1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 23, 2005

Gwamnatin Mugabe tayi fatali da karar da manoma farar fata suka daukaka

https://p.dw.com/p/Bvoz
Shugaba Robert Mugabe
Shugaba Robert MugabeHoto: dpa

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da al’amuran nahiyar Afurka a wannan makon mai karewa har da korafin cin hanci da sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya samu kansa a cikin, lamarin da ya dabaibaye bangaren farko na tarihin rayuwarsa da aka gabatar. Akwai dai masu ra’ayin cewar shiru da halin sanin ya kamata da babban jami’in diplomasiyyar ke nunarwa shi ne ke ba wa masu sukan lamirinsa damar cin karensu babu babbaka. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar GENERAL ANZEIGER ta birnin Bonn cewa tayi:

“Babban sakataren MDD Kofi Annan, wanda shi ne ya fi kowane farin jini daga cikin manyan sakatarorin majalisar guda bakwai da aka yi, yana cikin hali na kaka-nika-yi sakamakon tabargazar cin-hancin nan da ya shafi shirin cinikin mai domin sayen kayan masarufi ga al’umar Iraki dake fama da radadin wahala, shirin da aka gabatar tsakanin 1996 zuwa shekara ta 2003. Tababar da ake yi shi ne ko Ya-Allah wasu na kurkusa da sakatare-janar din na da hannu a wannan tabargaza, wacce ta hada har da dansa Kojo Annan. Zargin da ake wa Kofi Annan ya zo daidai lokacin da sakatare-janar din ke kokarin ganin an aiwatar da garambawul ga manufofin MDDr.”

A can kasar Botswana ta yankin kudancin Afurka gwamnati na da shirin canza wa wasu kabilun kasar guda biyu mazauni sakamakon dimbin albarkatun damenti da aka gano a yankinsu, kuma masu sukan lamirin wannan mataki na batu a game da tsangwama da gallaza wa mutanen da lamarin ya shafa. Jaridar NEUES DEUTSCHLAND ta ggabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“A makonnin baya-bayan nan an samu rahotanni masu tarin yawa dake Allah waddai da matakan da gwamnati ke dauka a kasar Botswana na take hakkin ‘yan kabilun Gana da Gwi. A makon da ya gabata gwamnatin kasar da ake yaba mata da bin wani nagartaccen tsari na mulkin demokradiyya tsantsa, ta kayyade wa kabilun guda biyu wa’adin kwanaki goma domin su tattara nasu ya nasu su fice daga yankunan da aka kebe musu sakamakon dimbim arzikin damentin da aka gano. A halin yanzu haka gwamnati kokari take yi daga an goge wani sakin layi na daftarin tsarin mulkin kasar dake ba wa wadannan kabilu kariya a yankunansu na asali.”

A karon farko an daukaka kara akan wani limamin katolika, farar fata daga kasar Belgium, bisa zarginsa da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ya wanzu a kasar Ruwanda sama da shekaru goma da suka wuce. Amma a daya bangaren kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun ce wannan zargin ba kome ba ne illa wata manufa ta makarkashiya, kamar yadda jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

“A farkon watan satumba ne aka tsare Guy Theunis da laifin amfani da matsayinsa na babban editan wata mujalla ta kasar Ruwanda wajen yayata kabilanci da wariyar jinsi da kuma rura wutar kisan kare dangin da ya biyo baya a 1994, inda daga bisani shi kansa ya karyata wanzuwar ta’asar ta kisan kiyashi da aka yi wa mutane kusan miliyan daya. Shi dai limamin na darikar katolika ya nuna cewar wannan rahoto da aka buga ba ra’ayi ne na mujallar ba, wadda ainifin makasudinta shi ne ta share fagen tattaunawa a game da mummunan yanayin da aka shiga a kasar Ruwandan a wancan lokaci.”

Gwamnatin Zimbabwe ta sa kafa tayi fatali da karar da wasu manoma farar fata su 4000 suka daukaka dangane da kwace musu gonaki da aka yi ba tare da wata diyya ba, kuma ta haka, kamar yadda jaridar GENERAL ANZEIGER ta nunar, wadannan manoma, wadanda a zamin baya suka taimaka wajen samar da rarar amfanin noma da kudaden musaya na ketare ga kasar Zimbabwe suka wayi gari ba su da wani iko na neman da a maido musu da gonakinsu a shari’ance. Wani abin mamaki ma a cewar jaridar shi ne yadda Mugabe, a cikin jawabinsa ga babbar mashawartar MDD a makon da ya gabata, ya fito karara yana mai nuna cewar kwace gonakin da gwamnatinsa tayi wani bangare ne na matakin yaki da talauci, alhali kuwa manyan jami’an gwamnati ne ke cin gajiyar filayen noma masu albarka da aka kwace, a yayinda su kuma tsaffin dakarun neman ‘yancin Zimbabwe suka share ragowar filayen domin zama na dindindin a cikinsu.