1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

March 25, 2005

A wannan makon jaridun Jamus sun gabatar da rahotanni masu yawa akan al'amuran Afurka

https://p.dw.com/p/BvpN

A wannan makon dai jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyar Afurka, kama daga gabaci zuwa yammacin nahiyar da kuma halin da nahiyar baki dayanta take ciki yanzu haka. Amma da farko zamu fara ne da jaridar DIE TAGESZEITUNG wacce ta yi bitar halin da aka kasance a ciki a kasar nijer a wannan makon, inda take batu a game da ta da kayar baya da talakawa ‘yan rabbana ka wadata mu suka yi dangane da matakin da gwamnati ta dauka na kara farashin ruwa da wuta, bayan mawuyacin halin da jama’a suka fuskanta na bannatar da amfanin noma da farin dango suka yi da kuma farin da ya lalata filayen noma. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Kasar Nijer dai ita ce ta biyu a tsakanin kasashen da suka fi talauci a duniya, kuma ga alamu al’umarta zasu kara shiga hali na kaka-nika-yi sakamakon wani karin haraji na kashi 19% da gwamnati ta ba da sanarwa kansa baya-bayan nan. Dalilinta kuwa shi ne wai saboda shiga inuwar gamayyar takardun kudin kasashen yammacin Afurka da kasar Nijer tayi, wacce ta tanadi tsarin haraji bai daya tsakanin illahirin kasashenta. Kazalika karin harajin wani sharadi ne daga bakin duniya da asusun ba da lamuni na IMF. Amma matsalar dake akwai shi ne rahotannin kungiyar abinci ta MDD sun ce kimanin kashi daya bisa hudu na al’umar Nijer su miliyan 12 ka iya fuskantar matsalar yunwa a wannan shekarar sakamakon rashin kaka mai albarka da kuma barnar farin dango."

A can kasar Namibiya ga alamu manoma farar fata zasu samu wata ‘yar sararawa sakamakon sabuwar majalisar ministocin da aka nada, wacce ke da sassaucin manufofin siyasa. A lokacin da take ba da wannan rahoto Jaridar DER TAGESSPIEGEL cewa tayi:

"An yi watanni masu yawa manoma farar fatan kasar Namibiya su dubu hudu na cikin halin dardar dangane da barazanar kwace gonakinsu. Dalili kuwa shi ne, ko da yake sabon shugaban kasar da aka yi wa mubaya’a a wannan makon Hifikepunye Pohamba, a wasu ‘yan kwanakin da suka wuce ya ba da sanarwar kwace gonakin akan kudaden diyya masu tsoka, amma ganin matakin da ya dauka na nada wani babban abokin hamayyarsa a mukamin P/M, wanda mutum ne mai sassaucin ra’ayi, manazarta suka hakikance cewar manufar sake rabon filin noman zata dauki wani sabon fasali, mai ma’ana, nan ba da dadewa ba."

Kasashe da dama na Afurka ke fama da tashe-tashen hankula, kuma hasashen da aka yi ya nuna cewar tashintashinar zata dada karuwa sakamakon gwagwarmayar dora hannu akan albarkatun kasa, a cewar Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG, wacce ta ci gaba da cewar:

"Yawa-yawanci akan danganta tashe-tashen hankula a nahiyar Afurka da matsaloli na kabilanci, amma ba a ba da la’akari da daya dalilin dake taka muhimmiyar rawa wajen billar wadannan tashe-tashen hankula. Wannan maganar, musamman ta shafi karancin ruwan da ake fama da shi a wasu sassa na gabacin Afurka da kuma yankin Sahel. Malalar hamada da zaizayar kasa da kafewar koguna duk suna taka muhimmiyar rawa wajen billar tashe-tashen hankula a nahiyar Afurka. Shi kansa kazamin fadan da ake fama da shi a lardin Darfur na kasar sudan yana da nasaba da mummunar gabar da aka dade ana fama da ita tsakanin manoma da makiyaya a wannan yankin da yashi ke dada yaduwa a cikinsa."

Ita kuwa jaridar DIE ZEIT mai fita mako-mako ta bayyana mamakinta ne a game da yadda wani kwarzon namiji kamar Rubert Mugabe, wanda ya taka rawar gani a gwagwarmayar neman ‘yancin kasarsa ya rikide ya koma dan kama-karya tare da danne hakkin al’umar kasarsa. Jaridar ta ce tun bayan da ya da ya karbe madafun iko, haukan mulki ya rutsa da shugaba Mugabe dake da shekaru 81 da haifuwa, inda yayi kane-kane a al’amuran kasarsa tare da daukar matakai iri dabam-dabam na murkushe duk wata manufa ta hamayya da shi ko neman mulkin demokradiyya. Tun abin da ya kama daga shekara ta 2000 al’amuran Zimbabwe ke dada rincabewa, amma ga alamu ba abin dake ci wa shugaban tuwo a kwarya a game da haka.