1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

August 26, 2005

Ziyarar Kofi Annan ga kasar Nijer na daya daga cikin abubuwan da masharhantan jaridun Jamus suka mayar da hankali kansa

https://p.dw.com/p/Bvp4
Kofi Annan a Nijer
Kofi Annan a NijerHoto: AP

Daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka har da halin da ake ciki a kasar Nijer dangane da ziyarar da sakatare-janar na MDD Kofi annan ya kai ga kasar a wannan mako. A lokacin da take gabatar da rahoto akan ziyarar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

“A ziyararsa ga Nijer, sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya bayyana cewar manufar majalisar ce ta ga taimakonta ya kai ga dukkan masu fama da matsalar yunwa a fadin kasar. Amma fa a daya hannun MDD na fuskantar suka da kakkausan harshe daga kungiyoyin taimako masu zaman kansu, wadanda, bisa ga ra’ayinsu, majalisar tayi wa matsalar rikon sakainar kashi.”

Ita kuwa jaridar DIE WELT sharhi tayi a game da matsalar yunwar a Nijer tana mai cewar:

“An saurara daga kakakin kungiyar taimakon abinci ta Jamus, a lokacin da aka samu rahoton matsalar yunwa a daidai ranar 11 ga watan agusta, tana mai cewar wannan ba shi ne karo na farko ba da majalisar dinkin duniya ta gaza wajen gabatar da taimako ga mabukata. Irin wannan gazawa ma abu ne da tuni ya zama ruwan dare. Amma fa idan an yi ta barawo sai kuma a yi ta mabi sau. Domin kuwa ita kanta gwamnatin Nijer ce ke da alhakin lamarin, inda ta fito tana mai ikirarin cewar kasar bata da wata matsala ta yunwa illa kawai dan karancin abincin da bai taka kara ya karya ba.

A yau juma’a ne ake wa sabon shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunzia mubaya’a, wanda shi ne na farko da aka nada ta hanyar zabe tun shekaru da dama da suka wuce. To sai dai kuma a daya hannun manazarta na fargabar cewar mai yiwuwa a yanzun a yi watsi da makomar kasar dake can kuryar tsakiyar Afurka a cewar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU, wadda kuma ta ci gaba tana mai cewar:

“Daya daga cikin kalubalar da sabon shigaban zai fuskanta shi ne komawar kusan ‘yan kasar Burundi miliyan daya dake zaman hijira a ketare da kuma sajewar tsaffin dakarun ‘yan tawaye domin cude-ni-in-cude-ka da sauran farar fula ka iya kara tsawwala matsalolin kasar dake fama da tabarbarewar tattalin arziki. Amma babban abin da ake tsoro shi ne ka da duniya ta sake yin watsi da makomar kasar ta Burundi ganin cewar kome ya tafi salin-alin ba tare da wata tangarda ba, a fafutukar sake dorata kan tsarin mulki na demokradiyya.”

A sakamakon matsaloli na karancin makamashi da kayan abinci da take fuskanta kasar Zimbabwe ta tinkari kasar Afurka ta Kudu da kokon bara tana mai neman rancen kudi. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar DER TAGESSPIEGEL cewa tayi:

“Manazarta sun hakikance cewar wannan matakin farko ne na tabarbarewar tattalin arzikin kasar zimbabwe, wacce a zamani baya ta kasance abar koyi ga sauran kasashen Afurka. Amma tun abin da ya kama daga kusan shekaru biyar da suka wuce, al’amuran kasar suka canza suka dauki wani sabon salo, inda shugaba Mugabe da Mukarrabansa suka kai ta suka baro. Bayan rashin nasarar kokon bararsa da ya mika ga kasar China, a yanzu shugaba Mugabe na fatan samun taimako daga ATK ko Ya-Allah zata iya ceto kasar ta Zimbabwe daga mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki.”

A cikin wani sabon ci gaba kuma gwamnatin Jamus na kokarin tatse kasar Kongo, inda take neman kasar da ta biya wasu kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 70 sakamakon rashin nasarar jarin da wani kamfanin Jamus ya zuba a harkar hakan ma’adinai a kasar wacce yakin basasa yayi kaca-kaca da ita. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ce ta rawaito wannan rahoton inda ta kara da cewar:

”Wani abin lura a nan shi ne a cikin watan oktoban bara ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieszorek-Zeul ta ba da sanawar sake kama hada-hadar taimakon raya kasa da kasar Kongo tare da ware mata tsaabar kudaden taimako na Euro miliyan 60. Amma tun tafiya bata je nesa ba, a cikin watan janairun da ya wuce sai ga shi gwamnati a nan kasar ta Jamus ta nema daga kafar kudi ta Hermes da ta daukaka kara kan kasar Kongo domin a dawo mata da kudadenta na dala miliyan 70, alhali kuwa dukkan rijiyoyin hakan ma’adinan dake Katanga ba sa aiki.”