Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.09.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Ci gaban da ake samu a yakin da cin hanci a Nijeriya na daya daga cikin batutuwan da suka shiga kanun labaran Jaridun Jamus

Shugaba Olusegun Obasanjo

Shugaba Olusegun Obasanjo

A wannan makon jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka, kama daga yammaci zuwa gabaci da tsakiya da kuma kudancin Afurka. Amma da farko zamu fara ne da ya da zango a tarayyar Nijeriya inda jaridar DIE TAGESZEITUNG ke cewar bayan shekaru da dama da aka yi ana fatali da manufar yaki da cin hanci a kasar, a watannin baya-bayan nan al’amura sun canza suka dauki wani sabon salo, inda hukumar yaki da cin hanci ta kasar ta shiga bin diddigin lamarin ba sani ba sabo. Jaridar ta kara da cewar:

“Tun misalin shekaru shida da suka wuce ne, bayan da ya dare kan kujerar mulkin Nijeriya shugaba Olusegun Obasanjo yayi alkawarin murkushe matsalar cin hanci a kasar, amma sai a ‘yan watannin baya-bayan nan ne aka fara daukar sahihan matakai akan wannan manufa. Jami’an siyasa da dama, abin da ya hada har da ministoci da wakilan majalisar dokoki da shi kansa shugaba Obasanjo sai da suka ba da shaida gaban hukumar yaki da cin hanci ta kasar Nijeriya. Kazalika matakin ya hada har da kamfanonin kasashen Turai, kamar kamfanin Sagem na kasar Faransa, wanda ake zarginsa da ba da toshiyar baka ta kwatankwacin dala miliyan biyu, sannan shi kuma darektan kamfanin Marsandi, reshen Nijeriya ya kashe kansa da kansa a farkon watan yuni sakamakon tababar da ake yi game da take-takensa.”

An fara shiga takun-saka tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da P/M kasar Habasha Meles Zenawi. Da kakkausan harshe P/M ya kalubalanci Ana Gomes, shugabar tawagar KTT da ta sa ido a zaben Habasha da aka gudanar kwanan baya, wadda ya ce take-takenta tamkar wata gimbiya ce ta mulkin mallaka. Meles Zenawi yayi wannan zargin ne sakamakon rahoton da ta rubuta inda take zargin magudi da almundahana a zaben na Habasha, kamar yadda jaridar Frankfurter Rundschau ta rawaito.

Kasashen Afurka dake fama da dimbin bashi akansu a yanzu zasu samu wata ‘yar sararawa, sakamakon amannar da bankin duniya da asusun ba da lamuni na IMF suka yi da kudurin kasashen G8 da suka fi ci gaban masana’antu game da yafe musu basussukan da suka kai musu iya wuya. Wannan shi ne kanun wani rahoto da jaridar ciniki ta Handelsblatt ta bayar, inda ta kara da cewar:

“Duk da doki da murnar da ake yi da wannan gagarumin ci gaba da aka samu, wanda kuma da yawa daga kasashen Afurka da lamarin ya shafa suka ce zasu yi amfani da shi wajen kyautata al’amuran ilimi da kiwon lafiya da hanyoyin sadarwa a kasashensu, amma fa muhimmin abu shi ne a yi taka tsantsan ka da wadannan kasashe matalauta su sake fadawa cikin wani sabon hali na kaka-nika-yi da wata matsala ta rancen kudi nan gaba. Jaridar ta Handelsblatt ta ce babban misali dai kasar Tanzaniya, wacce a 1999 aka yafe mata kusan kashi 50% na bashin da ake binta, amma sai ta wayi gari da wasu sabbin basussukan na sama da dala miliyan dubu bakwai shekaru biyun da suka wuce.”

A can kasar Nijer, ko da yake har yau akwai mutane sama da miliyan daya dake fama da bala’in yunwa, amma kungiyar taimakon abinci ta MDD ta kayyade yawan taimakon abinci da take bayarwa ga kasar, lamarin da kungiyar likitoci ta duniya ta kalubalance shi da kakkausan harshe, a cewar jaridar RHEINISCHE ZEITUNG, wadda ta kara da bayani tana mai cewar:

“Rahotanni masu nasaba da kungiyar likitoci ta duniya sun ce har yau ana fama da mawuyacin hali a sassa da dama na kasar Nijer kuma a sakamakon haka kungiyar ke sukan lamirin kungiyar taimakon abinci ta MDD dangane da shawararta ta kayyade yawan taimakon da take bayarwa.”

A karon farko, bana za a gudanar da taron duniya akan man fetur a nahiyar Afurka, sakamakon bunkasar da yammacin nahiyar ke samu a harkar hakan man yanzu haka, in ji jaridar DIE TAGESZEITUNG, wadda ta kara da cewar:

“Sannu a hankali nahiyar Afurka zata zama wata muhimmiyar madogara wajen hako mai a duniya, inda a halin yanzu haka ake hako abin da ya kai garewani miliyan hudu a rana a mashigin tekun Guinea kuma adadin zai karu zuwa garewani miliyan biyar da rabi nan da shekara ta 2009. To sai dai kuma abin takaici shi ne galibi harkar hakan man na tafiya ne akan wata sibga ta mulkin mallaka ta yadda talakawan kasa basa cin gajiyar wannan arzikin da Allah Ya fuwace wa kasashensu.”