1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 7, 2005

Halin da ake ciki dangane da bakin haure a Spain shi ne ya fi daukar hankalin Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/Bvox
'yan gudun hijira a Melilla
'yan gudun hijira a MelillaHoto: AP

A hakika dai babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na kusan dukkan jaridun Jamus dangane da al’amuran afurka shi ne halin da ake fama da shi a game da bakin hauren dake ci gaba da tuttudowa ta kan kasar Moroko domin karasowa nahiyar Turai. A cikin nata sharhin da ta rubuta karkashin taken: “Wajibi ne a gusar da shingen da aka kafa a Melilla”, jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“ A zamanin baya lokacin da ake fama da katangar nan ta Berlin da ta raba Jamus gida biyu an fuskanci kiraye-kiraye daga kasashen yammaci dake maganar ‘yanci ga walwala ga al’umar tsofuwar tsofuwar Jamus ta Gabas, kuma duk wani dan kasar da ya tsallako zuwa yammaci yana samun cikakken goyan baya da taimakon da yake bukata domin tafiyar da rasuwarsa ta yau da kullum. Amma a yau katangar an kafa ta ne tsakanin kasashen arwaci masu wadatar arziki da kasashen kudanci ‘yan rabbana ka wadata mu. Abin dake faruwa a Melilla na nuni ne da wani sabon yayi na wariyar jinsi da aka shiga tsakanin yanukunan duniya guda biyu, nahiyar Turai ta farar fata da nahiyar Afurka ta bakar fata. Amma fa wajibi ne kasashen Turai su yi watsi da wannan akida daidai yadda suka taimaka wajen ganin an murkushe wariyar jinsin a Afurka ta Kudu.”

Ita ma jaridar DIE WELT ta duba halin da aka shiga baya-bayan nan a mashigin tekun Melilla na kasar Spain, inda a jiya alhamis wasu ‘yan Afurka su shida suka rasa lokacin da jami’an tsaro suka bude wuta kan mutane kusan dubu dake kokarin tsallake shingen da aka kafa a yankin domin hana tuttudowar bakin haure. Jaridar ta ce gwamnatin kasar ta Spain, a karkashin wata yarjejeniyar da ta cimma da Moroko zata rika mayar da bakin hauren zuwa makobciyar tata a arewacin Afurka kuma tuni ta kara karfafa matakan tsaron iyaka. To sai dai kuma jaridar ta DIE WELT ta ambaci kakakin ‘yan adawa na kasar Spain akan manufofin ketare Gustavo de Aritegui yana mai zargin cewar akwai wasu a kasar Moroko dake neman amfani da halin da ake ciki a Melilla da Ceuta domin sake farfado da sabanin da ake yi tsakanin kasashen biyu akan wadannan tsuburai, inda suke cewar wai da dai Spain zata mayarwa da Moroko tsuburan nata guda biyu da kuwa nan take za a shawo kan matsalar ta bakin haure.

Kwararrun masana al’amuran tattalin arziki sun fara gargadi a game da yiwuwar tabarbarwar kasar Zimbabwe kwata-kwata, inda al’amuran sufuri suka tsaya cik sakamakon karancin kudi, shi kuma asusun ba da lamuni na IMF ya bayyana damuwarsa matuka ainun a game da halin da ake ciki a cewar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU. Jaridar ta kara da cewar:

“Rahotanni masu nasaba da rundunar sojan kasar zimbabwe sun ce tuni aka sallami wasu sojoji dubu biyu saboda karancin abinci a barikokin sojan. Hatta kafofi na gwamnati suna fama da matsalar motoci sakamakon rashin man fetur. Su kansu mahukunta a fadar mulki ta Harare a kasuwannin bayan fage suke sayen mai. A sakamakon haka asusun ba da lamuni na IMF ke bayyana damuwarsa da kuma gargadin yiwuwar tabarbarewar kasar Zimbabwen ma baki daya”.

Ana fuskantar barazanar sake billar yaki a arewacin kasar Kongo tare da kasar Uganda sakamakon amfani da ‚yan tawayen Ugandan ke yi da wannan yanki domin shirya hare-harensu na sare ka noke. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

„A cikin ‚yan kwanakin baya-bayan nan dukkan kasashen Uganda da Kongo sun bunkasa yawan sojojinsu akan iyakokin dake tsakaninsu. Dalilin wannan hali na dardar kuwa shi ne kasancewar tun misalin makonni biyu da suka wuce wasu dakarun kungiyar tawaye ta LRA su kimanin 400 daga kasar Uganda suka kafa sansaninsu a arewa-maso-gabacin Kongo suka kuma ki yarda sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD ko sojan kasar Kongo su kwance damararsu ta makamai.“