Afurka A Jaridun Jamus | Siyasa | DW | 12.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire shi ne muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon

A wannan makon ma kamar yadda aka saba jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa a game da nahiyar Afurka. To sai dai kuma sun fi mayar da hankali ne kacokam akan mawuyacin halin da aka shiga a kasar Cote d’Ivoire, misali jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta bi diddigin rikicin tun daga tushensa inda tayi bayani tana mai cewar:

"Tabarbarewar al’amuran kasar Cote d’Ivoire ta fara ne tun daga jajibirin bikin kirismetin shekarar 1999 lokacin da janar Robert Guei ya kifar da gwamnatin shugaba Henri Konan Bedie. Bayan wannan juyin mulki janar Guei yayi alkawarin tsayar da zabe tare da canza daftarin tsarin mulkin kasar, wanda ya zama ummal’aba’isin rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar ta yammacin Afurka. Domin kuwa a karkashin wannan tsari aka kirkiro akidar nan ta "Dan-Kasar Cote d’Ivoire Tsantsa". A sakamakon haka aka hana tsofon P/M Cote d’Ivoire Alassane Ouattara shiga zaben da aka shirya, wai saboda shi din dan usulin kasar Burkina Faso ne. Tare da wannan ikirarin aka mayar da ‘yan arewacin kasar saniyar ware a al’amura na yau da kullum. Wannan mummunar akidar, maras tushe, ita ce ta haifar da rikicin dake nema da ya rushe kasar kwata-kwata."

Ita kuwa jaridar DIE WELT tayi bitar dangantakar Cote d’Ivoire ne da Faransa ta la’akari da bayannin da shugaba Chirac yayi na cewar muhimmin abin da Faransar ta sa gaba shi ne samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin illahirin kabilun kasar ta Cote d’Ivoire. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Bisa ga ra’ayin shugaba Gbagbo da magoya bayansa dai Faransar da ‘yan tawayen duk jirgi daya ne ke dauke da su kuma babban shadair haka shi ne umarnin da Chirac ya bayar na lalata jiragen saman yakin Cote d’Ivoire din baki daya, bayan da wasu jiragen saman yakinta guda biyu suka kai farmaki kan sojojin Faransa suka kuma kashe dakaru tara a cikin batan-basira a cewar Gbagbo. Shugaban na Cote d’Ivoire har yau yana kan bakansa na ci gaba da yakar ‘yan tawayen, wai saboda a dakatar da tabarbarewar tattalin arzikin arewacin kasar. Domin kuwa a can ne manyan gonakin coco suke, wadanda Cote d’Ivoire ta dogara kacokam akansu domin samun kudaden shiga.

Al’amura sai dada tabarbarewa suke a lardin Darfur na kasar Sudan, inda ake fargabar cewar za a wayi gari rikicin ya zama gagara badau muddin ba a kawo karshensa a cikin hamzari ba. Akan haka jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi hira da P/M kasar Habasha Meles Zenawi, wanda a wannan makon ya kawo ziyara Berlin, inda kuma yayi bayani da cewar:

"A dai halin da ake ciki yanzu an fara samun ci gaba akan hanyar sasanta rikicin inda aka cimma wasu yarjeniyoyi guda biyu, sannan ita kuma Kungiyar Tarayyar Afurka ta tura dakarun sojojinta 300 zuwa Sudan. Ba shakka ana bukatar abin da ya ribanya hakan har sau goma amma, kamar yadda aka sani, kasashen Afurka na fama da matsalar kudi. A bisa dalilin haka ne suka gabatar da roko ga MDD da sauran kungiyoyi na kasa da kasa domin su ba da gudummawar kudi ta yadda za a tafiyar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a lardin Darfur akan wata sibga mai ma’ana."

Jamus ta tsayar da shawarar karfafa hadin kai da kasashen Kongo da Ruwanda bisa manufar kyautata makomar doka da oda a yankin kuryar tsakiyar Afurka. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ce ta rawaito wannan bayanin daga bakin ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemari Wieczorek-Zeul bayan ziyarar da ta kai yankin baya-bayan nan. Jaridar sai ta kara da cewar:

"An gabatar da wasu tsayayyun shirye-shirye da suka tanadi kyautata makomar rayuwar jama’a kai tsaye, inda za a mayar da hankali wajen samar musu da ruwan sha mai tsafta da kuma wayar da su a game da zaben da ake shirin gudanarwa a kasar Kongo shekara mai zuwa. Idan har aka samu canjin gwamnati a cikin ruwan sanyi a zaben na watan yuni mai zuwa to kuwa hakan zata taimaka wajen lafar da kurar rikici da kama hanyar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya.

Masu sauraro duka-duka iyakacin abin da ya samu shiga ke nan a cikin rahotannin jaridun na Jamus akan al’amuran nahiyar mu ta Afurka. Sai kuma in ce Ibrahim gare-ka.