Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 23.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Rikicin Sudan da Chadi na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka mayar da hankali kansu

'Yan gudun hijirar Sudan a Chadi

'Yan gudun hijirar Sudan a Chadi

Daya daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin da jaridun Jamus suka bayar akan al’amuran Afurka a wannan makon mai karewa dai har da halin da ake ciki dangane da rikici tsakanin Sudan da Chadi. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar lamarin inda take cewar:

“Kazamar bata-kashin da aka gwabza akan iyaka tsakanin Chadi da Sudan ta jefa shugaba Idris Deby cikin wani mawuyacin hali. Ita dai Sudan tana zarginsa ne da laifin rufa wa ‘yan tawayen Darfur baya. Amma fa wannan ba ita ce kadai matsalar da shugaban kasar Chadin ke fama da ita ba. Domin kuwa a karshen makon da ya gabata wata kungiya ta ‘yan tawaye mai kiran kanta wai kungiyar fafutukar neman mulkin demokradiyya da walwala a Chadi RDL a takaice ta ba da sanarwar kame wani yanki garin Adre dake bakin iyakarta da Sudan, wanda ke ma’anar sake tsundumar kasar cikin wani sabon yaki na basasa a baya ga dubban ‘yan gudun hijirar da take karbar bakuncinsu daga lardin Darfur.”

A wannan makon kasar Tanzaniya ta samu sabon shugaba sakamakon zaben da aka gudanar, inda a ranar larabar da ta wuce hukumar zabe ta kasar ta ce dan takarar jam’iyyar CCM dake mulkar Tanzaniya tun bayan samun ‘yancin kanta a 1961 Jakaya Kikwete ya lashe kashi 80% na jumullar kuri’un da aka kada, kuma masu sa ido na kasa da kasa sun yaba da yadda zaben ya gudana ba tare da magudi ko tangarda ba. Babban abin da al’umar Tanzaniya ke fatan gani daga shugaban shi ne tinkarar matsalar cin hanci da ta zama ruwan dare da kuma ci gaba da manufar sakarwa da harkokin kasuwanci mara a wannan kasa, wadda a zamanin baya dake bin tsarin mulki irin na gurguzu.”

Jaridar NEUES DEUTSCHLAND ce ta ba da wannan rahoto. Ita kuwa Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG lekawa tayi kasar Kenya mai makobtaka da Tanzaniya domin bitar rikici na siyasa dake addabar kasar ta gabacin Afurka. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Kasar Kenya ta samu kanta cikin wani mawuyacin hali na siyasa tun bayan da shugaba Kibaki ya sha kaye a kuri’ar raba gardama da aka gudanar akan sabon daftarin tsarin mulkin kasar da shugaban ya gabatar domin kara tabbatar da angizon mulkinsa. Shugaban, mai kwadayin mulki, ga alamu yana tattare da takaici ne a game da wannan kaye da ya sha. Amma a hakika shi ne ainifin ummal’aba’isin wannan ci gaba da aka samu, wanda ya sanya murnarsa ta koma ciki. Domin kuwa bayan gagarumar nasarar da ya samu na kawar da tsofuwar gwamnati ta shugaba Daniel Arap Moi da yayi shekaru 24 akan karagar mulki a zaben shekara ta 2002, Kibaki ya gaza wajen cika alkawururrukan da yayi. Kuma duk wanda yayi bitar mulkinsa tsawon shekaru uku da suka wuce zai ga gwamnatinsa ta sha fama da tabargazar cin hanci da rikici iri daban-daban.”

A wani sabon ci gaba kuma a wannan makon kotun kasa da kasa dake garin The Hague ta yanke wani hukuncin dake wajabta biyan diyya akan kasar Uganda dangane da barnar yakin da tayi a kasar Kongo. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Kotun kasa da kasa dake The Hague tayi Allah waddai da kasar Uganda ta kuma nema da ta biya diyyar yakin da ta gabatar akan kasar Kongo daga shekarar 1998 zuwa shekara ta 2003. To sai dai kuma a daya hannun kotun ta nema daga kasar Kongo a nata bangaren da ta biya diyya ga Uganda sakamakon hare-haren da ta kai wa jami’an diplomasiyyar kasar lokacin barkewar yakin a shekarar 1998. Kotun dai ta zargi Uganda ne da laifin amfani da karfin bindiga domin keta haddin wata kasa mai ikon cin gashin kanta da mamayar yankinta na Ituri tana mai cin zarafin dan-Adam da take tsarin yarjeniyoyin dake tsakanin kasa da kasa. Mai yiwuwa hakan ya zama gargadi ga sauran kasashen dake da niyyar daukar irin wannan mataki na mamaye, in ji jaridar ta DIE TAGESZEITUNG.