Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Muhimman batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus akan al'amuran Afurka a wannan makon sun hada ne da halin da ake ciki a kasashen Sudan da Ruwanda

A wannan makon muhimman batutuwa guda biyu ne suka fi daukar hankalin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka. Da farko halin da ake ciki a kasar Sudan tare da ba da la’akari da ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell da kuma sakatare-janar na MDD Kofi Annan suka kai kasar domin gane wa idanunwansu abin dake faru a lardin Darfur na yammacinta. Sai kuma zaman dardar da ake fama da shi tsakanin Ruwanda da janhuriyar demokradiyyar Kongo ta la’akari da ziyarar da shugaban Ruwanda Paul Kagame ya kawo nan kasar ta Jamus. Amma da farko zamu leka kasar Sudan, inda jaridar Neues Deutschland ke bayanin alkaluman majalisar dikin duniya dake batu a game da dubban mutanen da suka yi asarar rayukansu a Darfur na yammacin Sudan. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Yawan mutanen da suka yi asarar rayukansu a kashe-kashen gillar da dakarun sa kai masu samun daurin gindin gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ya zarce yadda ake zato. Kimanin mutane miliyan daya da dubu 200 suka tagayyara sakamakon hare-haren da dakarun na janjaweed ke kaiwa kan bakar fata a lardin Darfur."

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ba da la’akari ne da ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya kai kasar ta Sudan a wannan makon ne domin gabatar da bayani akan alkaluman da hukumar taimakon jinkai ta kasar Amurka USAID da bayar dangane da yawan mutane da kaddara ta rutsa dasu sakamakon matakan tsabtace kabila da dakarun sa kai Larabawa jajayen fatu ke dauka kan bakar fata a lardin Darfur, inda take cewar:

"Alkaluma masu nasaba da hukumar taimakon jinkai ta Amurka USAID a takaice sun kiyasce yawan mutanen da suka jirkata sakamakon matakan tsabtace kabila a lardin Darfur na yammacin Sudan ya kai dubu talatin a cikin watanni 16 da suka wuce. Dangane da yawan wadanda suka tagayyara ko kuma suka tsere domin neman mafaka a kasar Chadi kuwa adadin ya kai miliyan daya, a baya ga wasu miliyan biyu dake bukatar taimakon abinci ruwa a jallo. A dai kwanakin baya-bayan nan an sha yi wa kasar ta Sudan barazanar kakaba mata matakai na takunkumi muddin ba ta dakatar da wannan ta’asa ba."

A wannan makon shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya kawo ziyara nan Jamus inda yayi gargadi a game da barazanar billar wani sabon yaki da ake fuskanta a kasar Kongo sannan yayi kira da a dauki nagartattun matakai domin kawo karshen kisan kiyashin da ake fuskanta a kasar Sudan. Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi hira da shi, sannan ta gabatar da cikakken bayani game da shugaban na Ruwanda tana mai cewar:

"A zamanin baya shugaban kasar Ruwanda ya kasance cikin rukunin shuagabannin Afurka dake samun cikakken goyan baya daga kasar Amurka sakamakon matakansu na neman sauyi da dora nahiyar Afurka kan wata sahihiyar turba ta ci gaba da farfadowar tattalin arziki da kyautata makomar rayuwar jama’a. Amma tuni murna ta koma ciki tun bayan da sojojin Ruwanda suka rika kutsa kai cikin makobciyar kasa ta Kongo tare da zargin kasar ta Ruwanda yunkurin wawason dimbim albarkatun da Allah Ya fuwace wa makobciyar tata."