1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 2, 2005

Halin da ake ciki a Cote d'Ivoire na daga cikinbatutuwan da Jaridun Jamus suka duba a wannan makon

https://p.dw.com/p/Bvp3
shawarwarin sulhun Cote d'Ivoire
shawarwarin sulhun Cote d'IvoireHoto: AP

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da halin dake ciki a kasar Cote d’Ivoire dangane da fatali da ‘yan tawaye suka yi da kokarin da shugaban ATK Thabo Mbeki yake yi na sa baki domin sasanta rikicin kasar ta yammacin Afurka da ya ki ci ya ki cinyewa. A lokacin da take bayani game da haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

“Bisa ga dukkan alamu kome ya tsaya cik dangane da kokarin kawo karshen yakin basasar kasar Cote d’Ivoire. Domin kuwa bayan kokarin da aka sha famar yi domin janyo hankalin sassan da ba sa ga maciji da juna domin zama kan teburin shawarwarin sulhu, a yanzun kokarin baya-bayan nan da shugaba Thabo Mbeki domin sasanta rikicin ya ci tura. A sakamakon haka da wuya a gudanar da zaben da aka shirya a kasar a wajejen karshen watan oktoba mai zuwa, ballantana a yi batu a game da shawarar Mbeki game da kwance damarar makaman ‘yan tawaye da dakarun sa kai dake goyan bayan gwamnati a daya bangaren.

Ita ma jaridar DIE WELT ta gabatar da rahoto a game da karantsayen da ake fama da shi dangane da sasanta rikicin kasar ta Cote d’Ivoire, tana mai dora laifin akan ‘yan tawaye. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“’Yan tawaye a kasar Cote d’Ivoire sun ce faufau ba zasu yarda shugaban ATK Thabo Mbeki ya ci gaba da kokarinsa na shiga tsakani domin sasanta rikicin kasar ba. Dalilin da suka bayar game da haka shi ne fifiko da suka ce kasar ATK na ba wa gwamnati, sannan a daya bangaren kuma tana sayarwa da gwamnatin makamai a asurce.”

Gwamnatin hadin guiwa ta kasar Kenya na fuskantar barazanar rushewa sakamakon wani sabon daftarin tsarin mulkin da aka zayyana wanda ke adawa da wata jam’iyyar siyasar kasar mai matsakaicin ra’ayin demokradiyya LDP a takaice. Dangane da haka shugaba Mwai Kibaki ke neman goyan baya daga al’umar kasa ta hanyar kuri’ar rabna gardama akan sabon daftarin tsarin mulkin, in ji jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU, wadda ta kara da cewar:

“Da wuya shugaba Kibaki ya samu goyan baya ganin cewar masu adawa da sabon daftarin tsarin mulkin suna da yawan gaske. Tun a cikin watan yulin da ya gabata dubban dalibai suka shiga zanga-zanga a titunan Nairobi domin bayyana adawarsu da daftarin tsarin mulkin da aka zayyana. A kuma halin da ake ciki wasu wakilan majalisar ministocin Kenya su biyar, dukkansu ‘ya’yan jam’iyyar LDP, sun fito fili suna masu bayyana shirinsu na hadin guiwa da tsofuwar abokiyar gabarta jam’iyyar adawa ta Kanu, wacce ta mulki Kenya tun daga bayan samun’yancin kanta daga 1963 zuwa shekara ta 2002. Shi kuwa Kibaki tun a yakinsa na neman zabe ne yayi alkawarin aiwatar da canje-canje ga daftarin tsarin mulkin domin kayyade cikakken ikon da shugaban kasa ke da shi”

Gwamnatin shugaba Robert Mugabe a kasar Zimbabwe na ci gaba da kayyade ‘yancin al’umar kasar. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi bitar lamarin tana mai cewar:

“Kimanin kashi biyu bisa uku na wakilan majalisar dokokin kasar Zimbabwe suka ba da goyan baya ga sabon daftarin tsarin mulkin da gwamnatin shugaba Mugabe ta gabatar, wanda ya kunshi tsauraran canje-canjen da kasar bata taba ganin irin shigensa tun bayan samun mulkin kanta a 1980 domin kayyade ‘yancin jama’a da kuma share hanyar kwatar filayen noma daga hannun mutane ba tar da wata wahala ba. A baya ga haka a karkashin sabon daftarin tsarin mulkin za a kirkiro wata sabuwar majalisa ta dattawa, wadda wasu daga cikin wakilanta, shugaban kasa ne kadai ke da ikon nada su.”

A makon da ya gabata kasar Burundi ta samu sabon shugaba dan kabilar Hutu Pierre Nkurunziza. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta gabatar da sharhi tana mai cewar:

“Shugaba Nkurunziza, ko da yake dan kabilar Hutu ne, amma yana bin wata manufa ce ta neman kusantar juna da dinke dukkan barakar da ta haddasa yakin babasar da ya halaka mutane sama da dubu 300 a kasar Burundi. A sakamakon haka ya bude kofar jam’iyyarsa ga ‘yan Tutsi. Sai kuma yana da jan aiki a gabansa domin kuwa kimanin kashi 90% na al’umar burundi suna zaune ne hannu baka hannu kwarya sannan kuma yakin basasarta ya haddasa mummunan tabo, a baya ga wata kungiya ta ‘yan Hutun da ake ci gaba da fafatawa da ita, saboda ta ce faufau ba zata amince da manufar sulhu da cude-ni-in-cude-ka tsakannin illahirin al’umar kasar ba.”