Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Daga cikin batutuwan Afurka da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus har da barazanar billar sabon yakin basasa a kasar Kongo

Duk dai da hada-hadar da ake yi a game da zaben majalisar dokoki ta Bundestag da za a gudanar a jibi lahadi idan Allah Ya kai mu, jaridu da mujallun Jamus ba su yi ko oho da al’amuran dake wakana a nahiyarmu ta Afurka ba. Daga cikin batutuwan da suka yi sharhi akansu kuwa har da halin da ake ciki a kasashe kamar Sudan, Kongo, Cote d’Ivoire da ragowarsu. Amma zamu fara ne da wani dogon sharhin da jaridar DIE ZEIT mai fita mako-mako ta rubuta a game da wasu abubuwan da take ganin suna taimakawa wajen hana ruwa gudu a kokarin da ake yi na magance matsalar talauci da raya makomar kasashen Afurka. Jaridar dai ci gaba tayi da cewar:

“Nahiyar Afurka dai har yau ‘yar rakiya ce a manufofin da MDD ke fatan cin musu na magance matsalar talauci da kyautata al’amuran ilimi da kiwon lafiya ga kowa da kowa a kasashe masu tasowa. Domin cimma wannan burin ana bukatar taimakon kudi matuka da aniya. To amma abin tambaya a nan shi ne mene ne makomar kudaden taimako sama da miliyan dubu har sau dubu da suka rika kwarara zuwa nahiyar Afurka tun bayan da kasashen nahiyar suka samu mulkin kansu? Akwai dai wasu daga cikin gaggan ‘yan boko a wannan nahiya dake da imanin cewar musabbabin koma bayan da kasashen Afurka ke fama da shi, shi ne akidar camfi dake tattare a zukatan da yawa daga al’umar wadannan kasashe. Amma fa, kamar yadda jaridar ta DIE ZEIT ta nunar, idan an yi ta barawo sai a yi ta mabi sau, domin kuwa in ka kebe wasu daidaikun ‘yan kama karya da aka yi a kasashen Afurka, daga cikin abubuwan da suka hana samun wani ci gaba na a zo a gani a Afurkan har da manufofin bankin duniya da asusun ba da lamuni na IMF da rashin adalci a dangantakar ciniki ta kasa da kasa da kuma ire-iren sabon salon nan na mulkin mallaka. Dukkan wadannan abubuwa sune ummal’aba’isin koma baya a nahiyar Afurka.”

Al’amura sai dada tabarbarewa suke yi a kasar Cote d’Ivoire, inda ‘yan hamayya ke zargin shugaba Laurent Gbagbo game da kokarin mayar da kamfanonin tsaro masu zaman kansu a kasar karkashin ikonsa. Manufarsa game da haka kuwa shi ne kirkiro wata rundunar kwantar da tarzoma mai masa biyayyya sau da kafa. A lokacin da take rawaito wannan rahoton jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“A cikin watan yunin da ya wuce ne ‘yan hamayya ke bakin kokarinsu wajen wayar da shugaban kasar ATK Thabo Mbeki dake shiga tsakani don sasantawa, a game da dabarar shugaba Laurent Gbagbo. In kuwa har ikirarin nasu ya tabbata gaskiya ke nan za a wayi gari shugaban na Cote d’Ivoire na da dakaru sama da dubu 35 karkashin ikonsa, sannan a daya bangaren kuma baki ‘yan usulin Faransa da Lebanon zasu shiga hali na rudami da rashin sanin tabbas in har Gbagbo ya fara amfani da wadannan kamfanonin tsaro masu zaman kansu.”

Ana fama da karancin mai domin jigilar kayan taimako a kasar Sudan yanzu haka. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

“A daidai lokacin da wakilai ke tattaunawa a taron MDD don yaki da talauci a can birnin New York, kungiyar taimakon abinci ta majalisar na fama da hali na kaka-nika-yi a nahiyar Afurka. Kasashe masu ba da taimako sun fara yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi musu don ba da taimakon kudi, lamarin da ya haddasa karancin mai da ake bukata wajen jigilar abinci. Wannan maganar ta sako-sako da matakan taimako ta hada har da kasar Nijer, inda kananan yara ke fama da karancin abinci mai gina jiki duk da hada-hadar taimakon da jami’an MDD ke gabatarwa a kasar.”

A halin da ake ciki yanzu ana fuskantar barazanar sake billar yakin basasar kasar Kongo, inda ‘yan tawaye ke kokarin sake hade kansu a iyakokin kasar da Ruwanda, a yayinda ita kuma gwamnati a fadar mulki ta Kinshasa ta sa ido tana kallo bata da ikon tabuka kome, in ji mujallar DER SPIEGEL, wadda ta ci gaba da cewar:

“Tun bayan da janar Laurent Nkunda ya koma yankin gabacin Kongo, inda yayi kaurin suna wajen ta’asa da kashe-kashe na ba gaira, mutane suka shiga halin zaman dardar a Bukavu. Kusan a kowace rana ta Allah sai an samu wasu munanan rahotanni daga kuryar yankunan karkara na gabacin Kongo, kuma a sakamakon haka, mutane, musamman ma mata suka fara tattara nasu ya nasu domin tashi daga wannan yanki, saboda a ganinsu dawowar janar Nkunda na ma’anar sake shiga wani sabon mawuyacin hali na yakin basasa da ta’asar kisan kare dangi.”