1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 8, 2004

Boren sojoji a kasar Guinea Bissau na daya daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka mayar da hankali kansu a rahotannin da suka bayar game da al'amuran Afurka

https://p.dw.com/p/Bvfm

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa har da halin da ake ciki a Guinea Bissau ta yammacin Afurka sakamakon boren sojojin da aka fuskanta a wannan kasa. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto game da haka inda take cewar:

"Manazarta na fargabar barkewar wani yaki na basasa a kasar Guinea Bissau sakamakon ta da kayar baya da wani rukuni na sojan kasar suka yi. Wadannan sojojin, wadanda suka bindige tsofon shugaban sojan kasar da kuma darektan hukumar leken asirinta, sun taba aiki a karkashin tutar sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a Liberiya sun kuma nema daga gwamnati lalle sai ta rika biyansu albashi daidai da sauran sojojin da ba a yi musu fansho ba, sannan a baya ga haka ta biya kudaden diyya dangane da sojojin da suka yi asarar rayukansu. Kazalika sun yi zargin cin hanci da almundahana a tsakanin manyan hafsoshin soja kasar ta yammacin Afurka."

A can Tarayyar Nijeriya gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo ta gabatar da matakan tattaunawa domin shawo kan rikicin yankin Niger-Delta a cikin ruwan sanyi. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

"Shawarar da shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya tsayar game da shiga tattaunawa da madugun ‘yan tawaye mai ikirarin fafutukar ‘yantar da al’umar Ijaw Dokubo Asari, wata manufa ce ta siyasar sanin makama, kamar yadda aka san shugaban Nijeriya tun da dadewa. To amma fa a daya hannun an daukaka matsayin madugun ‘yan tawayen da ba shi wata martaba ta yadda zai iya zama abin koyi ga wasu dake sha’awar ta da zaune a kasar nan gaba. Domin kuwa gabatar da shawarwari na ma’ana ne cewar gwamnati ta amince da hakkin wanzuwar wasu sojan sa kai masu zaman kansu."

Al’amura sai dada rincabewa suke yi a kasar Sudan a yayinda ita kuma MDD take ci gaba da lalube a cikin dufu a game da shawarar kakaba wa fadar mulki ta Khartoum takunkumin karya tattalin arzikin kasa, kamar yadda jaridar SÜDDEUTSCHE ZEUTUNG ta nunar a cikin wani rahoton da ta bayar, ta kuma kara da cewar:

"A sakamakon mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira kimanin miliyan daya da dubu 300 ke ciki da kuma ci gaba da fafatawar da ake yi a lardin Darfur kungiyoyin taimakon jinkai ke tsoron kara kazancewar al’amura a kasar Sudan. Kuma ko da yake kudurin MDD ya tanadi daukar matakan takunkumi akan fadar mulki ta Khartoum, amma da wuya a iya wanzar da wannan mataki, saboda tuni kasar China ta bayyana shirinta na hawa kujerar na ki. Ana fama da matsalar karancin abinci saboda gibin kashi 80% na amfanin noma da aka samu sakamakon fatattakar mutanen da aka yi daga yankunansu na asali."

Majalisar dokokin Afurka Ta Kudu ta albarkaci wata takardar doka dake halasta kiwon lafiya da magungunan gargajiya a kasar. Jaridar BERLINER ZEITUNG ta bayyana dalilin wannan ci gaba tana mai cewar:

"Manufar ma’aikatar kiwon lafiyar ATK a game da wannan doka shi ne ba da damar shigar da masana magungunan gargajiya a matakan yaki da tarin fuka da sauran cututtukan dake addabar al’umar kasar. Kazalika wannan mataki zai kawo ga cunkoson jama’a da ake fuskanta a manya da kananan asibitocin ATKn."