1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 10, 2005

Mawuyacin hali na zanga-zangar dalibai a kasar Habasha na daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afurka

https://p.dw.com/p/BvpD
Tashe-tashen hankula a Addis Ababa
Tashe-tashen hankula a Addis AbabaHoto: AP

A wannan makon duk da ci gaba da ake yi da kai ruwa rana dangane da yiwuwar gudanar da sabon zaben majalisar dokokin Jamus nan gaba a wannan shekarar, amma jaridu da mujallun kasar ba su yi watsi da al’amuran Afurka ba, inda suka ci gaba da bin diddigin halin da ake ciki a sassa dabam-dabam na wannan nahiya. Misali jaridar Frankfurter Rundschau ta leka kasar Habasha inda a wannan makon jami’an tsaro suka bude wuta suna masu harbin kai mai uwa da wabi a tsakanin dalibai dake zanga-zangar adawa da yanayin zaben da aka gudanar a kasar kwanan baya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“Akalla mutane 22 suka yi asarar rayukansu sakamakon arangama tsakanin dalibai da jami’an tsaron kasar Habasha, lokacin da daliban suka barbazu akan titunan birnin Addis Ababa domin zanga-zangar bayyana rashin gamsuwarsu da yanayin zaben da aka gudanar a kasar a watan mayun da ya wuce. A nasu bangaren ‘yan tireda da direbobin tasi sun shiga yajin aiki domin nuna goyan bayansu ga daliban, wadanda da yawa daga cikinsu suka ji mummunan rauni. Gwamnati dai bata yi wata-wata ba wajen dakatar da aikin wasu ‘yan jarida guda bakwai biyu daga cikinsu wakilan DW ne dake aiko wa sashen harshen Amharic da rahotanni daga kasar Habasha, sai kuma wasu wakilan gidan rediyon muryar Amurka, bisa zarginsu da nuna son kai a rahotannin da suke bayarwa.”

Bisa ga dukkan alamu murna ta koma ciki dangane da yajin aikin da aka shirya gudanarwa a kasar Zimbabwe domin nuna adawa da matakan cin zarafin talakawan kasar ‘yan rabbana ka wadata mu da ‘yan sanda da jami’an tsaro ke yi bayan rushe gidajen mutane kimanin dubu 200 da gwamnati ta yi a karkashin matakin da ta kira wai na tsabtace birnin Harare, a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda ta kara da cewar:

“A daidai lokacin da mutane ke cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsu sakamakon matakai na danniya da muzantawa da cin zarafi daga bangaren jami’an tsaro, a jiya alhamis shugaba Robert Mugabe ya gabatar da bikin bude zaman farko na sabuwar majalisar dokokin kasar Zimbabwe. Shugaban mai shekaru 81 da haifuwa na fatan yi wa daftarin tsarin mulkin Zimbabwe gyaran fuska domin kara tabbatar da angizonsa akan karagar mulkin wannan kasa. A karkashin matakin da gwamnatin Mugabe ta dauka a ‘yan kwanakin da suka wuce an fatattaki ‘yan tireda dake baje teburansu a bakin titunan Harare da na sauran biranen kasar tare da rushe dukkan gidaje da bukkokin da talakawa ‘yan rabbana ka wadata mu suka kafa a ire-iren yankunan nan na share wuri zauna. Kimanin mutane 200 000 suka tagayyara sakamakon wannan mataki na tsaftace biranen Zimbabwe.”

A wannan makon shugaba Bush na Amurka ya bayyana goyan bayansa ga shirin nan na taimakon Afurka da P/M Birtaniya Tony Blair ya gabatar. Bisa ga ra’ayin jaridar Süddeutsche Zeitung, wannan ba kome ba ne illa wani yunkuri na daga martabar shugaban Amurkan a idanun duniya ba tare da ya taka wata muhimmiyar rawa a manufofin raya kasashe masu tasowa ba. Jaridar sai ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“Ba shakka P/M Birtaniya Tony Blair ya cancanci yabo a game da kokarin da yake na kyautata makomar nahiyar Afurka. Amma fa ba zai iya cimma wannan buri ba sai tare da taimakon kasar Amurka, wacce duk wanda ya bi diddigin manufofinta na ketare zai ga ba da damu da makomar wannan nahiya ba. Babban abin da Amurka ke ba wa fifiko shi ne yankin gabas ta tsakiya da nahiyar Asiya. Shi kansa goyan bayan da Bush ya nuna wa Blair ba kome ba ne illa wata dabara ta neman daga martabarsa a idanun duniya, saboda ainifin kudaden da yake batu kansu tuntuni aka tanadar da su a matakan kasar Amurka na taimakon raya kasashe masu tasowa, duka-duka abin da ya rage shi ne a shigar da su a kasafin kudin Amurka dangane da kasashen Afurka.”