1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 29, 2004

Matsalar mulke-mulke na rai da rai a nahiyar Afurka na daya daga cikin abubuwan da masharhanta na jaridun Jamus suka mayar da hankali kansa a wannan makon mai karewa

https://p.dw.com/p/Bvpf

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon dai har da halin da ake ciki a kasar Kongo da fafutukar sasanta rikicin lardin Darfur na kasar Sudan. A cikin rahoton da ta bayar dangane da kasar Kongo a karkashin taken:Murna na neman komawa ciki dangane da zaman lafiyar kasar Kongo, jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

"Gwamnatin shugaba Joseph Kabila ta harzuka da kalaman da aka ji daga bakin ministan harkokin wajen kasar Belgium Karel De Gucht, inda yake sukan lamirin halin da ake ciki a kasar Kongo kuma a sakamakon haka ta kira jakadanta dake Brussels zuwa Kinshasa wai domin neman shawarwari. Shi dai ministan harkokin wajen na Belgium yayi kakkausan suka inda ya ce bai hangi wani ci gaba na a zo a gani ba, inda ‘yan siyasa dake da hannu a gwamnatin rikon kwaryar da aka nada suka dukufa wajen kalubalantar juna sannan su kuma mahukunta, tuni cin hanci ya zama ruwan dare tsakaninsu. Wannan dai ba shi ne karon farko da De Gucht ke Allah waddai da halin da ake ciki a kasar Kongo ba. Alakar Belgium da kasar da ta rena a tsakiyar Afurka tana da muhimmanci saboda ita Belgium ce ke daidaita manufofin KTT a game da kasar ta Kongo."

A ziyarar da ya kai ga kasar Sudan kantoman kungiyar tarayyar Turai akan manufofin ketare da na tsaro Javier Solana ya bayyana kwarin guiwarsa a game da cimma zaman lafiyar kasar dake fama da rikici. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Ita dai ziyarar ta Solana zuwa Khartoum da Addis Ababa tana da nufin janyo hankalin mutane zuwa ga irin gudummawar da KTT ke bayarwa a fafutukar lafar da kurar rikicin da yaki ci ya ki cinyewa a lardin Darfur. Kazalika domin bayyanarwa a fili cewar dangantakar kasashen turai da nahiyar afurka ba ta tuke ne akan taimakon kudi da alakar tattalin arziki ba, ta hada har da manufofin siyasa a kokarin lafar da kurar rikice-rikice dake addabar sassa dabam-dabam na nahiyar Afurka."

Shi dai rikicin lardin Darfur, kamar yadda wasu ke gani, musabbabinsa shi ne gwagwarmayar dora hannu akan filayen noma da rijiyoyin ruwa, musamman ta la’akari da yadda yashi ke dada mamayar arewacin kasar Sudan. amma a daya bangaren akwai masu dora laifin akan gwamnatin Sudan, wacce sakamakon manufofinta na son kai, ya sanya al’amura ke dada yin tsamari a wannan yanki. jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi sharhi tana mai cewar:

"A hakika da dai a ce fadar mulki ta Khartoum ta mayar da hankalinta wajen shigar da sauran yankunan kasar a shawarwarin ikon cin gashin kai a karkashin tsarin mulkin tarayya, a maimakon mayar da hankali kacokam da tayi akan yankin kudancin Sudan, to da kuwa al’amura ba su ta’azzara suka dauki wannan mummunan fasalin da ake ciki ba. A sakamakon nasarorin da ‘yan tawayen kudancin Sudan ke samu ne gwamnati ta tsayar da shawarar yi wa Larabawan Janjaweed damarar makamai da kuma cusa musu akidar kyamar bakar fata bisa ikirarin cewar suna kokarin mamaya da kwace dukkan filayen noma a lardin Darfur ta yadda larabawan makiwata ba zasu samu sauran filayen kiwata dabbobinsu ba."

Wani binciken da aka gudanar a kasashe goma na nahiyar Afurka, kimanin kashi 50% na mutane 7500 da aka saurari albarkacin bakinsu sun bayyana gamsuwarsu da matsayi na rayuwa da suke ciki, duk kuwa da matsaloli na cin hanci da rashin aikin yi da nahiyar ke fama da su. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

"Babban abin dake ci wa al’umar Afurka tuwo a kwarya shi ne rashin samun wani canji ga gwamnatocinsu, inda ake da masu mulke-mulke na rai da rai. A kasashe uku ne kawai aka samu canjin siyasa a cikin ruwan sanyi a nahiyar ta Afurka a cikin shekarun baya-bayan nan. wadannan kasashe sun hada ne da Ghana da Senegal da kuma Kenya. Babban misali a game da mulkin rai-da-rai kuwa shi ne shugaba Biya na kasar Kamaru, wanda duk da rashin koshin lafiyarsa ya dage akan lalle shi ne ya lashe zaben kasar domin ci gaba da mulki."