Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 17.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Ziyarar da shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya kai nahiyar Afurka na daga cikin muhimman batutuwan da suka fi daukar hankalin jaridun Jamus a game da al'amuran Afurka

Daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da al’amuran Afurka a wannan makon har da ziyara ta kwanaki goma da shugaban kasa Horst Köhler ya kai ga wasu kasashe hudu na wannan nahiya, sai kuma mawuyacin halin da aka sake fadawa ciki a rikicin kasar Kongo da ya ki ci ya ki cinyewa. Da farko dai zamu fara ne da rahoton da jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta rubuta a game da wannan ziyara inda take cewar:

"A ziyararsa ga kasashen Afurka dake da nufin nuna goyan baya ga canje-canjen da ake samu a wannan nahiya, shugaban kasar Jamus Horst Köhler, ko da yake yayi kira ga kasashen dake da ci gaban masana’antu da su kawar da shingen ciniki da manufarsu ta karya farashin kaya tare da bunkasa yawan kudaden taimakon raya kasa ga kasashen Afurka, amma a daya bangaren yayi godo ga su kansu kansu kasashen nahiyar da su tashi tsaye wajen yaki da cin hanci da manufofin nuna son kai, wadanda ke daya daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu wajen ta da komadar tattalin arzikin Afurka. A jawabin da ya gabatar ga babbar mashawartar Kungiyar Tarayyar Afurka a Addis Ababa Horst Köhler yayi madalla da kudurin da kungiyar ta tsayar na kafa rundunar kwantar da tarzoma domin katsalandan da tsaron lafiya a sassan da ake fama da rikice-rikice a cikinsu. A karshe dai shugaban na kasar Jamus ya bayyana fatan ganin Afurka ta taka muhimmiyar rawa a huldodin ciniki da siyasar duniya tare da yin na’am da ganin nahiyar ta samu dawwamammen wakilci a kwamitin sulhu na MDD."

A wannan makon rukunin farko na sojan Jamus suka fara sauka kasar Gambiya akan hanyarsu ta aikin kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur na yammacin kasar Sudan. A lokacin da take gabatar da rahoto kan haka jaridar DIE TAGESZETUNG cewa tayi:

"Wannan manufar tana da muhimmanci domin nuna halin sanin ya kamata akan manufa. Domin kuwa daya daga cikin muhimman manufofin da Jamus ta sa gaba shi ne ba wa kungiyar tarayyar Afurka goyan baya a matakanta na kiyaye zaman lafiya, kuma rikicin Darfur ya zama tamkar zakaran gwaji ne ga matakan katsalandan na kungiyar."

Kimanin mutane dubu 350 suka kama hanyar gudun hijira sakamakon mawuyacin halin da aka sake fadawa a ciki a rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a janhuriyar demokradiyyar Kongo. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta rubuta sharhi akan haka tana mai cewar:

"Hatta alkaluman da ake bayarwa ba su wadatar wajen bayyana mummunar ta’asar dake wanzuwa a janhuriyar demokradiyyar Kongo ba, inda aka ce kusan mutum dubu daya kan yi asarar rayukansu a kowace rana ta Allah duk da ikirarin kawo karshen yakin basasar kasar ta kuryar tsakiyar Afurka. Kuma tun bayan barkewar rikicin a 1996 kawo yanzu mutane sama da miliyan uku da dubu dari takwas suka bakunci lahira. Dadai wadannan alkaluma sun shafi wani yankunan duniya ne dabam da kuwa an sha fama da kiraye-kiraye da kokwe-koke na kungiyoyin kasa da kasa. Amma dangane da kasar ta Kongo tuni aka yi ko oho da ita duk kuwa da cewar yakinta shi ne mafi muni a tsakanin yake-yaken da ake fama dasu a sassa dabam-dabam na duniya yanzu haka. Ta la’akari da haka ba zai zama abin mamaki ba idan mutum yayi hasashen cewar za a ci gaba da wannan kashe-kashe a kasar Kongo har sai Illamasha-Allahu."