1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Mawuyacin halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire da takunkumin da MDD ta kakaba mata shi ne abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

Halin da ake ciki a kasar Cote d’Ivoire shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon, sai kuma matsalar amfani da yara da ake yi a yake-yake na basasa, musamman a wasu kasashen dake fama da rikici a nahiyar Afurka. Kazalika rikicin lardin Darfur da kuma fafutukar da ‘yan gudun hijira daga kasashen yammacin Afurka ke yi domin shigowa nahiyar Turai. Amma da farko zamu fara ne da ya da zango a kasar Cote d’Ivoire, wacce a wannan makon kwamitin sulhu na MDD ya kakaba mata wasu matakai na takunkumi. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

"Da farko dai an kakaba wa Cote d’Ivoire takunkumin haramcin cinikin makamai da ita nan take, wanda kuma zai yi aiki na tsawin watanni goma sha uku. Wannan takunkumin ya hada da ‘yan tawaye da kuma gwamnati kuma ta haka kasar ba zata iya sayen sabbin jiragen saman yaki ko masu saukare ungulu ba bayan da askarawan faransa suka bannatar da illahirin jiragen saman yakin da take mallaka domin mayar da martani akan amfanin da tayi dasu na kai farmaki da kisan sojojin Faransar da dama. An kayyade wa marikitan kasar ta Cote d’Ivoire wa’adin nan da sha biyar ga watan desamba domin nuna halin sanin ya kamata wajen cimma sulhu, in kuwa ba haka ba za a kakaba wa jami’an dukkan bangarorin dake da hannu a wannan rikici takunkumin haramcin tafiye-tafiye da kuma dora hannu kan kadarorinsu."

Jaridar ta FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta kara da yin nuni da cewar: Take-taken kungiyar tarayyar Afurka ta AU a game da rikicin Cote d’Ivoire abu ne dake nunarwa a fili a game da damuwar dake tattare a zukatan kasashen Afurka, musamman ma na yammacin nahiyar a game da tabarbarewar al’amuran wannan kasa dake da muhimmanci ta fuskar tattalin arziki, sannan suka kuma ankara da gaskiyar cewar shugaba Laurent Gbagbo, shi ne ainifin mai hana ruwa gudu wajen cimma sulhu.

A hakika da wuya ne kwamitin sulhu na MDD ke barin mazauninsa a birnin New York domin gudanar da taro a ketare. Amma a wannan makon kwamitin ya hallara domin guidanar da wani taro na musamman a Nairobin Kenya, inda ya mayar da hankali kacokam akan kasar Sudan. A lokacin da take ba da rahoto game da haka Jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

"Dalili dai shi ne kasancewar Sudan ta zama tamkar zakaran gwaji ne ga ikon da MDD ke da shi na warware rikici. Kafofin majalisar na kwatanta mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur tamkar wani rikici mafi muni a duniya yanzu haka, wanda kuma yake dada jefa mutane cikin kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsu. Yakin wannan lardi, wanda ya fara a wajejen tsakiyar shekarar da ta wuce yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu dari, sannan ya tagayyara wasu sama da miliyan daya da dubu dari takwas. Ci gaban wannan rikicin zai iya sanya murna ta koma ciki a game da kwaryakwaryar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin fadar mulki ta Khartoum da ‘yan tawaye a can kudancin Sudan."

A wannan makon jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi bitar matsalar nan ta tuttudowar ‘yan gudun hijirar Afurka dake bi ta hamadar Sahara domin shigowa nahiyar Turai, inda take cewar:

Tun misalin shekaru 20 da suka wuce ne ake satar hanyar shigowa da ‘yan gudun hijirar Afurka, wadanda akan biya da su ta Agadez a Nijer ko Gao a Mali domin kutsawa arewacin Afurka a fafutukar karasowa zuwa nahiyar Turai. Wannan cinikin dake samar da kazamar riba ga masu manyan motoci ko jip-jip sai dada bunkasa yake yi ba kakkautawa.