Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 25.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon ma halin da ake ciki a kasar Togo shi ne ya fi daukar hankalin masharhantan jaridun Jamus akan al'amuran Afurka

A wannan makon duk da kasancewar masharhanta na jaridun Jamus sun fi mayar da hankalinsu ne ga ziyarar yini biyar da shugaba George W. Bush na Amurka ya kawo ga nahiyar Turai tare da ya da zango a nan Jamus, amma fa ba su yi ko oho da al’amuran nahiyar Afurka ba, musamman ma halin da ake ciki a kasar Togo, wacce ke dada fuskantar matsin lamba a cikin gida da ketare domin ta sake maido da aikin daftarin tsarin mulkinta da aka yi wa gyaran fuska domin ba wa dan marigayi shugaba Gnassingbe Eyadema damar ci gaba da mulkin kasar. A lokacin da take ba da rahoto a game da mawuyacin halin da Togo zata iya samun kanta a ciki sakamakon wannan matsin lamba na kasa da kasa, jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Tuni dai gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka ta dakatar da wakilcin kasar Togo sannan ta kakaba wa gwamnati a fadar mulki ta Lome takunkumi. Kuma ko da yake sabon shugaban kasar ta Togo Faure Eyadema ya mika wuya bori ya hau, inda yayi alkawarin shirya zabe a cikin watanni biyu masu zuwa, amma kungiyar Ecowas da ta tarayyar Afurka AU sun yi ko oho da wannan alkawari suka ce lalle sai yayi murabus".

Wani rahoton da aka samu baya-bayan nan sun ce wasu manema labarai na kasashen ketare guda uku sun bi dufun dare suka tsere daga kasar Zimbabwe saboda barazanar tsaresu da aka yi. Dalilin haka kuwa shi ne kyamar da Mugabe ke yi na ganin an sa ido akan zaben kasar. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto jaridar DIE TAGESZEITUNG karawa tayi da cewar:

"Makonni kalilan kafin zaben majalisar dokokin Zimbabwe, shugaba Robert Mugabe ya fara zuga jami’ansa na ‘yan sanda domin farautar manema labarai. A sakamakon haka wasu ‘yan jarida na ketare guda uku suka tsere daga kasar saboda tsoron makomar rayuwarsu. Musabbabin matakin na shugaba Robert Mugabe dai shi ne domin hana gabatar da wani sahihin rahoto a game da zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 31 ga watan maris mai kamawa, da kuma karya alkadarin ‘yan hamayya ko ta halin kaka."

Mutane masu tarin yawa ne ke cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsu a kasar Swaziland dake can kuryar kudancin Afurka, a yayinda sarkin sarakunanta Mswati na III ke sheke ayarsa ba kakkautawa. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

"A yayinda talakawansa ke fama da mawuyacin hali na yunwa sarki Mswati na III ya kashe abin da yaki Euro miliyan daya domin sayen motoci masu alfarma daga nan Jamus, kuma wannan ba shi ne karo na farko ba. A baya ga haka sarkin ya kebe abin da ya kai Euro miliyan goma sha biyu da rara, daga kasafin kudin kasa, domin sabunta gidajen matansa su 12, wadanda kowace daga cikinsu ke da motar nan mai alfarma samfurin BMW, abin da ya bunkasa gibin kasafin kudin kasar da misalin Euro miliyan 100 shekarar da ta wuce. A kokarin cike wannan gibi, daga baya-bayan nan aka wajabta haraji akan kungiyoyin taimakon jinkai da cibiyoyin ilmi na kasar."

Bisa manufar ba wa kasar Nijeriya wata sahihiyar alkiblar da zata taimaka wajen kyautata makomar kasar da ta fi kowace yawan jama’a a nahiyar afurka gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo ta kira taron kasa. Jaridar DIE Tageszeitung tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

"Wakilai kimanin 400 da aka gayyata domin halartar taron dake da nufin ba da shawarwarin garambawul ga manufofin Nijeriya, ba jama’a ne suka zabe su ba, shugaban kasa da gwamnatocin jiha da jam’iyyun siyasa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ne suka nada su, kuma ba wanda ya san tahakikanin abubuwan da ake bukatar ganin sun tattauna kansu da kuma irin sakamakon da taron zai haifar. Manazarta dai sun hakikance cewar duka-duka shawarwari ne zasu bayar kuma ba lalle ba ne gwamnati tayi aiki da su."