids da kuma rashin damina mai albarka. Jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar wannan mawuyacin hali inda take cewar:

"Alkaluma na MDD sun kiyasce cewar mutane kimanin miliyan goma ne ke dauke da kwayoyin cutar nan ta Aids a yankin kudancin Afurka yanzu haka. Hatta kudaden da kasar Amurka da MDD ke da niyyar turawa yankin nan ba da dadewa ba, ba zasu taimaka a tsame kudancin Afurka daga wannan bala’i ba, musamman ta la’akari da sako-sako da su kansu gwamnatocin kasashen da lamarin ya shafa suke yi da wannan mummunan ci gaba dake neman ya kai kasashensu ya baro. A baya ga haka ana fama da karancin amfanin noma a kasashe kamar Namibiya da Malawi da Lesotho da Swaziland da kuma Zimbabwe, wadda ita ce ma ta fi fama da koma bayan amfanin noma."

A cikin wata sabuwa kuma a can kasar Kenya an ba da rahoton mutuwar mutane sama da 120 sakamakon aiwatar da wata masara mai guba. Matsalar kuwa tafi shafar yankunan kasar ne da ake fargabar fuskantar karancin amfanin noma a wannan shekarar, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma kara da cewar:

"Masara dai ita ce amfani mafi a’ala da al’umar kasar Kenya ke aiwatarwa a rayuwarsu ta yau da kullum, kuma wannan ba shi ne karo na farko da aka fuskanci matsalar funfunar aflatoxin dake tattare da guba a masarar da kasar ke nomawa ba. To sai dai kuma a wannan karon lamarin na nema ya zame wa kasar gagara-badau kuma talakawanta ‘yan rabbana ka wadata mu sune suka fi jin radadinta. Bisa ga ra’ayin kungiyar taimakon abinci ta MDD wajibi ne a dauki matakan kai gudummawa ga akalla mutane miliyan daya da dubu 400, wadanda zasu iya fuskantar barazanar karancin abninci a kasar ta Kenya tun abin da ya kama daga watan agusta mai zuwa."