Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a Liberiya na daya daga cikin batutuwan Afurka da jaridun Jamus suka yi sharhi akai

Babu wani ci gaba a game da kawo karshen rikicin Darfur

Babu wani ci gaba a game da kawo karshen rikicin Darfur

A wannan makon jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyar Afurka, tun abin da ya kama daga yammaci zuwa gabaci da kuma kudancin Afurka. Amma da farko zamu fara ne da rahoton jaridar GENERAL ANZEIGER ta birnin Bonn, wadda take cewar babu wani ci gaban da ake samu na a zo a gani a rikicin da ake fama da shi a lardin Darfur na kasar Sudan..Jaridar ta ce:

“A sakamakon matsalolin da ake fama da su a wasu sassa na Afurka, kamar dai matsalar nan ta yunwa da ta rutsa da kasar Nijer, an yi watsi da mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur. Babu wata alamar dake nuna samun ci gaba wajen shawo kan rikicin tsakanin ‘yan tawaye da gwamnati a fadar mulki ta Khartoum. Kimanin mutane dubu 300 suka halaka sannan wasu sama da miliyan biyu kuma suka kama hanyar hijira sakamakon ta’asar ‘yan janjawid dake samun goyan baya daga gwamnati.”

A can kasar Namibiya, a asurce, gwamnati ta fara kwace filayen noma daga hannun farar fata, amma akan diyya, ba kamar yadda lamarin ya kasance dangane da kasar Zimbabwe ba. To sai dai kuma duk da haka lamarin ya jefa manoma farar fata cikin hali na kaka-nika yi kamar yadda jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

“A matakin farko da gwamnatin Namibiya ta dauka a asurce, ta kwace filin noma na wata mata mai suna Hilde Wiese dake da shekaru 69 da haifuwa akan kudi kwatankwacin Euro dubu 470 a matsayin diyya ga filinta na noma mai fadin eka dubu hudu da shida. To sai dai farawar da aka yi da karbe gonar Hilde Wiese, ‘yar usulun Jamus, yana da dalilai da dama. Daya daga cikin dalilan haka shi ne korar wasu ma’aikatanta bakar fata guda shida da tayi, lamarin da ya harzuka kungiyar kodago, shi kuma tsofon shugaba Sam Nujoma ya kwatanta shi tamkar wani mummunan laifi.”

Ita ma jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi bitar matakin na kwace filayen noma daga hannun manyan manoma farar fatar Namibiya, inda take cewar:

“Tuni wasu manyan manoma 17 na kasar Namibiya suka samu sanarwar shirin gwamnati na kwace gonakinsu. Gaba daya dai gwamnatin Namibiya na fatan kwace gonaki 200 ne a cikin shekaru biyar masu zuwa. Kuma ko da yake matakin na kasar Namibiya ya banbanta da na makobciyarta Zimbabwe amma har yau ba a tantance sharuddan kwace gonakin ba. Domin kuwa da farko gwamnati cewa tayi matakin zai shafi manoma ne dake da filayen noma daga biyu zuwa sama ko kuma suke zaune a ketare. Amma wadannan sharudda guda biyu ba su shafi Hilde Wiese ba, ‘yar shekaru 69 da aka kwace gonarta, wanda kuma a sakamakon haka ma’aikatanta 24 zasu yi asarar guraben aikinsu.”

A cikin watan oktoba mai zuwa ne aka shirya gudanar da zaben shugaban kasar Liberiya, bayan shekaru 14 na yakin basasar da ya halaka mutane sama da dubu 150. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta duba halin da ake ciki a kasar ta yammacin Afurka inda take cewar:

“Daga daga cikin ‘yan takarar zaben su 22 shi ne shahararren dan wasan kwallon kafar nan mai suna George Weah, wanda babban burinsa shi ne ya sake hade kan kasar da sabunta al’amuranta na ilimi da kiwon lafiya da tabbatar da doka da oda karkashin wani sahihin tsari na demokradiyya da kuma farfado da hanyoyinta na sadarwa, wadanda yaki yayi kaca-kaca da ita.”

Wadannan ba shakka manufofi ne kyawawa, in ji jaridar ta FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG, amma fa sai tare da taimako daga Indallahi ne zai iya tafiyar da su. Domin kuwa ko da yake kasar Liberiyar na karkashin kulawar sojan kiyaye zaman lafiya na MDD su dubu 15, kuma Taylor na zaman hijira a Nijeriya a yayinda aka kwance damarar makaman sojoji ‘yan yara kanana masu tarin yawa, amma kasar bata da cikakkiyar kwanciyar hankali. Kuma da yawa daga ‘yan takarar su 22 suna karbar albashinsu ne daga Taylor, a kokarinsa na neman dawowa kan karagar mulkin kasar.

A sakamakon hauhawar farashin mai da ake fuskanta yanzu haka duniya ta fara karkata ga wasu kasashen Afurka, wadanda aka hakikance cewar Allah Madaukakin sarki Ya fuwace musu albarkar mai. Daya daga cikin kasashen kuwa ita ce Angola, wadda ke biye wa Nijeriya wajen cinikin mai tsakanin kasashen Afurka. To sai dai kuma a inda take kasa tana dabo shi ne, wani salo na cinikin mai da gwamnatin Angola ke tu’ammali da shi, inda take amfani da man domin biyan basussukan da ta karba. A lokacin da take wannan bayani jaridar DER TAGESSPIEGEL cewa tayi:

“Tare da wannan dubarar gwamnatin Angola ta karbi basussukan da yawansu ya kai dala miliyan dubu takwas tun daga 1995. Amma matsalar dake akwai ita ce kasancewar ta haka shuagabannin kasar ke da ikon arzuta kansu da kansu, saboda kudaden balalle ba ne su kwarara zuwa baitul-malin gwamnati, kamar yadda wani nazari ya nunar, inda aka ce tsabar kudi na dalar amurka miliyan dubu hudu suka sulale, ba wanda ya san makomarsu tsakanin 1997 zuwa shekara ta 2002.