Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 22.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki dangane da zaben kasar Togo shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon

Daga cikin muhimman batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa har da halin da ake ciki a kasar Togo dangane da shirye-shiryen zaben shugaban kasar, inda jaridar LE MOND DIPLOMATIQUE, reshen Jamus, a cikin wani dogon sharhin da ta gabatar take cewa:

"Da yawa daga manazarta al’amuran yau da kullum sun kalubalanci matakin juyin mulki a fakaice da shuagabannin Togo suka dauka domin ba wa dan marigayi Gnassingbe Eyadema damar ci gaba da mulkar kasar tamkar wani mummunan koma baya ga ci gaban da nahiyar Afurka take samu akan hanyar mulkin demokradiyya. Sai fa da shugaban kungiyar tarayyar Afurka Olusegun Obasanjo yayi barazanar katsalandan soja ne Faure Gnassingbe ya nuna halin sanin ya kamata yana mai alkawarin biyayya ga daftarin tsarin mulkin kasar ta Togo na gabatar da zabe a cikin kwanaki sittin."

Ita kuwa jaridar DIE TAGESZEITUNG ta duba halin da ake ciki ne a game da yakin neman zaben kasar ta yammacin Afurka, inda take cewar tashe-tashen hankula sune suka dabaibaye yanayin yakin neman zaben kasar Togo yanzu haka: Jaridar sai ta kara da cewar:

"Tun daga iyakar kasar Togo mutum zai iya lura da hali na dardar da ake ciki dangane da zaben shugaban wannan kasa ta yammacin Afurka. Amma a daya hannun kuma mutum zai yi zaton cewar dan takara daya kwal ne zai tsaya takarar zaben. Domin kuwa hatta ofishin ‘yan kwasta da jami’an tsaron iyaka duk an dabaibaye shi da hotunan Faure Gnassingbe dan marigayi Gnassingbe Eyadema. ‘Yan hamayya na zargin cewar jam’iyyar gwamnatin na samun rufa baya daga dakarun soja domin tsoratar da jama’a, musamman magoya bayan ‘yan hamayyar. To sai dai kuma duk da haka ‘yan hamayyar na da kwarin guiwar cimma nasarar zaben."

A wannan makon kasar Zimbabwe ta samu shekaru 25 ga ‘yancin kanta. Jaridar GENERAL ANZEIGER ta nan birnin Bonn ta bayyana takaicinta a game da alkiblar da kasar ta fuskanta a cikin wadannan shekaru 25, inda bayan kakkabe ta daga kurar mulkin mallaka, shugabanta Robert Mugabe ya rikide zuwa dan mulkin danniya da kama karya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"A hakika tun tafiya ba ta je nesa ba aka fara hangen alkiblar da shugaba Mugabe ya fuskanta, misali kisan kiyashin da aka yi wa magoya bayan babban abokin hamayyarsa Joshua Nkomo a lardin Mutabeleland a cikin shekarun 1980, amma duniya ta yi watsi da lamarin sakamakon mayar da hankalin da aka yi akan danyyen mulkin nan na wariya da kabilanci a Afurka ta Kudu. Shugaban na kasar zimbabwe ya ci gaba mulkinsa na danniya da neman murkushe ‘yan hamayya. Kuma ainifin dalilin da ya sanya ya kirkiro manufofinsa na sake rabon filin noma, shi ne, imanin da yayi na cewar farar fata ne ke tallafa wa abokan hamayyarsa da kudi. A sakamakon haka ya shiga kwace gonakinsu, matakin da ya taimaka wajen tabarbarewar al’amuran kasar ta Zimbabwe kwata-kwata."

Daya daga cikin matsalolin dake addabar Nijeriya shi ne game da ‘yan fasakwabrin mai, wanda aka kiyasce cewar su kan sace abin da ya kai kashi 10% na yawan mai da Nijeriya ke hakowa a shekara, musamman ma idan aka yi la’akari da cewar a shekarar da ta wuce Nijeriya ta hako mai da yawansa ya kama kwatankwacin Euro miliyan dubu 23. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto Jaridar DER TAGESSPIEGEL karawa tayi da cewar:

"Wannan matsalar ta dade tana addabar Nijeriya, amma mahukuntan kasar suka yi ko oho da ita, mai yiwuwa saboda wasu daga cikin magabatan kasar na cin gajiyar lamarin, amma a yanzun an tashi haikan domin karya alkadarin masu fasa-kwabrin, inda a baya-bayan nan aka cafke mutum 200 aka kuma kwace abin da ya kai dalar Amurka miliyan 700 daga hannunsu."