Afurka A Jaridun Jamus | Siyasa | DW | 05.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Liberiya shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon

Tashe-Tashen hankula a Monrovia

Tashe-Tashen hankula a Monrovia

A wannan makon, muhimmin abin da masharhanta na jaridun jamus suka mayar da hankali kansa dangane da nahiyar Afurka shi ne mawuyacin hali na zaman dardar da aka sake shiga a can kasar Liberiya, inda rahotanni suka ce akalla mutane 14 suka yi asarar rayukansu sannan wasu daruruwan kuma suka ji rani sakamakon wata tashin-tashinar da ta barke a Monrovia, fadar mulkin kasar ta yammacin Afurka. A lokacin da take sharhi game da haka, jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

"Wannan tashin-tashinar wata alama ce dake bayani a game da ire-iren takaicin dake tattare a zukatan al’umar liberiya saboda ba su ga wani canjin da aka samu ga makomar rayuwarsu ba tun bayan kawo karshen yakin basasar wannan kasa. Watanni 15 bayan fatattakar tsofon shugaba Charles Taylor da aka yi har yau jama’a na cikin mawuyacin hali na rayuwa. Ita kanta fadar mulki ta Monrovia ba ta da wutar lantarki ko ruwan sha mai tsafta. Bugu da kari kuma kimanin kashi 80% na al’umar kasar ne ke zaman kashe wando. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar duka-duka mutum dubu 50 ne suka koma gida daga cikin dubban daruruwan ‘yan kasar da suka yi kaura zuwa kasashen dake makobtaka da ita."

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Bayan ‘yar sararawar da aka samu ta tsawon shekara daya, a yanzu murna na neman koma ciki dangane da zaman lafiyar Liberiya ta la’akari da tashe-tashen hankulan baya-bayan nan, lamarin dake yin nuni da hali na zaman dardar da ake ciki a kasar, duk kuwa da cewar an samu kaar kance damarar makaman dakarun sa kai kimanin dubu 95, a sanarwar MDD."

A can lardin Darfur al’amura na dada rincabewa, inda MDD ta fito fili tana Allah Waddai da matakan da gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ke dauka na canza wa mazauna yankin muhalli ala-dole. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi bitar matsalar sai ta kara da cewar:

"Ana fama da sabani tsakanin gwamnatin Saudan da MDD sakamakon wani matakin da fadar mulki ta Khartoum ta gabatar na canza wa ‘yan gudun hijirar Darfur matsugunai, inda a ranar talata da sanyin safiya wasu manyan motoci na ‘yan sanda suka yi jigilar mutane kimanin dubu biyu daga Nyala zuwa wasu yankunan dabam. Bisa ga ra’ayin jami’an taimakon jinkai manufar wannan mataki shi ne domin tsorata ‘yan gudun hijirar da kuma share hanyar mayar da su kauyunkansu da aka bannatar kwata-kwata. Kimanin ‘yan gudun hijira miliyan daya da dubu 450 ne suka tagayyara sakamakon hare-haren dakarun sa kai na Larabawa, inda wasu 200.000 daga cikinsu suka nemi mafaka a makobciyar kasa ta Chadi."

Ita ma jaridar DIE Tageszeitung ta gabatar da sharhi inda take cewar:

"Irin wannan mataki ba abin da zai tsinana illa ya kara sanya al’amura su dada yin tsamari. Wani abin takaici ma shi ne yadda mahukuntan Sudan ke ke wa ‘yan gudun hijirar karyar cewa MDD ce ta ba da shawarar canza musu muhallin zama."

An shirya gudanar da zabe a kasar Kongo a shekara mai zuwa, amma fa kawo yanzu babu wani takamaiman shirin da gwamnatin rikon kwarya ta shugaba Joseph Kabila ta tanadar dangane da wannan manufa. To sai dai kuma ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul, wacce ta kai ziyara kasashen Kongo da Ruwanda a wannan makon ta bayyana gamsuwarta da irin ci gaban da ake samu a wannan yanki. A lokacin da take ba da rahoto akan haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

"Duk da gamsuwar da ta bayyanar, ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus ta ki amsa rokon MDD a game da shigar da sojan kasar a tsakanin sojan kiyaye zaman lafiyar majalisar Monuc a takaice, a kasar Kongo. Ita dai rundunar ta kiyaye zaman lafiya, wacce aka dora mata alhakin taimakawa a shirye-shiryen zaben na shekara mai zuwa ta sake nuna gazawa a makonnin baya-bayan nan abin da ya taimaka wajen zubewar martabarta a idanun al’umar Kongo."