Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

Matsalar cutar Aids dake gurgunta tattalin arzikin kasashen Afurka tana daya daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi a kansu a wannan makon mai karewa

A wannan makon ne aka gabatar da wani sabon zagayen taron sulhu dangane da rikicin lardin Darfur na kasar Sudan a Abujan Nijeriya, wanda ke samun halarcin gaggan jami’an gwamnatin Sudan da kuma wasu wakilai ‘yan sa ido daga gwamnatocin kasashen Afurka. A lokacin da take ba da rahoto game da taron jaridar DIE TAGESZEITUNG nuni tayi da cewar:

"Zagayen farko na irin wannan taron sulhu an gabatar da shi ne a kasar Habasha watan da ya gabata, wanda kuma ya tarwatse ba tare da an cimma tudun dafawa ba, sakamakon kiyawa kememe da gwamnatin Sudan tayi a game da kwance damarar dakarun Larabawa na Janjaweed domin zama sharadin zaman lafiya da ‘yan tawayen Darfur. Wannan maganar, ita ce za a sake mayar da hankali kanta a zauren taron na Abuja, wanda aka sikankance cewar za a dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da shi. Tun da farkon fari ne dai gwamnatin Sudan ta ki amincewa da shawarar tsugunar da sojan kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afurka a lardin na Darfur."

Ta la’akari da mawuyacin halin da ake ciki a kasar Sudan, a wannan makon Jamus ta fara shawara a game da tsugunar da rundunar sojanta domin aikin kiyaye zaman lafiya a duk inda bukata ta kama a nahiyar Afurka. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka inda ta ambaci ministan tsaron Jamus Peter Struck yana mai cewar:

"Ko da yake a halin yanzu haka sojojin Jamus kimanin dubu takwas ne ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasashen ketare, amma akwai yiwuwar tura wasu karin sojojin domin aikin tsaron zaman lafiya a nahiyar Afurka. Domin kuwa Jamus na da wani alhaki na musamman akanta dangane da makomar wannan nahiya. Kasar zata iya gabatar da wannan mataki a hadin kai tare da tsaffin kasashen mulkin mallaka kamar Birtaniya da Faransa da kuma Belgium domin tabbatar da kwanciyar hankali a lardin Darfur idan har MDD ta fito fili ta bukaci hakan."

Bayan kimanin shekara daya na mulkin hadin gambiza, a wannan makon ‘yan tawayen kasar Kongo sun janye daga gwamnati sakamakon wata ta’asa ta kisan kiyashin da aka fuskanta a Burundi makonni biyu da suka wuce. To sai dai kuma wannan janyewar kamar yadda Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta nunar ka iya zama wata sabuwar dama a fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar dake can kuryar tsakiyar Afurka. Jaridar ta gabatar da sharhi inda take cewar:

"Ita kanta gwamnatin hadin gambizar da tayi tsawon shekara daya tana mulki ta gaza wajen samar da zaman lafiya a duk fadin kasar Kongo, saboda ta kasa kwance damarar makaman ‘yan tawaye da sojojin dake fafatawa da juna. Wannan gibin da ake fama da shi shi ne ya sanya murna ta koma ciki a game da ci gaban da aka samu a siyasance. A yanzu muhimmin abin da ake bukata shi ne sabbin dabaru da taimako na kasa da kasa tun kafin al’amura su ta’azzara."

Cutar nan ta Aids mai karya garkuwar jikin dan-Adam tana ci gaba da barazanar gurgunta tattalin arziki da kuma tabarbara al’amuran ilimi da na gudanarwa a kasashe da dama na nahiyar Afurka a cewar Jaridar NEUES DEUTSCHLAND. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Yaduwar cutar Aids a kasashen Afurka, musamman na yankin kudancin nahiyar, na taimakawa wajen tabarbara al’amuran tattalin arziki da koma bayan ilimi da kuma gurguncewar ayyukan gudanarwa na gwamnati. Dalili kuwa shi ne yadda cutar ke awon gaba da kwararrun masana da ma’aikata da malaman makaranta a dukkan bangarori na rayuwa a kasashen da lamarin ya shafa. Akwai bukatar taimakon kudi na dalar Amurka miliyan dubu 20 a shekara muddin ana fatan dakatar da wannan mummunan ci gaba."