Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 01.07.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon ma jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama dangane da nahiyar Afurka, musamman ma halin da ake ciki a kasar Kongo

Rushe gidajen talakawa a kasar zimbabwe

Rushe gidajen talakawa a kasar zimbabwe

A wannan makon jaridun na Jamus sun yi bitar matsaloli dabam-dabam dake addabar kasashen Afurka, kama daga yammaci zuwa gabaci da kuma arewaci zuwa kudancin nahiyar. Amma da farko zamu duba sharhin da jaridar Der Tagesspiegel ta rubuta ne a game da kokarin da P/M Birtaniya Tony Blair ke yi na ganin an yafe wa kasashen Afurka dimbim bashin dake kanta, inda jaridar ta ce ba Birtaniya ce kadai ta damu da makomar Afurka ba, dukkan kasashen G8 dake da ci gaban masana’antu sun damu matuka a game da makomar nahiyar, inda suka fara ba da la’akari da ita a lokutan taron kolinsu tun abin da ya kama daga shekara ta 2002. Jaridar sai ta ci gaba da nuna irin rawar da Jamus ta dade tana takawa wajen farfado da al’amuran Afurka, inda take cewar:

“Jamus ta dade tana ba da goyan baya ga kasashen Afurka dake dora manufofinsu kan nagartaccen tsari na demokradiyya. Kazalika kasar na ba da cikakken goyan-baya wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma tallafa wa cibiyoyin ba da horo ga dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Afurka. A takaice kasar ta gabatar da taimakon da ya kai na Euro miliyan daya da dubu dari shida ga kasashen na Afurka tun daga shekara ta 2003 zuwa halin da muke ciki yanzun.”

A jiya alhamis ne wa’adin mulkin wucin gadi na shugaba Joseph Kabila ya kawo karshensa a janhuriyar demokradiyyar Kongo, amma duk da haka shugaban bai kakkabe hannuwansa daga al’amuran mulki ba, a sakamakon haka manazarta ke sa ramn fuskantar mummunar zanga-zanga da zub da jini a fadar mulki ta Kinshasa a cewar jaridar Frankfurter Rundschau, wadda ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“Tun watanni da dama da suka wuce ne al’umar kasar Kongo suka dokata a game da zaben kasar da aka shirya gudanarwa a kasar domin nada wata sabuwar gwamnati da zata maye ta wucin gadi dake ci karkashin shugaba Joseph Kabila. Da dai a jiya alhamis ne wa’adin mulkinsa zai kare, amma majalisar dokoki ta kara wa’adin har ya zuwa karshen shekara, wai saboda tafiyar hawainiyar da hukumar zabe ta kasa ke fuskanta a shirye-shiryen zaben a duk fadin kasar ta Kongo. To ko Ya-Allah al’umar kasar dake dokin ganin an samu canji saboda kyautata makomar rayuwarsu zasu hakura da hakan? lamarin dai da walakin.”

A cikin wani sabon ci gaba kuma kasar Sudan ta fara sakin fursinonin siyasar da ta tsare tare da dage dokar ko-ta-kwana ta soja dake ci a duk fadin kasar tsawon shekaru da dama da suka wuce. A lokacin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ke ba da wannan rahoton cewa tayi:

“Daga cikin fursinonin siyasar da aka sake har da Hassan Atturabi. To sai dai kuma a daya hannun fadar mulki ta Khartoum tayi fatali da maganar mika masu miyagun laifuka na ci zarafin dan-Adam a lardin Darfur domin fuskantar shari’a a kotun kasa da kasa. Bugu da kari kuma dokar ko-ta-kwanan tana ci a lardin na Darfur dake fama da rikici.”

A kasar Zimbabwe, kamar yadda jaridar Die Zeit ta rawaito, a ‘yan kwanakin baya-bayan nan mutane sun daina tambayar lafiyar jiki a gaishe-gaishensu, sai dai su tambaya ko shin gidanka na nan tsaye. Domin kuwa a halin yanzu haka mutane kimanin dubu 300 aka fatattakesu daga gidajen su aka kuma rushesu nan take. Wannan dai wani bala’i ne irin shigen na tsunami ke neman rutsawa da al’umar Zimbabwe, in ji jaridar ta Die Zeit.

Wani rahoto mai nasaba da asusun taimakon yara na MDD UNICEF a takaice ya ce kimanin kashi daya bisa biyar na yaran da akan haifa a nahiyar Afurka ke asarar rayukansu sakamakon cutar Aids, wacce radadinta ke neman zarce na zazzabin cizon sauro a wannan nahiya. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto, jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi:

“Alkaluma sun nuna cewar kimanin yara miliyan hudu da dubu dari bakwai ne ke mutuwa a nahiyar Afurka a duk shekara, wanda ya kama kusan kashi 50% na illahirin yaran da kan yi asarar rayukansu a duk fadin duniya, alhali kuwa duka-duka yawan al’umar wannan nahiya bai zarce kashi 12% na al’umar duniya ba. Cutar Aids dai ita ce ke da alhakin kashi 30% na wannan mace-mace a nahiyar Afurka yanzu haka.”