Afurka A jaridun Jamus | Siyasa | DW | 24.06.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afurka A jaridun Jamus

Matsalar cin hanci a kasar Liberiya na daya daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus a wannan makon

A wannan makon ma kamar yadda aka saba jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan halin da ake ciki a sassa dabam-dabam na nahiyar Afurka, kamar dai wani sabon hali na ta da zaune tsaye da aka shiga a Nijeriya da barazanar billar sabon rikici a Sudan da halin da ake ciki a Liberiya da sauran sassa na Afurka. A makon da ya gabata aka yi garkuwa da wasu ma’aikatan hakan mai guda shida a Nijeriya, abin da ya hada har da wasu Jamusawa. Kuma ko da yake an sake su, amma wannan ci gaba ya sanya wasu kasashe suka tsayar da shawarar rufe kananan ofisoshin jakadancinsu dake Lagos na wani dan gajeren lokaci. Jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar lamarin inda take cewar:

“Dalilin matakin rufe kananan ofisoshin jakadancinsu da kasashen Amurka da Birtaniya da Italiya da Jamus suka dauka shi ne gangamin da aka yi a game da makarkashiyar kai harin ta’addanci a daidai lokacin da Amurka da wasu kasashe tara na nahiyar Afurka ke gudanar da rawar daji a yankin Sahel. Sojojin Amurka 700 da na kasashen Afurka 3000 suka shiga wannan atesaye a karkashin matakan murkushe ta’addanci a duniya. Ita dai Amurka fargaba take game da sulalewar ‘yan ta’adda, musamman daga arewacin Afurka zuwa Iraki. Ana kyautata yaduwar magoyan bayan wata kungiya mai ra’ayin mazan-jiya, ko kuma ‘yan salafi dake da dangantaka ta kut-da-kut da al’ka’ida, a kasashe kamar su Mauritaniya da Mali da Chadi. “

Gwamnatin rikon kwarya da aka nada a kasar Liberiya, wacce ke samun kariya daga MDD, an ce, ita ce ta fi kowace almubazzaranci da watandarar da dukiyar kasar fiye da dukkan gwamnatocin da aka yi a kasar. A lokacin da take gabatar da wannan rahoto, jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“A yayinda ya rage watanni shida kacal kafin a gudanar da zaben sabuwar gwamnati a kasar Liberiya, jami’an gwamnatin rikon kwarya dake ci sun tashi haikan wajen wawason dukiyar kasar da arzuta kansu da kansu ba ji ba gani. Saboda a ganinsu duk wanda bai cika aljifunsa ba a halin da ake ciki yanzu to kuwa zai yi nadama nan gaba, domin kuwa murnarsa zata iya komawa ciki, saboda mai yiwuwa ba zai taba sake samun irin wannan dama ba nan gaba. Kusan babu wani banbanci tsakanin shugaba Gyude Bryant da mukarrabansa, a bangare guda, da kuma tsaffin shuagabannin kasar a daya bangaren. Dukkansu jirgi daya ne ke dauke da su. Kuma ire-iren wannan halayya ta cin hanci da al-mubazzaranci ce ta haddasa yakin basasar da ya tabarbara al’amuran kasar ta Liberiya.”

A can kasar Somaliya, har yau tana kasa tana dabo dangane da makomar zaman lafiyarta, domin kuwa hatta ita kanta sabuwar gwamnatin da aka nada karkashin shugaba Abdullahi Yussuf Ahmed tana iya fuskantar barazana da billar wani sabon yakin basasa a kasar da al’amuranta suka tabarbare kwata-kwata, a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung, wacce ta kara da bayyana cewar:

“A hakika nada sabuwar gwamnatin ta sabuwar majalisar dokoki babban ci gaba ne akan matakin samar da zaman lafiyar kasar Somaliya da kuma sake farfado da al’amuranta, amma a inda take kasa tana dabo shi ne kasancewar tun da dadewa aka raba madafun ikon kasar tsakanin haulakan yakinta. Bugu da kari kuma sakamakon shekara-da-shekaru da tayi bata da wata tsayayyar gwamnati, kasar ta Somaliya ta samu kanta akan wani tsari na daban ta yadda sabuwar gwamnatin da aka nada zata iya zama tamkar kadangaren bakin tulu ga al’umar kasar.”

A gabacin kasar Sudan an sake shiga wani sabon hali na yakin basasa, inda ‘yan tawayen Beja Congress ke amfani da harabar makobciyar kasa ta Eritrea domin kai farmaki kan sojojin gwamnati. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung ta ce bayan kudancin Sudan da Lardin darfur a yanzu kasar Sudan ta sake shiga wani sabon yakin basasa cikon na uku a gabacinta. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Yau sama da shekaru goma ke nan ake fuskantar tashe-tashen hankula akai-akai a gabacin Sudan, inda mazauna yankin, daidai da kudanci da kuma yammacin Sudan ke tattare da ra’ayin cewar ana kwararsu a al’amuran rayuwa ta yau da kullum. Kungiyar tawaye ta Beja Congress tana amfani da harabar makobciyar kasa ta Eritrea domin shirya hare-harenta akan sojan kasar Sudan. Kuma wannan sabon hali mawuyaci da aka shiga ya zo ne daidai lokacin da al’amura suka fara sararawa, inda a baya ga yarjejeniyar sulhu da aka kulla da kudancin Sudan ake samun ci gaba da shawarwarin zamkan lafiyar Darfur, kuma a karshen makon da ya gabata gwamnatin Sudan ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya larabawa ‘yan hamayya, wadanda ke neman ganin an dama dasu a shirin sabon daftarin tsarin mulkin Sudan.