Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 18.03.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon har da halin da ake ciki a arewacin kasar Angola mai arzikin damenti

A wannan makon mai karewa ma jaridu da mujallun Jamus ba su yi ko oho da al’amuran Afurka ba, inda suka gabatar da rahotanni iya gwargwado a game da halin da ake ciki a wasu sassa na nahiyar. Misali jaridar DIE TAGESZEITUNG ta leka janhuriyar demokradiyyar Kongo domin duba halin da ake ciki a game da makomar siyasar kasar dake can kuryar tsakiyar Afurka, wadda ta ce ana fama da sabanin ra’ayi tsakanin al’umarta a game da hadin kan kasarsu. Jaridar ta kara da cewar:

"Sabanin da ake fama da shi ya jibanci tsarin mulkin da za a ba wa kasar ta Kongo ne. Domin kuwa a zamanin baya kusan dukkan jam’iyyun siyasar kasar suna goyan bayan wani tsarin mulki na tarayya inda jihohin kasar zasu samu ikon zartaswa iya gwargwado. Amma ba zato ba tsammani majalisar dattawan kasar dake karkashin gwamnatin rikon kwarya ta sa kafa tayi fatali da shawarar da aka zayyana tana mai neman ganin an bi wani tsari na gwamnatin tsakiya. Wannan matakin ya haifar da mummunan rikici na siyasa, wanda kuma ba wanda ya san lokacin da zai zo karshensa."

A can kasar Angola, mai makobtaka da kasar Kongo a arewacinta, wacce ba kasafai ne take shiga kanun labarai ba, mahukuntan ‘yan sandan kasar sun dauki wani mataki na kandagarkin fasakwabrin damenti da ya zaman ruwan dare a wannan kasa, wacce tayi shekaru gommai tana mai fama da yakin basasa. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto jaridar NEUES DEUTSCHLAND cewa tayi:

"Mahukuntan kasar Angola sun shafe watanni 15 suna masu fafutukar mayar da ‘yan kasar Kongo sama da dubu 100 da suka kwarara zuwa cikinta zuwa gida. Duk wanda yayi kurarin sake kutsa kai kasar ta Angola ba za a dauke shi tamkar dan gudun hijira ba. Nan take za a tsare shi a tasa keyarsa zuwa kurkuku. Dalili kuwa shi ne, a baya ga dimbim arzikin damenti da Allah Ya fuwace wa Angolar a wannan yanki, kazalika yana da muhimmanci ta fuskar tsaro. A zamanin yakin basasar kasar, ‘yan tawaye a karkashin jagorancin marigayi Jonas Savimbi, sun mayar da yankin karkashin ikonsu suna masu tafiyar da cinikin damenti domin samun kudaden sayen makamai. Bayan mutuwar Savimbi a shekara ta 2002, ‘yan tawayen kasar Kongo da ‘yan gudun hijira na kasar sun yi kaka-gida a yankin suna masu dogara akan arzikin damentin Angola domin samun kudaden shiga." Kasashen gabacin Afurka sun tsayar da kudurin tura sojojinsu domin rufa wa gwamnatin gudun hijira ta kasar Somaliya baya wajen komawa fadar mulki ta Mogadishu. Amma a can kasar Somaliyar ana fama da adawa mai tsanani game da wannan shawara, musamman saboda hannu da kasar Habasha, babbar abokiyar gabar Somaliya take da shi a matakin. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Kasar Somaliya na fuskantar barazanar sake fadawa cikin wani sabon fada. Domin kuwa kasashen gabacin Afurka na so su yi amfani da karfin hatsi domin mayar da gwamnatin hijirar dake kasar Kenya zuwa fadar mulki ta Mogadishu, a yayinda a can Somaliyar ake dada samun karuwar yawan masu adawa da wannan mataki na katsalandan soja. Adawar ta kara yin tsanani ne bayan da kasar Habasha ta tsayar da shawarar shiga a dama da ita a cikin watan fabarairun da ya wuce. An sha shiga takun-saka tsakanin Somaliya da Habasha, kuma tuni Amurka da wata kungiya ta kasa da kasa dake sa ido akan rikici suka yi gargadin katsalandan soja domin mayar da gwamnatin hijirar zuwa fadar mulki ta Mogadishu."