1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A jaridun Jamus

December 2, 2005

Ranar Aids ta duniya ita ce ta fi daukar hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvQD
Aids a Afurka
Aids a AfurkaHoto: AP

Babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon dai shi ne ranar duniya ta nuna zumunci ga masu fama da cutar kanjamau da kuma yadda wannan cuta ke neman kayar kifi a wuyan kasashe da dama na nahiyar Afurka. Da farko kuwa zamu fara ne da rahoton jaridar GENERAL-ANZEIGER ta birnin Bonn, wacce ta leka can kasar Afurka ta Kudu domin bitar yadda matsalar yaduwar cutar kanjamau ke addabar al’umar kasar a rayuwarsu ta yau da kullum, ba ma kawai ta fuskar kiwon lafiya kadai ba, kazalika har da fannin tattalin arziki da zamantakewar jama’a. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“A halin da ake ciki yanzu haka makabartun ATK na fama da cunkoson gawawwakin mutanen da cutar kanjamau ta kashe su a yayinda danginsu kuma ke fama da basussuka akansu sakamakon yawan abin da suke kashewa wajen dawainiyar makoki. Wani da ake kira Paul Sithele mai shekaru 60 da haifuwa, bashi ya kai masa iya wuya saboda rancen kudin da yayi wajen makokin ‘ya’yansa guda biyu da suka yi asarar rayukansu sakamakon cutar kanjamau. A yayinda a zamanin baya yawa-yawancin matattun kan samu akalla shekaru 70, a yanzun akasarinsu ba su kai shekaru arba’in na haifuwa ba.”

Ita kuwa jaridar DIE TAGESZEITUNG lekawa tayi kasar Uganda, wadda a zamanin baya ake yaba mata da zama abin misali game da matakan yaki da cutar kanjamau da take dauka, amma a yanzu murna na neman komawa ciki sakamakon wata tabargaza ta cin hanci da aka gano a karkashin wadannan matakai na yakar kanjamau. Jaridar ta kara da cewar:

“A wajejen karshen shekarun 1980 kasar Uganda ta samu kafar kayyade yawan masu kamuwa da cutar kanjamau daga kashi 20 zuwa kashi 7 cikin dari a shekara. Amma a yanzu kasar ta samu kanta a cikin wata tabargaza ta cin hanci da ta shafi asusun yaki da cutar kanjamau na MDD. Wannan tabargazar ta kai ga dakatar da dukkan ayyukan asusun a kasar ta gabacin Afurka. Kimanin dala miliyan 201 MDD ta ware domin amfanin kasar Uganda, inda tuni aka danka mata dala miliyan arba’in da biyar. Amma bincike ya nuna cewar kusan dukkan wadannan kudade sun kwarara ne zuwa aljifan gaggan jami’an siyasar kasar wadanda ke amfani da sunayen wasu kafofin yaki da cutar kanjamau na jabu.”

A can kasar Gabun shugaba Umar Bongo ya sake lashe lashe zaben kasar da aka gudanar a wannan makon domin wani sabon wa’adi na mulki na shekaru bakwai masu zuwa bayan shekaru 38 da yayi yana shugabancin wannan kasa. Amma bisa ga ra’ayin jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG duk da wadannan shekaru masu tarin yawa da shugaba Bongo yayi yana kan karagar mulki, zai zama babban kuskure a kwatanta shi da sauran ‘yan kama karyar da aka yi a nahiyar Afurka. Jaridar ta ce:

“Ko da yake ‘yan hamayya sun yi zargin magudi a zaben na kasar Gabun, amma a hakika shugaba Bongo, mutum ne mai sassaucin manufofi ba ya mulki na danniya da kama karya, a maimakon haka kirkiro wata kyakkyawar dabara dake taimaka masa wajen ci gaba da mulki. Ita dai kasar Gabun tana da albartun kasa abin da ya hada har da man fetur dake samar mata da kudaden shiga. Shugaba Bongo kan yi amfani da wadannan kudade domin neman goyan baya daga masu fada a ji a kasar, lamarin da ya sanya shugaban ke da ikon dogara akan da yawa daga cikin jam’iyyun siyasar gabansa gadi.”

A wannan makon gano gawawwakin wasu ‘yan daruruwan tsaffin mayakan kungiyar neman ‘yancin kan Namibiya ta SWAPO a wani katon ramin da ake binnesu a ciki. A lokacin da ta tabo wannan rahoton jaridar NEUES DEUTSCHLAND cewa tayi:

“Da yawa daga gawawwakin sun mutu ne tsakanin 1985 da 1989. A wancan lokaci kuwa Namibiya na karkashin mulkin mallakar Afurka ta Kudu ne. Amma tsofon kwamandan askarawan ATKn a Namibiya ya nuna cewar ba ya da wata masaniya a game da wannan tabar gaza da kisan kiyashi, inda yace a tambayi tsofon kantoman MDD akan Namibiya Marti Ahtisaari dan kasar Findland saboda a wancan lokaci shi ne ke da alhakin al’amuran tsaro a kasar a dab da samun ‘yancin kanta.”