1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

February 3, 2006

Gazawar da kasashen Ghana da togo da angola suka yi a gasar cin kofin Afurka na daga cikin batutuwan da jaridun suka yi sharhi kansu

https://p.dw.com/p/BvQ5

Ko da yake a wannan makon jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama a game da al’amuran afurka, amma zamu fara ne da sharhin jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG akan rashin tabuka wani abin a zo a gani da kasashen Ghana da Togo da Angola suka kasa yi a gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afurka a kasar Masar. Jaridar sai ta ci gaba da saka ayar tambaya a game da ko shin wadannan kasashe zasu kai labari a gasar cin kofin kwallon kafa da za a gudanar a nan Jamus daga watan yuni zuwa yuli mai zuwa..sai ta ci gaba da cewar:

“Kasashe uku daga cikin kasashen Afurka biyar da suka cancanci shiga gasar kofin kwallon kafa ta duniya sun gaza tun a zagayen farko na gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afurka. Kazalika ita ma Afurka ta Kudu da zata karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekara ta 2010, ita ma ba ta kai labari ba. Sannan su kuma ragowar kasashe biyun da suka tsallake rijiya da baya wato Tunesiya da Cote d’Ivoire, domin kaiwa zagaye na biyu, babu wata rawa ta a zo a gani da suka taka a wasan karshe da suka yi, inda kowace daga cikinsu tayi asarar wannan wasa. A yanzu ba abin da ya rage illa a sa ido a ga irin rawar da wadannan kasashe zasu taka a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya nan gaba a wannan shekara.”

Matsaloli na yunwa da cin hanci, a halin da muke ciki yanzun, su ne ke gurgunta al’amuran kasar Kenya. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar DER TAGESSPIEGEL ‘yar Berlin cewa tayi:

“A hakika tun misalin shekaru biyu da suka wuce ne aka fara hangen mummunar alkiblar da za a fuskanta. Domin kuwa tun a wajejen tsakiyar shekara ta 2004 aka yi hasashen fuskantar fari a kasar kenya. Kuma da kamata yayi tun a wancan lokaci a fara taimaka wa jama’a da irin shuka masu jure zafin yanayi da kuma tanadar musu da ruwan sha. Amma sai gwamnati tayi sako-sako da lamarin. A maimakon haka jami’an gwamnatin a fadar mulki ta Nairobi sai suka mayar da hankalinsu ga wani lamarin dabam. A tsakanin watan janairu na shekara ta 2003 zuwa nuamban shekara ta 2004 gwamnati ta shigo da mutoci masu alfarma samfurin marsandi kimanin 57 da ta sayosu daga Stuttgart akan tsabar kudi sama da dalar Amurka miliyan 12, kamar yadda kungiyar Transparenc ta nunar a cikin rahotonta, a baya ga wasu tabargazar cin hanci iri daban-daban da ake zargin gwamnatin Kibaki da aikatawa.”

A can janhuriyar demokradiyyar Kongo ana ci gaba da fama da yamutsi, wanda a sakamakon haka Kungiyar tarayyar Turai ke shawarar tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya domin rufa wa rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD baya dangane da zaben kasar da aka shirya gudanarwa nan gaba a wannan shekarar. To sai dai kuma Jamus na dari-dari a game da ba da gudummawar nata sojojin kamar yadda jaridar DIE WELT ta rawaito tana mai ambaton ta bakin ministan tsaron kasar Franz-Josef-Jung. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Nan da kwanaki 100 masu zuwa ne aka shirya gudanar da zaben demokradiyya na farko a cikin tarihin kasar Kongo tun daga shekara ta 1965. To sai dai kuma duk da dimbim sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD ta tsugunar a kasar, amma har yau ana ci gaba da fama da tashe-tashen hankula da yamutsi a gabacinta. To ko Ya-Allah Kungiyar Tarayyar Turai zata yarda ta tura sojojinta zuwa wannan kasa a cikin irin wannan hali, kamar yadda MDD ta bukata..A yanzun dai ba tabbas game da haka.”

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar matsalar inda take cewar:

“MDD na ci gaba da fafutukar neman taimakon kasashe domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar Kongo. A dai halin da ake ciki yanzun Kungiyar Tarayyar Turai ta tura tawagar wakilan sojanta zuwa Kinsahasa domin neman karin bayani a game da yiwuwar ba da gudummawar askarawan kwantar da tarzoma. Amma ba tabbas game da yiwuwar aikewa da sojojin sakamakon bijirewar da Jamus tayi, wadda ta ce faufau ba zata tura sojojinta a wannan mataki ba.”