1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

April 29, 2005

Halin da ake ciki a kasar Togo shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/BvpJ
Tashe-tashen hankula a Togo
Tashe-tashen hankula a TogoHoto: AP

Babban abin day a fi daukar hankalin masharhanta na illahirin jaridun Jamus a wannan makon shi ne halin da ake ciki a kasar Togo bayan gabatar da sakamakon zaben kasar da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce. A cikin nata sharhin jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

“Bisa ga dukkan alamu shirin zaman lafiyar da gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka ta tsara ga kasar Togo ya ci tura tun kafin a aiwatar da shi. A karkashin wannan tsari, kamar yadda sanarwa ta nunar bayan ganawar da aka yi tsakanin ‘yan takarar zaben shugaban kasar ta Togo da shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo, jim kadan bayan kamala zaben, shi ne kafa wata gwamnati ta hadin kan kasa. Amma ba zato ba tsammani sai aka ji shugaban ‘yan hamayya Gilchrist Olympio, dan marigayi Sylvanus Olympio, wanda Eyadema ya kifar da mulkinsa a farkon shekarun 1960 yana mai bayyana kin amincewarsa da sakamakon zaben, lamarin day a haddasa tashe-tashen hankulan da yayi sanadiyyar rayukan mutane da dama a kasar ta yammacin Afurka.”

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a cikin nata sharhin cewa tayi:

“Kasar Togo da shiyyar yammacin Afurka baki daya na fuskantar barazanar tsunduma cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Ana amfani da dukkan mataki na rashin imani a gwagwarmayar kama madafun iko a wannan kasa, tun kuwa abin day a kama daga sojoji da dakarun sa kai da magoya bayan gwamnati da na bangaren ‘yan adawa dukkansu ana amfani da bindigogi da gurnati da adda da gatari a tashin-tashinar da ta biyo bayan zaben kasar da aka gudanar ranar lahadi da ta wuce. Amma fa ummal’aba’isin tabarbarewar rikicin shi ne Faure Gnassingbe, wanda y adage akan lalle sai ya gaji karagar mulkin kasar ta yammacin Afurka, tun bayan rasuwar mahaifinsa a cikin watan fabarairun day a wuce.”

A daura da mawuyacin halin da aka shiga a kasar Togo, an samu kyakkyawan ci gaba a kokarin da ake yin a shawo kan rikicin day a ki ci ya ki cinyewa a daya kasar ta yammacin Afurka, wato Cote d’Ivoire, kamar yadda jaridar frankfurter Rundschau ta rawaito inda ta kara da cewar:

“Shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo ya kawar da babban abin dake hana ruwa gudu wajen cimma zaman lafiyar kasar, inda ya amince, shugaban ‘yan hamayya Alassane Ouattara ya tsaya takarar zaben da za a gudanar nan gaba a wannan shekara. An yi shekaru da dama shuagabannin kasar Cote d’Ivoire na daukar matakai iri-iri domin hana tsofon P/M kasar shiga zaben shugaban kasa, wai saboda iyayensa sun fito ne daga makobciyar kasa ta Burkina Faso. Da wannan mataki shugaba Gbagbo ya bad a kai bori ya hau ga daya daga cikin sharuddan da ‘yan tawayen dake da ikon arewacin kasar suka shimfida. Daya matsalar da ta rage it ace ta kwance damarar makaman dakarun sa kai daga dukkan sassan dab a sag a maciji da juna a rikicin kasar Cote d’Ivoire, kamar yadda aka cimma daidaituwa a shawarwarin sulhu a Pretoria.”