1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 10, 2004

Sabon halin da aka shiga a kasar Angola na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/Bvpj

Da farko zamu fara ne da yada zango a kasar Sudan domin bitar halin da ake ciki a game da makomar zaman lafiyar lardin Darfur dake fama da riki. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta gabatar da sharhi a game da yadda MDD ke wa rikicin rikon sakainar kashi, inda take cewar:

"Sako-sako da MDD ke yi da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a lardin Darfur na kasar Sudan wani mummunan abin kunya ne. Bayan samun kwanaki goma da cikar wa’adin da majalisar ta kayyade wa gwamnatin Sudan domin kwance damarar dakarun dake da alhakin kisan kare dangin dake wanzuwa a lardin yammacin kasar, sai a jiya alhamis ne kwamitin sulhu ya sake hallara domin tattaunawa akan mataki na gaba da za’a iya dauka bisa manufa. Hakan kuwa na ma’ana ne cewar fadar mulki ta Khartoum tana iya ci gaba da cin karenta babu ba babbaka tun da yake majalisar dinkin duniyar ba wani abin da take da ikon tabukawa in banda tattaunawa da kayyade mata wani sabon wa’adi maras ta’asiri."

A wannan fannin ba wani banbanci tsakanin MDD da Kungiyar Tarayyar Turai a cewar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU. Jaridar sai ta ci gaba da bayani da cewar:

"Ko da yake KTT ta gabatar da bayani akan matakai na takunkumin da zata iya kakaba wa kasar Sudan, amma a wannan halin da muke ciki ba zata yi garajen daukar wani mataki ba zata sa ido ne ta ga irin ci gaban da za a samu a fafutukar cimma zaman lafiyar lardin Darfur. Da wannan shawarar kungiyar ta bi sawun MDD, wacce ta ce zata sararawa fadar mulki ta Khartoum domin ta ga salon kamun ludayinta bisa manufa, duk kuwa da cewar yau kwanaki goma ke nan da cikar wa’adin kwanaki 30 da majalisar ta kayyade mata domin kwance damarar dakarun dake da alhakin kashe-kashen kare dangin dake wanzuwa a Darfur."

A cikin wata sabuwa kuma ana fama da gwagwarmaya a kokarin cin gajiyar albarkar damentin da Allah Ya fuwace wa kasar Angola. Dalili kuwa shi ne matakin da mahukuntan kasar ke dauka na korar baki ‘yan ci rani daga rijiyoyin hakar wannan ma’adani mai alfarma, wadanda galibi ‘yan usulin janhuriyar demokradiyyar Kongo ne. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar rikicin tana mai cewar:

"Tun a shekarar da ta gabata ne mahukuntan kasar Angola suka fara fatattakar ‘yan ci rani na kasar Kongo dake fafutukar cin gajiyar arzikin damentin da Allah Ya albarkaci Angolar da shi. Kimanin ‘yan kasar ta Kongo dubu 120 ne aka kora daga Angola tsakanin watan desamban bara da watan mayu na bana. To sai dai kuma a wannan karon ga alamu ‘yan kasar Kongon su fara jan daga domin mayar da martani. Bayanai na mahukuntan Angola sun ce mutane da dama suka yi asarar rayukansu a lardin Luanda Norte dake da arzikin damenti sakamakon musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da ‘yan kasar Kongo dake cikin damarar makamai a makonnin baya-bayan nan."

A can kasar Burkina Faso, ko da yake akwai kafofin yada labarai masu zaman kansu, amma fa ‘yan jarida na dari-dari wajen tsage gaskiya saboda makomar rayuwarsu, a cewar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU lokacin da take ba da rahoto akan wani dan jaridar kasar ta Burkina Faso mai suna Norbert Zongo misalin biyar shida da suka wuce. Jaridar ta kara da cewar:

"Har yau ana ci gaba da lalube a cikin dufu a game da kisan gillar da aka yi wa Norbert Zongo dan jaridar kasar Burkina Faso, wanda a daidai ranar 13 ga watan desamban 1999, tare da wasu mukarrabansa su uku lokacin da suke kanhanyarsu ta zuwa gonarsa. Kuma ko da yake mutane shida ne ake tuhumarsu da wannan danyyen aiki, amma daya ne kawai daga cikinsu aka yanke masa hukunci. Shi kansa shugaban kasar dan kama-karya ne kuma hakan ta sanya ‘yan jarida ke sara tare da duban bakin gatarinsu wajen tsage gaskiya da sukan lamirin manufofin gwamnati."