Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon ma halin da ake ciki a Chadi shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

Babban abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon, wanda shi ne na farko a sabuwar shekarar miladiyya ta 2006, shi ne halin da ake ciki a rikici tsakanin Chadi da Sudan. Jaridar kasuwanci ta Handelsblatt tayi amfani da wannan dama domin duba halin da ake ciki a kasar Chadi tana mai saka ayar tambaya a game da ko shin jama’a sun fara cin gajiyar hada-hadar hakan man fetur da kasar ta fara tun misalin shekaru biyu da suka wuce. Jaridar ta kara da cewar:

“Babu dai wata alamar dake yin nuni da samun canjin al’amura a kasar Chadi nan gaba kadan. A halin yanzu haka ana fama da takun saka tsakanin fadar mulki ta Njamena da bankin duniya. Bugu da kari kuma ainifin ribar da kasar ke samu daga garwanin mai dubu 225 da take haka a kowace rana, tana kwarara ne zuwa aljifan shuagabanninta, a maimakon aiwatar da ita a matakan yaki da talauci. Kuma rahoton kungiyar Transparency ya nuna cewar a shekarar da ta wuce kasar Chadi tafi kowace kasa fama da matsalar cin hanci a duniya.”

Kasar Cote d’Ivoire har yau tana fama da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali duk kuwa da gwamnatin wucin gadi da aka nada karkashin P/M Charles Konan Banny, inda a wannan makon aka fuskanci bata kashi tsakanin wasu dakarun da ba a san ko su wane ne ba da kuma sojan gwamnati a cibiyar kasuwanci ta Abidjan. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG, a lokacin da take ba da rahoto game da haka cewa tayi:

“Wani abin lura a nan shi ne jim kadan bayan nadin Charles Konan Banny sabon P/M gwamnatin wucin gadi da ta kunshi dukkan sassan da ba sa ga maciji da juna a rikicin kasar Cote d’Ivoire da ya ki ci ya ki cinyewa, sai da aka fuskanci mummunar arangama a birnin Abidjan saboda magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo na tattare da imanin cewar an kwaresu saboda ba a ba su wasu muhimman mukamai a sabuwar gwamnatin ta rikon kwarya ba. Akwai dai rahotannin dake cewar masu alhakin kai harin wani bangare ne na sojan kasar da suka shiga bore domin neman karin albashi da kuma mukamai.”

Ita ma kasar Uganda tana fama da zaman dardar, inda aka fuskanci mummunan hargitsi bayan sanarwar da aka bayar ta sakin Kiiza Besigye dan hamayyar shugaba Yewori Museveni, wanda kuma ke da niyyar kalubalantarsa a zaben kasar da za a gudanar wata mai zuwa. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar halin da ake ciki a kasar ta Uganda inda take cewar:

“’Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsofuwa da harsasai na kwarai akan masu zanga-zangar murnar sakin Besigye, wanda ya ce shi da magoya bayansa zasu yi bakin kokarinsu don kawo canji ga shugabancin kasar Uganda. To sai dai kuma akwai alamar sake tasa keyar jami’in hamayyar zuwa gidan wakafi da kuma gabatar da shi gaban koliya domin amsa sauran laifuka guda biyu da ake zarginsa da su wadanda suka hada da cin amanar kasa da kuma yi wa mata fyade. Ita dai jam’iyyar adawa da FDC ta ce zata ci gaba da yakinta na neman zabe ba tare da la’akari da shari’ar akan Besigye da kuma sakamakonta ba.”

Masu sauraro duka-duka iyakacin abin da ya samu shiga ke nan a cikin rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka sai kuma in sake mika ku ga jagoran shirinmu na harkokin yau…