Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a Darfur na daya daga cikin muhimman batutuwan da jaridun Jamus suka duba a wannan makon

Rikicin Kongo

Rikicin Kongo

MOD.:To madalla. Daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa har da kai ruwa ranar da aka sha famar yi dangane da shugabancin kungiyar tarayyar Afurka a zauren taron kolin kungiyar da kasar Sudan ta karbi bakuncinsa a bana. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Bayan cece-kucen da aka rika yi a karshe kasar Kongo Brazaville ce aka cimma daidaituwa kanta domin yi wa kasashen Afurka tsawon shekara daya nan gaba, a maimakon Sudan, wadda a bisa al’ada da ita ce ya kamata ta shugabanci wannan kungiya saboda ita ce ta karbi bakuncin taron kolinta na bana. Wannan daidaituwar da aka cimma ta taimaka aka samu wata ‘yar sararawa a lardin Darfur. Domin kuwa gaggan kungiyoyin tawayen lardin guda biyu sun bayyana cewar idan har aka ba wa fadar mulki ta Khartoum shugabancin kungiyar ta tarayyar Afurka zasu janye daga shawarwarin zaman lafiyar da ake gudanarwa a Abuja.”

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG a cikin nata sharhin kira tayi ga MDD da ta tashi tsaye domin tabbatar da zaman lafiya lardin Darfur. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“Yankuna da dama na wannan lardin dake yammacin kasar Sudan na fama da tashe-tashen hankula jefi-jefi kuma har yau akwai mutane sama da miliyan daya dake zaune a sansanon na ‘yan gudun hijira. Har yau ana fama da lalube a cikin dufu a kokarin neman bakin zaren warware rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa. Akalla abu daya da za a yaba da shi shi ne kasancewar an samu raguwar yawan mutanen dake fama da yunwa ko rashin lafiya sakamakon rawar da kungiyoyin taimako masu zamansu ke takawa bisa manufa.”

A wannan makon aka kammala taron kasa da kasa akan makomar jin dadin rayuwar jama’a a Bamako fadar mulkin kasar Mali. Jaridar NEUES DEUTSCHLAND tayi bitar sakamakon taron tana mai cewar:

“Wani muhimmin abin da ya kamata a yaba da shi shi ne shawarar da aka tsayar na rarraba dandalin tarukan kasa da kasa akan makomar jin dadin rayuwar jama’a a sassa daban-daban. Nahiyar Afurka baki dayanta ta karbi bakuncin bangaren taron da aka gudanar a kasar Mali. Taron a Bamako ya ba wa kungiyoyin kasashen Afurka masu zaman kansu da manoma kwarin guiwa. A nahiyar Afurka dai a halin yanzu ana dada samun muryoyi masu adawa da shawarar da kungiyar ciniki ta kasa da kasa ta bayar game da rage yawan kudaden kwasta, wanda ke daya daga cikin muhimman madogarar kasashen nahiyar wajen samun kudaden shiga da cike gibin kasafin kudinsu da kuma rage yawan bashin da ya kai musu iya wuya.”

Kungiyar Tarayyar Turai zata tura wata tawagar bincike zuwa kasar Kongo domin share fagen aikawa da sojojinta na kiyaye zaman lafiyarta a wannan kasa. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Kungiyar Tarayyar Turai ta tsayar da wannan shawarar ce domin amsa rokon da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Kongo suka gabatar na neman da kungiyar da taimaka musu da dakarun sojanta na kwantar da tarzoma domin hana billar sabbin tashe-tashen hankula ko wani yunkuri na juyin mulki dangane da zaben kasar da aka shirya gudanarwa watan afrilu mai zuwa. To sai dai kuma kasancewar kasashen Jamus da Faransa ne kawai ke da ikon ba da taimakon irin wannan runduna ta kwantar da tarzoma aka shiga mahawara a kasar ta Jamus a game da abin da jama’a ke gani wani mataki na shisshigi a riklicin kasar ta Kongo da ya ki ci ya ki cinyewa.”