1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Ci gaban da aka samu tsakanin Chadi da Sudan shi ne ya fi daukar hankalin Jaridun Jamus

Idriss Deby

Idriss Deby

Ci gaban da aka samu a shawarwarin sasanta rikici tsakanin Chadi da Libiya na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka mayar da hankali kansu a game da al’amuran nahiyarmu ta Afurka. A cikin nata rahoton dai jaridar FRANKFURTER ALLEGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

“An samu kyakkyawan ci gaba tsakanin Chadi da Sudan, inda shuagabannin kasashen biyu, a lokacin taron kolinsu a Tripolin Libiya suka cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicinsu na kan iyaka. Dukkansu sun amince da a tsugunar da rundunar kiyaye zaman lafiya a tsakanin iyakokin nasu sakamakon zargin da suka rika yi wa juna na keta haddin iyakokin kuma a farkon watan janairun da ya wuce shugaba Deby na Chadi yayi batu a game da wani yanayi na yaki tsakanin Chadin da Sudan.”

A sakamakon takunkumin da MDD ta kakaba wa shuagabanni biyu na wata kungiyar ‘yan ta kife dake da dangantaka ta kut da kut da gwamnatin kasar Cote d’Ivoire a yanzu askarawan kiyaye zaman lafiya na majalisar na fuskantar barazanar hare-hare a kasar ta yammacin Afurka, in ji jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU, wadda ta kara da cewar:

“Tun a farkon wannan shekarar ne yanayin dangantaka tsakanin MDD da gwamnatin kasar Cote d’Ivoire ya gurbace sakamakon umarnin da wani kwamitin bin bahasi na majalisar a karkashin jagorancin Pierre Schori ya ba da umarnin rushe majalisar dokokin kasar. A karkashin wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen dake da ikon arewacin kasar Cote d’Ivoire, wadda aka cimma a shekara ta 2002, an shirya gudanar da zabe a cikin watan oktoban da ya gabata, amma shugaba Gbagbo ya hana gudanar da zaben saboda rashin isasshen kayan aiki. An amince shugaban ya ci gaba da mulki har tsawon shekara daya a karkashin wata gwamnati ta hadin gambiza da zata hada da ‘yan tawaye da sauran jam’iyyun hamayya a wannan kasa. Kuma ko da yake an kafa wannan gwamnati, amma ana zargin Gbagbo da neman amfani da majalisar dokokin domin yin ta zarce. A sakamakon barazanar hare-haren da take fuskanta MDD ta kara karfafa damarar sojojinta na kiyaye zaman lafiya a kasar ta Cote d’Ivoire.”

Har yau dai kasar Kenya na ci gaba da kaka-nika-yi da matsalarta ta yunwa, wadda ake dora laifinta akan gwamnati, sannan shi kuma bankin duniya ya dakatar da rancen kudin ga kasar har sai gwamnati ta gabatar da nagartattun matakai na yakar cin hanci. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta sake bitar matsalar inda take cewar:

“Alkaluma masu nasaba da kungiyoyin taimakon sun kiyasce cewar kimanin kashi 30% na yara a kasar Kenya ke fama da rashin koshin lafiya sakamakon karancin abinci mai gina jiki sannan kashi 10% na illahirin al’umar kasar ke bukatar taimakon abinci daga ketare. Gwamnati na ci gaba da gangami domin neman taimakon kudin da yawansu ya kai dala miliyan 110, saboda kamar yadda ta nunar a halin da ake ciki yanzun bata da ikon magance wannan matsala sai tare da taimako daga ketare.