Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Matsalar 'yan gudun hijira a Spain ita ce ta fi daukar hankalin masharhanta

Darfur

Darfur

A wannan makon ma daidai da makon da ya gabata, inda dukkan jaridu da mujallun Jamus suka mayar da hankalinsu kacokam akan mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira na Afurka ke ciki a tsakanin kasashen Moroko da Spain a kokarinsu na tsallakowa zuwa nahiyar Turai domin kyautata makomar rayuwarsu. A cikin nata sharhin jaridar DIE ZEIT mai fita mako-mako ta dora wani bangare na laifin matsalolin da nahiyar Afurka ke fama da su ne akan manufofin noma na kungiyar tarayyar Turai inda take cewar:

“Matsalolin Afurka da kuma kaddarar ‘yan gudun hijirar nahiyar na da dalilai masu yawa, kuma ana iya dora laifin akan dukkan kasashen Afurka da na Turai. Kuma wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanysa ake fama da wahala wajen neman bakin zaren warware matsalar ‘yan gudun hijirar da suka yi cincirindo yanzu haka a iyakar kasar Spain. A yayinda a wasu kasashen Afurka ake fama da cin hanci na mahukunta da yake-yake na basasa ko kuma bunkasar yawan jama’a, a daya bangaren manufofin noma na kasashen Turai na taimakawa wajen gurgunta tattalin arzikin Afurka, inda suke karya farashin amfanin da manomansu ke samarwa domin shigar da su akan farashi mai rafusa a kasuwannin Afurka, kuma ta haka suke kashewa manoma na kasashen nahiyar kasuwa.”

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

“Nahiyar Turai ba zata iya yin ko oho da matsalar dmbin ‘yan gudun hijirar dake kokarin shigowa nahiyar domin kyautata makomar rayuwarsu ba. Wannan matsala ce dake bukatar a tinkare ta daga tushenta, saboda tana da dalilai da dama. Galibi babu wani takamaiman taimakon da ake gabatarwa domin sake gina kasashen ya bannatar dasu ko kuma kandagarkin wasu rikice-rikice da suka fara kunno kai. A baya ga haka kasashe mawadata na kashe makudan kudi domin karya farashin amfanin noma ta yadda kasashen Afurka ba zasu iya gogayya da su a kasuwannin duniya ba. Muddin ba shawo kan matsaloli na rayuwa aka yi a nahiyar Afurka fa to kuwa za a ci gaba da fama da matsalar ‘yan gudun hijirar har sai illa masha’a Allahu.”

A wannan makon aka gabatar da matakin farko na shari’ar tsofon mataimakin shugaban kasar Afurka ta Kudu Jacob Zuma, lamarin dake haddasa mummunan sabani tsakanin ‘ya’yan kungiyar ANC. Jaridar NEUES DEUTSCHLAND tayi bitar lamarin inda take cewar:

“A halin yanzu haka dai ana fama da baraka tsakanin ‘ya’yan kungiyar ANC dake mulki a ATK sakamakon shari’ar da ake wa Jacob Zuma tsofon mataimakin shugaban kasa bisa tuhumarsa da laifin cin hanci. Sama da mutum dubu hudu daga sassan kasar daban-daban suka hallara kofar kotun domin nuna goyan bayansu ga tsofon dan juyin juya halin. A bainar jama’a suka rika kone rigunan dake dauke da hoton shugaba Thabo Mbeki. Mai yiwuwa dai wannan kiki-kaka da ake yi wata alama ce ta gwagwarmayar neman wanda zai maye gurbin shugaba Mbeki, kamar yadda aka taba fuskanta dangane da wanda zai gaji shugaba Nelson Mandela a zamanin baya.”

Al’amura na dada yin tsamari a sabon rikicin da ya sake kunno kai a lardin Darfur na kasar Sudan, wanda hatta sojan kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afurka suka fara jin radadinsa in ji jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU, wadda ta ci gaba da cewar:

“Gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ita ce ummal’aba’isin wannan sabon mawuyacin halin da aka shiga saboda ta ki ta cika alkawarinta game da kwance damarar makaman dakarun sa kai na larabawa ta kuma gurfanar da masu laifin keta hakkin dan-Adam gaban kotu. Kawo yanzun dai rikicin lardin na yammacin kasar Sudan ya halaka mutane sama da dubu dari biyu.”