Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 18.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Togo shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon mai karewa

A wannan makon mai karewa dai, babban abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka, shi ne halin da ake ciki a kasar Togo da Sudan, sai kuma zargin da ake wa sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a game da cin mutuncin mata a kasar Kongo. Amma da farko bari mu fara leka kasar Togo, inda jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG, bayan bitar zanga-zangar da ake ci gaba da yi a kasar take cewar:

"An samu mutanen da suka yi asarar rayukansu a zanga-zangar da aka gabatar a Lome, fadar mulkin kasar Togo, domin adawa da sabon shugaba Faure Eyadema. Yan hamayya sun gabatar da zanga-zangar tasu ce suna masau fatali da dokar haramcin jerin gwanon da aka kafa har tsawon watanni biyu. Gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka ta Ecowas tayi Allah Waddai da matakin da mahukuntan kasar Togo suka dauka na nada Faure Eyadema da aka yi domin ya gaji mahaifinsa ta kuma yi barazanar kakaba wa kasar takunkumi muddin ba ta sake maido da aikin daftarin tsarin mulkinta ba."

Daga bisanin nan aka fallasa wata tabargazar fyade da ake zargin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da aikatawa a kasar Kongo. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar zargin tana mai cewar:

"A sakamakon tabargazar fyaden da suka rika yi wa mata a Goma ta gabacin kasar kongo sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD, musamman daga kasashen Moroko da Afurka ta Kudu, gwamnatin kasar Moroko ta kori babban kwamandan rundunarta da mataimakinsa sannan aka tsare wasu sojojin kasar guda shida da suka taba aiki karkashin tutar MDD a kasar Kongo. Sojojin na Moroko na cikin rukunin sojan kiyaye zaman lafiya na farko da MDD ta tura zuwa kasar ta Kongo a shekara ta 2001, sannan aka maye gurbinsu da sojan ATK, wadanda aka ce cin zarafin matan da suka yi ya zarce na sojan Moroko."

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU, a cikin sharhin da ta gabatar a game da wannan mummunar tabargaza cewa tayi:

"Tabargazar fyade da ake zargin sojan MDD da aikatawa a kasar Kongo abu ne da ya shafa wa ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar kashin kaza, kuma mutane ba zasu taba sake yarda da gaskiyar matakan kiyaye zaman lafiyar ba, ganin yadda su kansu ainifin sojojin da aka tura domin su ba su kariya, su ne suke cin zarafinsu. Wadannan sojoji suna amfani ne da mawuyacin hali na talauci da fatara da mutane ke ciki domin ci da guminsu."

A wannan makon gwamnatin Jamus ta bayyana shirinta na shiga a dama da ita a duk wani matakin kiyaye zaman lafiya da MDD zata dauka a kasar Sudan. Jaridar DER TAGESSPIEGEL ta ba da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Fadar mulki ta Berlin tayi na’am da rokon da MDD ta gabatar mata a game da ba da gudummawar dakarun sojanta a matakin kiyaye zaman lafiyar kudancin Sudan. Amma kuma ta ce yawan sojojin nata ya danganta ne da kudurin da majalisar zata yanke akan wannan manufa, wacce ta shafi sa ido akan aikin yarjejeniyar nan ta zaman lafiya da aka cimma tsakanin gwamnatin Sudan da ‘yan tawayen SPLA a kudancin kasar a cikin watan janairun da ya wuce."

A yayinda gwamnatin shugaba Robert Mugabe ke ci gaba da kwace gonakin farar fata a kasar Zimbabwe tare da fatali da yarjeniyoyin dake tsakaninta da sauran kasashe, dubban daruruwan al’umar kasar na fama da kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsu. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Ita kanta gwamnatin shugaba Mugabe ta hakikance da gaskiyar cewa jama’a na fama da matsalar yunwa tana mai fatali da ikirarin da tayi da farko cewar bata bukatar taimakon abinci saboda damina mai albarka da ta samu. Bayanai daga ma’aikatar jin dadin jama’a ta Zimbabwe sun ce mutane kimanin miliyan daya da rabi ne ke fuskantar matsalar yunwa a kasar."