1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

January 14, 2005

Halin da ake ciki a kasar Sudan na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

https://p.dw.com/p/BvpX

A wannan makon mai karewa ma jaridu da mujallun Jamus sun fi mayar da hankali ne akan halin da ake ciki a yankunan kasashen kudancin Asiya da bala’in tsunami ya rutsa da su da kuma hada-hadar taimakon da ake gabatarwa ba kakkautawa. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi amfani da wannan dama domin gabatar da rahoto a game da jerin kasashen dake bukatar taimako, amma aka yi fatali da makomarsu, inda take cewar:

"A kasar Sudan, ana ci gaba da fama da yakin basasa a lardinta na Darfur, kuma akwai mutane kimanin miliyan daya da dubu dari shida dake bukatar taimako domin ceto rayuwarsu. Abin da ake bukata na kudi ya kai dalar Amurka miliyan 719, amma duka-duka abin da aka bayar bai zarce miliyan arbaminya ba. Ita ma Liberiya tana bukatar dalar Amurla miliyan 140 dangane da ‘yan gudun hijirarta dake komawa gida, amma ta samu taimakon dala miliyan 60 ne kacal. Ita kuwa Somaliya abin da take bukata ya kai dala miliyan 120, amma aka kaddamar da dala miliyan 62. Alkaluman dai suna da yawa ta yadda ba za a iya kawo bayani kansu dalla-dalla a cikin wannan dan gajeren lokaci ba. Gaba daya abin da MDD ke bukata don taimaka wa sauran sassan duniya dake fama da rikici, a shekarar nan ta 2005, ya kai dala miliyan dubu uku da dari biyar."

Ita kuwa jaridar KÖLNER STADT-ANZEIGER ta mayar da hankali ne ga kasar Somaliya, wadda ta ce a hakika abin dake hana ruwa gudu wajen kai wa kasar taimakon da ya kamata shi ne kasancewar bata da wata tsayayyar gwamnati ta tsakiya, lamarin da ya sanya masu gabatar da taimakon ke fargaba a game da makomar rayukansu. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Kasar Somaliya dau ta fara farfadowa ne daga matsalolin da ta sha fama da su na fari da ambaliyar ruwa a cikin ‘yan shekarun da suka wuce, amma sai ga shi ta sake afkawa cikin wata sabuwar masifar ta mahaukaciyar igiyar ruwannan ta tsunami da tayi kaca-kaca da wasu yankunanta. Amma abun da ya kara kazanta lamarin shi ne tabarbarewar al’amuranta na tsaro ta yadda kungiyoyin taimako na kasa da kasa ke fargabar tura ma’aikatansu zuwa yankin. Domin kuwa galibi wasu ‘yan bindiga dadi ne kan tsare motocin dake dauke da kayan taimakon su kuma wawashe dukkan abin da motocin ke dauke da shi. Wannan shi ne ainifin abin dake haddasa tafiyar hawainiya ga matakan taimakon Somaliya."

Bayan shekaru 20 na yakin basasa an cimma daidaituwa akan zaman lafiyar kasar Sudan. Jaridar DER TAGESSPIEGEL tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

"Da yawa daga cikin bakar fatar kudancin Sudan na tattare da imanin cewar abu mafi alheri ga makomar rayuwarsu shi ne ballewa daga gwamnatin Larabawa a fadar mulki ta Khartoum. Amma kuma sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya kwatanta wannan yarjejeniyar da ta kawo yakin basasar da yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da miliyan biyu a kasar Sudan a cikin shekaru 20 da suka wuce, tamkar wata kyakkyawar dama ta shiga wani sabon babi na zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin jinsuna da kabilu dabam-dabam da kasar ta kunsa. Shi ma madugun ‘yan tawayen SPLA John Garang ya ce wannan yarjejeniyar zata ba wa Sudan wata sabuwar suffa ta wanzuwa."

Ita ma jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi bitar yarjejeniyar zaman lafiyar ta Sudan tana mai bayyana tababarta a game da wannan kawance da aka kulla tsakanin shugaba El-Bashir da madugun ‘yan tawaye John Garang. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Wannan yarjejeniyar da aka kulla tana ma’ana ne cewar kasar Sudan zata koma karkashin wasu shuagabanni biyu dake da salon mulki na kama-karya. Amma fa tilas a saka ayar tambaya a game da wannan kawance. Domin kuwa shi shugaba El-Bashir ya lashi takobin murkushe ‘yan tawayen Darfur. Shi kuwa John Garang, ko da yake baya kaunar ganin ‘yan tawayen su yi masa cikas dangane da gagarumin matsayin da ya samu da kuma arzikin man da Allah Ya fuwace wa yankin kudancin Sudan, amma fa sanin kowa ne cewar yana mara wa ‘yan tawayen baya. Mai yiwuwa yana yin hakan ne domin ya kara raunana matsayin shugaba El-Bashir."